Chapter twenty four

4 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
24

Successfully, Kaka da Baba Talatu suka amince da batun makarantar Huda, Kaka shi ya sanar wa Madu wanda shima bai hana ba bai kuma ce taje ba kawai dai ya jinjina kai alamar ya ji kuma ya fahimta.
Kaka ne ya yanke shawarar Hudan ta tafi gidan su Ummu tayi koda sati ne, bayan ya kira Baba da Umma da Jalila yayi musu fad'a sosai!! Sannan ya cewa Jalila "tunda y'ar daba take son ta zama kuma iyayenta sun kasa tsawatar mata to ta tabbata tana gama ssce d'inta ta fito da Miji idan ba hakaba to zai bada hotonta a masallaci duk wanda ya zo kuma shi zata aura koda kuwa gurgu ne!."
Jalila kuka wiwi haka suka baro gidan Kaka, Umma sai mita take yi wai 'anyi son kai!' Idan ba haka ba dan maiyasa ba a yiwa Sakina fad'an dukan da ta yiwa Jalila ba?!.

A Daren ranar da su Ummu suka koma gida suka samu takardun Sakina itama har sun zama ready..
Duk wani preparation na exams d'in yi suke dan Arshaad har wata lesson teacher ya d'auko tayi musu isashshen lesson ranar asabar da lahadi wanda da farko shi yaso yi musu lesson d'in amman sai aka tura shi wani aiki Abuja sai monday da yamma tukunna zai dawo.
Sakina tana fahimtar lesson d'in sosai amman Hudan kam sai dai godiyar Allah,
matsalar da aka samu shine ita lesson teacher bata jin Hausa ita kuma Huda turancin sai a hankali.
Sai da ya zamana
duk abinda lesson teacher ta fad'a sai an mata translating da Hausa! Duk k'ok'ari da hak'uri irin na matar sai da ta k'ule a cikin kwana biyun.
Da kyar Hudan ta tsinci iya abubuwan da zata iya tsinta ranar Litinin kamar yadda aka fad'a Baban Sakina da Ummu suka kaisu makarantar domin su zana jarabawar.

Hudan har kusan kukan murna tayi da taga jarabar tasu zab'i ka tik'a ce! Saboda daman adduar da take ta yi kenan.
Sai dai kuma duk da hakan
da kyar da sid'in goshi ta iya amsa question biyar a cikin guda d'ari biyun da take tunanin ta gane wanda hakan ya d'auketa sama da awa d'aya.
Tayi kokari wajen ganin ta amsa ragowan dan bata so ace ta fad'i jarabawar nan tana mugun son tayi karatu a rayuwarta amman kwata kwata sai ta kasa.
Har kuka tayi a exams hall d'in, bata ankara ba taji ana cewa "20 minutes remaining!!" idan ta fahimta sauran minti ashirin kenan a tashi! Hakan ya sanya
kawai ta rufe idanunta ta karanto sunayen Allah ta nemi nasara da sa'a sannan ta d'aga pencil d'inta ta fara sheding, duk shed d'in da zata yi sai ta kira sunan Allah tukunna ta tik'a...
Haka tayi daga Ar Rahman zuwa As Sabboor, ta sake dawowa Ar Rahman a haka har ta gama wanda yayi dai dai da fara amsar takardun nasu.
Sai da ta tofe takardarta da addua tukunna ta bayar invigilator d'in yana ta tsokanarta.

Kasancewar y'an hall d'in su Sakina sun rigasu shiga yasa tana fitowa suka had'u da Sakina a k'ofa tana jiranta.
Sakina na ganinta ta k'araso da murnarta tana cewa
"Hudan jarabawar tayi sauk'i ko? kinga duk abinda malamarnan ta koya mana kusan duk sun fito, kamar ta sani."
Da mamaki Hudan ta kalleta kafin tace "Tab! Ni fa biyar kawai na gani irin wanda tayi mana, a maths d'in kuma naga irin wannan mai kamar triangle d'in wanda kika sake koya min da daddare dayawa amman duk sun chanja nambobin."
Lumshe ido Sakina tayi a hankali sannan ta bud'e, kafin tace mata
"Ai numbers d'in kawai suka chanja, kin dai yi ko?".
Hudan bata b'oyewa Sakina ba ta gaya mata yadda tayi..
Jikin Sakina duk sai yayi sanyi amman gudun kar ta sace mata guiwa ya sa kawai tayi ta  bata kwarin gwiwa.
Suna shirin wucewa aka ce  "kowa ya tsaya akwai d'an guntun orientation da za ayi musu, babu isheshshen lokacine amman da it's sopposed to be for weeks.."
Haka nan suka d'unguma aka fara orientation d'in. Ita kam Huda zuciyarta duk a dagule, bare ma da aka fara orientation d'in nan ta sake ji makarantar ta shiga ranta, duba kuma da abunda ta rafka a exams d'in duk sai hankalinta ya sake tashi.

Sai da aka yi rounding up sannan suka kama hanyar inda su Ummu suka yi parking, Hudan har da y'ar kwallarta,
da kyar Sakina ta d'an lallasheta ta bata kwarin guiwa tukunna aka samu hankalinta ya d'an kwanta.

Suna zuwa nan ma Ummu da Baban Sakina suka shiga tambayarsu, ita dai Hudan k'arshe ma kuka ta saka, dan gani take yi kamar har ta fad'i ne, sai da su Ummu suka yi ta bata baki tukunna ta hak'ura tayi shiru.
A haka dai duk jikinsu yayi sanyi jin Hudan bata yi wani abun kirki ba, suka k'araso gida.
D'aki suka wuce ita da Sakina sai da suka yi wanka suka shirya suka yi waya da Mama sannan suka fito suka ci abinci suka d'an yi hira da kallo sama sama isha nayi kowa ya nufi gado.
Ranar Hudan bata yi bacci ba kwana tayi tsayuwar dare tana rok'on Allah yasa suci jarabawar nan...
Washegari ma da safe haka ta tashi duk jiki ba kwari har dare, kamar jiya yau ma bata yi bacci ba, kwana tayi tana sallah..
Haka ta kasance kullum, itama Sakina daga baya tayi joining d'inta a sallar daren, a haka aka yi sati.
Ranar litinin da yamma sai ga Arshaad ya zo.
Su bama su san yazo ba, suna falo suna kallo, sun gama waya da Mama kenan! Wayar Baban Sakina ta shigo layin Ummu, d'auka tayi suka yi magana bayan ta ajjiye ta kalli Sakina da Huda tace "kuje Babanku yana son ganinku, Arshaad yazo da result d'in jarabawar da kuka yi."
Da kyar gabansu yanata fad'uwa suka iya mik'ewa suka nufi d'aki, bayan sun d'auko hijabansu suka tafi parlourn Baban Sakinan.
Sakina ce tayi sallama aka basu izinin shiga, ita ta fara shiga sai Hudan a bayanta kansu a k'asa suka gaida Arshaad.
Cikin kulawa ya amsa yanata satar kallon Huda wadda ta kusan yin fitsari a wando tsabar fargaba! So take kawai taji me za a ce.
Baban Sakina ne ya mik'a musu takardun yace "ga results d'inku"
Da kyar Sakina ta iya mik'ewa taje ta amso sannan ta dawo kusa da Huda ta mik'a mata d'aya... har rige rigen bud'ewa suka hau yi.
Hudan tana bud'ewa taga  149/200 sai kuma daga chan k'asa anyi stamping 'PASS' da green rubutu!
Sai da ta kalli sama sai taga sunan ba nata bane ashe takardar Sakina ce. Murna ta hau yi dan taji dad'i duk da fargaban rashin ganin nata amman atleast Sakina ta wuce.
Ita kuma Sakina tana bud'ewa taga sunan Huda, da sauri Hudan ta lek'o, bata san lokacin data ce
"Kaiii!! nawa ne kuwa?"
Da taga 185/200 itama an mata stamping 'PASS'.
Ai kuwa da sauri suka rungume juna a wajen suna dariya suna maimaita kalmar "Alhamdulillah" Hudan har da kwallarta a ranta tana aiyyana
"Yanzu kenan itama zata yi karatu kuma a wannan makarantar y'an gayun data gani zata je tayi karatunta."

SO DA BURI Where stories live. Discover now