Chapter twenty

12 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
20

Kamar yadda Baba Bashir ya rok'eta akan 'ta rabu da Abba'
hakan take k'ok'arin yi.
Dan ko da ace bai fad'a ba tabbas ba zata sake bi ta kan Abba ba, tayiwa kanta wannan alk'awarin! Ya ga soyayyar ta yanzu kuma zaiga fushinta
In sha Allah ko shine autan maza ta hak'ura da shi.
Abu d'aya ne wanda Maryam tayi domin Abba shine 'sakawa y'arta suna Huda' da tayi saboda shi, dan tun lokacin da take boarding school indai suna hira yakance "Idan Allah ya basa y'a mace zai saka mata suna 'Huda' saboda yana matuk'ar son sunan, idan
kuma Namiji ne zai saka mishi 'Aslam'. Zai barta ta zab'i duk sunan da take so a duniyar nan
amman lak'abin ya zama Huda ko Aslam."
Da matar Yayanshi ta haifa mai sunanshi shiyasa ta zab'i lak'abin 'Aslam' yanzu kuma ta sakama Yarinyarta suna Maryam ana kiranta da Huda ba dan komai ba sai dan kawai
tasan ba a tab'a chanjawa tuwo suna....tanaso wannan ya zama last abu da zatayi mishi
a matsayin sa na Mahaifin Hudan..
Bayaga haka! Duk wasu memories na Abba k'ok'ari kawai take yi ta goge su, ta samu ta ciresa gaba d'aya daga kanta har abada....

A lokacin data dawo Sadiya  shiri take yi da ita sosai,musamman ma data  lura da yadda y'ay'anta suke son Maryam d'in da Bilkisu, idan zata tafi yawonta haka nan zata kwaso su ta kawowa Maryam d'in suyita wasa suna d'ebe mata kewa....dama ita Maryam tana da son Yara sosai suma suna sonta, musamman ma Jalila wadda a lokacin da Maryam ta dawo shekararta 1 yanzu kuma tana shirin rufe biyu..
Har sati Jalila takanyi a wajen Maryam, sunanta ta fara kira a duniya kafin ma na Mahaifiyarta! Tun tana ce mata 'miya' har ta fara ce mata 'mama miya' daga baya ta koma ce mata 'Mama' kawai.
Shak'uwa ce sosai ke a tsakaninsu, ana yayeta kuwa Maryam dukda a lokacin tsohon ciki gareta, haka Jalila ta dawo wajenta dan tak'i yarda da kowa sai Maryam d'in......

Yanzu kuwa da Sadiya taga auren Maryam ya mutu!! gashi ko idda babu a kanta, tun daga lokacin taje ta d'auke Jalila, su Junaidu suma ta hana su kula Maryam d'in sai dai suyi a b'oye.
Tashi d'aya Jalila duk ta bi ta rame kullum cikin kuka take tana cewa "ita wajen Mama zata tafi amman furr!! Sadiya ta hana. Dan zuwa wannan lokacin ko gidan taje ba kula Maryam take yi ba sai dai idan ita Maryam d'in ce ta kulata
tukunna za ta amsa da kyar
shima kuma ciki ciki take amsata ba tare da ta kalli ko inda take ba! Idan kuwa iyaka su biyu ne a guri tofa in Maryam zatayi mata magana sau goma ba zata kulata ba!
Duk akan Mijin da bata saniba shi tun lokacin da Maryam ta dawo yake ta addua Allah ya bashi ikon raba aurenta da Abba!
Ranar kuwa da Abba ya saki Maryam a gaban shi suna gama gudun famfalak'in karnuka bayan sun dawo gida
ya cewa su Madu idan ta fita idda shi har yanzu yana sonta!
Ranar da ta haihu kuwa shi so yayi ma a d'aura musu aure a ranar! Sai da su Baaba Talatu suka yi masa da gaske! Tunkunna ya hak'ura.
To yanzunma ya sake tada balli
Hakan yasa kawai su Madu suka yanke shawarar d'aura musu aure amman Baba Bashir yace "zai fara tambayar Maryam d'in tukunna, tunda ita yanzu bazawara ce basu da hurumin zab'a mata Miji."
Shi dai Madu bai biye Baba Bashir d'in ba ya tashi ya fita yana mai ce masa "idan yayi fixing date ya fad'a masa zai bayar a sanar a masallaci!dan shi kam ya gama zab'awa Maryam Usman."

A b'angaren Maryam kuwa duk yadda ta kai ga k'in Ya Usman bata isa tace 'a'a' ba a gaban Mahaifin shi wanda yayi mata gata!....Bai duba yadda ta gudu ta sanya d'anshi a garariba haka ya rik'eta kamar komai bai faru ba!
Shiyasa yana zuwa mata da maganar tashi d'aya ta amince nan take.
A cikin sati d'aya aka gama komai aka d'aura auren
Usman Bashir
Da
Maryam Muhammad Madu akan sadaki naira dubu ashirin lakadan ba ajalan ba.
Murna a wajen Ya Usman a wannan rana abun har sai da ya bawa wasu mamaki!!!

Sadiya kuwa daman b'oye musu auren akayi....
Ranar taje wajen Baba Laraba suna hira kawai taji ana d'aura aure a masallaci, tun a lokaci ta fara hauka kamar tab'abb'iya! Tana cewa "Maryam taci amanarta, dan haka wallahi sai ta koya mata hankali!."

Tun lokacin take hauka kwata kwata ya ma k'i ta saurari kowa, babu yadda Baaba Laraba bata yi akan ta tsaya ta nutsu ba amman tak'i! Ko y'ar
kissar nan ma ta mata ita kam ta kasa kwatantawa.

SO DA BURI Where stories live. Discover now