Chapter twenty three

5 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
23

Sai da Ummu taga fitarsu tukunna ta juyo ta cewa Mama
"At least ai in suna wajen babu mai yi mana lab'e! Sannan su kansu bana so suji zancen yet."
Ajiyar zuciya Mama ta sauk'e kafin tace "Tun shekaran jiya nake zulumin ganin ki, gashi bani da ko sisi a waya ta, ke kuma baki kirani ba."

"Wallahi aiyuka ne suka chakud'e min suka yi mini yawa shiyasa kika jini shiru, yau ma Baban su Sakina ne ya taso ni yace 'in zo In faiyyace miki yadda sukayi da wannan Yaron da kika tura wajensa." Cewar Ummu.

D'an matsowa Mama tayi kafin k'asa k'asa tace "Au yaje?
Ai ni akansa ne naketa neman ki. Bilkisu na chanja shawara fa, ni ban san haka yake ba!
Ina tsoron masu kud'in nan
A bayanin junaidu da huda na fahimci cewa Yaron ba tsaran aurenta bane ba. Dan haka gara mu bari kawai Allah ya kawo mata wani...
Shine dalilin neman da kikaji nace Inata yi miki."

Dariya Ummu tayi kafin tace
"Ai Mama yanzu kam bakin alk'alami ya riga ya bushe!
Dan bawan Allah n nan da gaske yake...
Shekaran jiya inaga yana barin nan ya kira Baban Sakina, da yake a lokacin yana gida dawowarshi kenan muna zaune na gama bashi labarin za a kirashi kenan kawai sai ga kiran....
Bayan sun gaisa yace mishi 'shine Arshaad yana zuwa wajen Huda ne so mamanta ta bada numbershi tace a kirashi
zai iya zuwa yanzu ya same sa ba damuwa?'.
Ganin yana free d'in ne yasa Baban Sakinan yace masa
"eh, ya zo."
Cikin y'an mintuna k'alilan San gashi yazo.
Sun jima sosai dan sai bayan isha tukunna ya tafi.

Bayan tafiyar sa, nayi tunanin ko Baban Sakina yaji ko yaga wani mugun abu a tare dashi ne, dan sai naga duk jikin shi  yayi sanyi sosai, har wajen biyun dare yanata tunani yayi shiru shi kad'ai! Kuma sai waya yaketa fita yanayi da wani Abokin shi, jikinshi duk yayi sanyi....

Jiya wajajen k'arfe 12 ga mamakina sai ga Arshaad d'in ya dawo, dan har parlour na ya shigo muka gaisa.
Da zasu fita Baban Sakina ya kirata ta kai mishi abu sai da ta dawo ne take cemin wai passport d'in Huda suke tambaya.

Bayan tafiyarshi ma babu yadda banyi da Baban su Sakina akan ya gaya min halin  da ake ciki ba amman yak'i, kuma naga ya bashi takardu a cikin envelop.
Yau da safe ma ya dawo amman ban ganshi ba , Sumayya ce tace mini yazo
dan ita baban nasu ma yasa ta kai mishi ruwa har yanata tsokanarta ya bata kud'i ma tak'i karb'a, to yana tafiya ne Baba su Sakina ya kirani yace 'inzo yana son ganina'.

Ina shiga na sameshi a zaune
Bayan na zauna ne nake ce  mishi 'dan Allah in akwai matsala ka fad'a min naga gaba d'aya jikin ka yayi sanyi tun jiya.'
Sai a lokacin yake cemin 'ba issue d'in Arshaad ne yasa shi tunani ba, wata y'ar matsala ce a office kuma yanzu sun magance ta. Maganar Arshaad kuma ranar da yazo yayi mishi tambayoyi ne akan family d'inshi, and ya gaya mishi komai kuma bayan ya bincika ya gano iyayenshi, and basu da matsala, yayi bincike a kanshi, har makarantar da yayi a Dubai Herriot watt dan
akwai wani d'an Abokin yayanshi dama daya sani yayi makarantar shima so ya tambayeshi ko ya sanshi and an yi sa'a kuwa ya san Arshaad d'in sosai kuma ya bada kakkyawar sheda akanshi....

So daman tun a ranar shi Arshaad d'in yake yi mishi magana akan ita Hudan tace mishi bata zuwa makaranta a ina ta tsaya dan yanaso taci gaba, saboda har ga Allah ba zai b'oye ba family d'insa y'an boko ne sosai.
So yace mishi 'iya js
ta fara js 1 kenan aka cireta.
Jiya daya tashi zuwa kawai sai gashi da form na makaranta 'Nigerian Turkish' wai suna d'aukar y'an scholarship, saboda da farko cewa yayi zai sakata a makarantar ya dinga biya mata shi kuma Baban Sakina yaga abun kamar ana sauri saboda yaushe ma aka san juna da har za a bashi damar fara biya mata kud'in makaranta?
Shikuma Arshaad d'in ganin da yayi Hudan bata da foundation na karatu mai kyau ne yasa yake son sakata a babbar makaranta dan ta samu ta taddo mates d'inta tunda dai yanzu ba zai yiu ace Huda ta shiga js1 ba.
To shi dai Baban Sakina a lokacin yace mishi 'gaskiya A'a'
sai kuma ga maganar scholarship ta b'ullo.  

SO DA BURI Where stories live. Discover now