Chapter sixteen

7 1 0
                                    

So Da Buri
Free Book
16
                
Cikin sheshshek'ar kuka Maryam tace "Hajiya fa fushi takeyi dani, yanzu idan na gudu zata kuma jin haushi na."

Hannu biyu Abba ya d'aura a kansa, kafin yace "O my God!!Maryam da wanne yare kikeso in yi miki bayani ne??
Ko bayan auren ki da Usman zata ci gaba da jin haushin ki ne....in dai kika auri Usman to kun yi ta janyo fad'a kenan a tsakanin iyayenku har azo a lalata zumuncin..."
A hankali ya matso kusa da ita yace "Nace miki kar ki duba kowa yanzu, just ki duba mu biyu kawai, and trust me! Please Maryam, this is the right thing to do...."

Cikin share hawaye tace "Abbana fa?"

"Abban ki ya riga ya zab'a miki ni, so Abbanki ba zai ji haushin komai ba, this is his choice Maryama.
Itama Hajiyan blackmailing d'inta aka yi, sannan kunyan Baaba Talatu take ji shiyasa amman da zarar mun yi aure idan taga kina cikin farin ciki tuni zata manta da komai! Burin ko wacce uwa taga farin cikin Y'arta
Maryam i assure you Usman cannot give you the happiness you deserve!."
Ya k'arashe maganar kamar zai fashe da kuka..

Shiruu, tayi tana tunani..
Tabbas duk abinda Abba ya fad'a haka ne sannan ta yarda dashi d'ari bisa d'ari!

Cikin katse mata tunani a hankali taji yace "muje..idan komai ya d'an lafa na yi miki alk'awari zamu dawo mu bawa su Hajiya hak'uri, na san zata hak'ura in sha Allah.
Abba kuwa na san shikam farin ciki ma zaiy yi, dan munyi abunda ake k'ok'arin hanasa, wanda hakan shine zab'in shi.
Na tabbatar idan mijin Innarku ya zo ba zai bari a d'aura aurenmu ba, kuma Inna da kanta kinji tace ba zata tab'a bari muyi aureba
wanda na tabbatar Abba ba zai tab'a iya shallake umarnin su ba."

Cike da gamsuwa da maganganunsa Maryam ta hau d'aga kai alamar amincewa kafin tace
"Amman zamu dawo anjima mu gansu, ko iya Abba ne shi kad'ai, na san ya san yadda zaiyi ya lallab'a Hajiya Shuwa watak'l ta hak'ura, kayi
mini wannan alk'awarin?".

Ajiyar zuciya ya sauk'e kafin yace "Nayi miki!
Amman nima kiyi mini alk'awari idan mun gama ganinsu, anjiman zamu wuce, saboda ina so in yin nesa da mahaifina ko da na wata d'aya ne. Ba zan iya fuskantarshi a yanzu ba, dan ban san hukuncin da zai yanke
mini ba."
Ajiyar zuciya ta sauk'e kafin tace "Na yarda!."
Ahankali yace "Alhamdulillah"sannan ya juya ya bud'e mata gaban mota.

Har ta wuce ta shiga, ta zauna sai kuma ta juyo ta kalleshi
yana shirin rufe mata k'ofar  tace "Abba, kana ganin ba matsala?"
Murmushi yayi sannan yace
"Yes Maryam, in shaa Allah, just trust me please.."

"Na yi, amma dan Allah kar ka sa in yi dana sani"
Murmushi yayi yace "i promise, I won't!".

Sai da ya juyo ya shiga, ya tada motar tukunna idanunta suka sauk'a akan Sadiya wadda take tsaye a k'ofar gidansu gaba d'aya hankalinta yana a kansu.....

Tafiya mai d'an nisa sukayi dan Maryam kam kanta har ya juye abunka da wadda bata fita sosai, tana cikin y'an kalle kallenta suka iso wani tafkeken masallaci a d'an gaba kad'an akwai hotel...
Wuce masallacin sukayi ya shiga cikin hotel d'in wanda ya gaji da had'uwa ga securities ta koina, ya nemi waje yayi parking.
Babu yadda bai yi da ita akan ta fito ta shiga cikin hotel d'in saboda shi yanaso ya je ya samu limamin yayi mishi bayanin komai, kuma akwai y'an shirye shiryen da yake so ya fara so zai kama mata d'aki ita d'aya shikuma ya fara preparations amman tak'i tace "ita a mota zata jirashi har yaje ya dawo", hakanan ba yadda ya iya ya kunna mata AC ya bata mukullin ya kwashi abubuwan da zai buk'ata.
Sai da yaje wajen Limamin suka tattauna sannan ya fito ya tari motar haya ya shiga aikin gabanshi.
Sai wajajen 12 tukunna ya dawo Maryam har tayi bacci ta tashi ga tsoro ga yunwa, yana zuwa ya kwankwasa, da kyar ta iya bud'e k'ofar ya shigo mata da abinci sannan yace bara yaje yayi Sallah idan an idar zai zo su wuce.
Haka kuwa akayi sai wajen 2:00pm
Time d'in masallacin kowa an watse tukunna ya dawo.
Yana zuwa ya sa key sannan ya umarce ta da ta koma baya, bayan ta koma ya tada motar yaja suka isa bakin masallaci.
Wani dattijo cikin alkyabba da rawani suka tsaya suka d'auka a bakin masallacin sannan suka hau titi, basu yi wani tafiya mai nisa ba suka gangara kan hanya suka shiga wani layi, a bakin wani gida sukayi horn aka bud'e gate d'in suka shiga.
Bayan sunyi parking sun fito
dattijon ya nuna musu babban parlourn gidan yace wa mai gadi "ya kaisu gurin Hajiya"
Shi kuma ya nufi parlourn bak'i dan yanada bak'i.

SO DA BURI Where stories live. Discover now