Chapter thirteen

7 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
13
                     

Maryam tana shiga d'aki ta fad'a kan gado ta fashe da wani mugun kuka...ta kusa awa d'aya tana abu d'aya, idanuwanta duk sun kumbura fuskarta tayi jajawur!!! Sai da tayi mai isarta tukunna ta hak'ura ta shiga sauk'e ajiyar zuciya akai akai....
Kamar wadda ta tuna da wani abun ta mike zumburr!! ta nufi wajen kayanta, k'asan ta d'aga ta zaro wata farar takarda..tun ranar da Abba ya bata takardar bata duba ba, warewa  ta shiga yi a hankali,
tana gama bud'ewa idanuwanta suka sauk'a kan wasu y'an nambobi a jere waenda ko ba a fad'a mata ba ta san number landline d'inshi ce.
"Lalle ma Abba!! wato ma nice zan kirashi!! despite the fact that na yi mishi kwatancen gidanmu!! he didn't even bother to come. Sannan kuma all this time already yanada wadda zai aura ya tsaya b'ata mini lokaci......Allah ya isanaa!!"
Ta fad'i hakan a cikin zuciyarta cikin d'aci da zafin zuciya.
Jin zuciyarta tana shirin fashewa ne yasanya ta duk'unk'une takardar ta jefar da ita ta koma ta zauna a kan gado ranta yana sake b'aci.
Gaskiya Shuwa ta fad'a da tace mata "b'ata mata lokaci kawai zai yi amma yanada wadda zai aura.' Dan kuwa  gashi ashe Abba yaudarar ta yake yi ita bata sani ba, dan inda ace son gaskiya yake mata ai da zai lek'o ta.
Ganin zuciyarta tana shirin fashewa tsabar takaicin abinda take tunanin yayi mata gashi zaai mata auren dole kuma duk shi ya ja amman bai ma damu da ya san halin da take ciki ba, kuma duk yadda ta k'ok'arta ta kasa rabashi da zuciyarta! Hakan ya sanya kawai ta yanke shawarar ta d'auki number ta kirashi, ta fad'a mishi ta fa san yaudararta yayi, at least zata rage wani b'angaren na  damuwa takaici da tashin hankalin da take a ciki!! kwana biyun nan.
Sai dai kuma Allah yasa yana gidan, dan ta san maybe a time d'innan yana school yanzu....
Da wannan tunanin ta mik'e ta isa inda ta yar da duk'unk'unanniyar takardar....da kyar ta iya bud'ewa dan har sai da ta d'an yage tsabar yadda ta d'unkuleta ta jefar d'azun...Haddace nambobin tayi a kanta sannan ta nufi falo. Kamar ko da yaushe landline d'insu yana kan tebur kusa da tv, kamar munafuka haka ta lek'a kitchen ta tabbatar Shuwa bata nan maybe ko ta fita ne Itada Bilkisu dan gidan shiruu, a hankali ta isa ta murza nambobin ta d'aga ta kara a kunnen ta...ba'a wani dad'e ba aka d'aga.

"Hello who is there?"
Taji ance mata
A hankali tace "please i want to speak with Abba."
"Ok!  hold on, let me tell him."
Mutumin yace sannan taji yana magana "Sir, someone wants to talk to you."
Daga chan nesa taji muryar Abba yana cewa "Who's it?"kamar bashi da lafiya
Jin muryar tasa kuwa da tayi , sai taji kamar rabin damuwarta ya kau, dukda haushin sa da take ji.
Mutumin ne ya sake tambayar ta "Ma'am pls what's your name?"
"Maryam"
Ta bashi amsa.
Tanaji mutumin yace mishi "Maryam."
Kafin kace kwabo muryar Abba har ta iso cikin dodon kunnen ta, da alamun har ya k'araso ya amshi wayar, muryarshi har wani rawa take yi
taji yana cewa
"Maryam! da gaske kece?
Ya kike? how is everything?
Zan zo soon, in shaa Allah...i missed you a lot!"
Ya fad'a kamar zai yi kuka wanda hakan yasa Maryam ta ji tausayinshi a d'ayan b'angaren zuciyarta kuwa tana ganin rainin hankali irin na Abba wai 'he missed her!' amman kuma shine ya kasa zuwa ya ganta?.

Murmushin takaici tayi sannan tace "Ai ba zaka damu ka zo ka ganni ba tunda kana da wadda zaka aura, Abba I just call saboda Ina so in tambayeka dalilin da yasa ka tsaya b'ata mini lokaci, bayan ka san an yi maka mata??"
Tayi mishi tambayar ranta yana sake b'aci.

Murmushi taji yana yi, kafin yace "Even your anger sounds sweet to me Maryam, i'm just happy Ina jin muryar ki yanzu.."

Maryam zuwa yanzu ranta ya b'aci sosai kamar ta fashe da kuka haka take ji...
Jin tayi shiru yasa yace
"Maryam kema idan kin san kina da wanda zaki aura mai yasa kika tsaya kulani??"
Jin tayi shiru yasa shi sake maimaita mata tambayar.
A hankali tace
"Ni bana sonshi, tun farko"
Da sauri yace "nima haka wallahi
&
Inaso ki san cewa 'ni Abba na yi miki alk'awarin ke! Zan aura duk runtsi, ko menene zai faru after that I don't care, i'll choose our happiness akan koma......."
Kukan da ta fara yi ne ya saka shi kasa k'arasawa.. nan ya fara tambayarta "mai ya faru??"
Cikin sheshshek'ar kuka tace "Abba duk wannan ba shi da amfani yanzu, da ace ka zo ka lallab'a Abban mu da duk hakan bata faru ba, amman ya...."
Cikin tare numfashin ta yace
"Maryam Yayana ne yayi grounding d'ina for 2 weeks!! Ya ma k'i ya tsaya ya saurareni kwata kwata, gaba d'aya baya kulani...
Bayan tafiyar ku ya zo nema mini transfer, shinefa wannan matar ta tisa shi a gaba ta dinga yi mana sharri...Amman kar ki damu, duk fushin da Yaya zai yi dani na san 2 weeks d'innan yana cika ya huce, kuma zai saurareni, daga nan zan zo in sha Allah..
Yau sauran 5 days ai kwanankin su k'are."
Ya fad'a sounding so relieved.

SO DA BURI Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz