Chapter twenty five

7 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
25

Jiki a mace haka Arshaad ya shiga gida, bai tarar da kowa a parlour ba, dama kuma hakan yake hoping dan ya san in dai Mammy ta ganshi a wannan situation d'in to sai ta fahimci yana cikin matsala, kuma ta dinga tambayar shi kenan, shi kuma a halin yanzu baya buk'atar yin magana ma, he just need rest, peace and quite!.

A haka ya k'arasa side d'inshi ya wuce bedroom, yana shiga ya fad'a kan gado rigingine yayi pillow da hannayenshi ya lumshe ido ko takalmin k'afarsa bai cire ba.

Ya dad'e a haka, tukunna ya zaro wayarsa daga aljihu ya shiga contacts ya fara scrolling, yana zuwa kan 'bff' yayi dialing da alamun daman number yake nema...
Bugu uku a na hud'u aka d'auka!
Wata murya very calm cike da jarumta da dad'in sauraro  mamallakinta yayi amfani da ita wajen cewa
"Assalam alaika!"

Nannauyar ajiyar zuciya Arshaad ya sauk'e kafin yace
"Ameen, wa alaika assalam. Ya aiki?"

"Alhamdulillah, wats up!?"
Aka ce daga d'ayan b'angaren.

"A lot!"
Shine abinda Arshaad yace, sannan cikin nutsuwa ya hau kwararo mishi bayanin yadda suka yi da Granpa da Auwal d'azun, da kuma zancen shiga kotu!...

Shiruuu, kowannen su yayi bayan Arshaad ya gama bayani. Chaan!! daga d'ayan b'angaren akace ,
"I'm coming home this Sunday, in sha Allah."

Da k'arfi Arshaad wanda a take yaji kusan 70% na damuwarshi ya kau, yace
"Really?? Woow!"

Sai a lokacin 'ASLAM' yayi murmushi, sannan yace
"Yeah really, Bro. I was planning nayi surprising naku gaba d'aya, but naga u need something to brighten up your mood, so i have no choice but to tell u."

"U really did brighten up my mood kam.
Allah ya kawoka lafiya and i also have a surprise for you."
Cewar Arshaad.

"Ok, sai na zo d'in in sha Allah."
Cewar Aslam, har zai kashe wayar sai kuma yace "karfa ka gayawa kowa, remember it's a surprise."

"Yeah i won't, i promise."
Shine abunda Arshaad yace yana murmushi.

D'an tattaunawa suka yi akan case d'in da Auwal ya had'a, bayan sun gama
Arshaad yayi mishi godiya sannan yace "bara ya barshi ya ci gaba da aiki." Dan ya san maybe abunda yake yi kenan ya tsayar da shi.

Shiruuu, Aslam yayi bai kashe ba kuma bai yi magana ba....chaan! Ya sauk'e ajiyar zuciya sannan yace "how is she??"

Lumshe ido Arshaad yayi a hankali, sannan ya bud'e su kafin yace
"She's fine, sai ka dawo."

Fahimtar da Aslam yayi k'ok'arin hanging up Arshaad yake son yi yasa da sauri yace
"No, pls wait!".

Shiruu, ne ya sake biyo baya chan Aslam d'in yace
"Tayi maganata? Did she ask about me?
Dan Allah ka gaya min gaskiya."

Gaba d'aya zuwa yanzu Arshaad ya fara regretting kiran sa d'in da yayi!
Wani yawu mai mugun d'aci ya had'iye da kyar kafin yace
"A'a!
Amman tana....."
'Kit!!' yaji an yanke kiran...

Da k'arfi Arshaad ya runtse idanunshi tare da damk'e hannunshi kamar zai yi boxing!
Ya fi minti biyar a haka tukunna a hankali ya fara bud'e idanuwan nashi da suka sauya kala tukunna ya samu ya iya janye wayan daga kunnenshi...
Yana mugun jin tausayin Yayan nasa, da ace yana da yadda zai yi to da ko nawa ne zai biya in iyakar kud'in shi kenan to zai biya ya yaye mishi wannan damuwar!.
Duk fad'in duniyar nan ko wajen Mammy yaje bata samo mishi solution d'in problems d'inshi amma minti goma yayi yawa Aslam zai nema mishi solution d'in matsalar shi ko wacce iri ce.

But shi gashi matsala guda d'aya tak! Wadda ya taso ya ganshi a cikinta sam ya kasa taimaka mishi...
Gaba d'aya Arshaad sai ya fara jin haushin kanshi...

SO DA BURI Where stories live. Discover now