Chapter thirty three

13 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
33

Da sauri Ummu ta k'arasa inda take ta hau tambayarta
"Mai ya faru??".
A hankali Mama ta share hawayen da suka sake zubo mata sannan tace
"Bilkisu, barin garin nan zan yi!! Na gama deciding.
Ba zan iya ci gaba da zama ba."
Ummu na shirin yin magana
Mama ta katse ta ta hanyar ci gaba da magana
"Duk tsawon shekarun nan da aka d'auka....ina hak'uri, ina rok'on Allah yasa su Hajiya su sauk'o daga fushin da suke yi da ni amman har yanzu ace sam babu chanji babu wani sassauci daga ita har Abba Madu??
Abun yana damuna ba kad'an ba!
Saboda Allah idan ni nayi mata laifi
Ita Hudan meye nata a ciki?.
Yanzu fa naga kiranta
ina bin kiran ta d'auka ko gaisuwata bata tsaya amsawaba tace
'Wai taga Khadijah ta warewa Hudan da Sakina ankon su,
In tabbatar na hana Huda zuwa saboda ba zata iya yiwa mutane bayanin wacece ita ba!'."
Kuka ne mai k'arfi ya kufcewa Mama, cikin kukan tace
"Saboda Allah sai kace wata shegiya?...
Shiyasa kawai na gama yanke shawara zan bar garin nan inaga zaman da nake yi a kusa da su ne ya sanya har yanzun bamu daidaita ba!
Watak'il idan muka d'anyi nesa da su abun zai yi sauk'i in basa ganinmu akai akai!
Kuma nima har ga Allah hankalina zai fi kwanciya.."

A hankali Ummu ta d'an juyar da kanta ta share hawayenta
kafin ta juyo ta cewa Mama
"Maganar 'barin gari' bata taso ba Mama
Ki tuna fa barin garin nan da kika yi a farko shi ya janyo komai in the first place!
Ki kwantar da hankalinki
duk abinda kika ga yayi zafi
tou zai yi sanyi da izinin Allah.
Kiyi hak'uri wata rana sai labari......"
Cikin tausasawa da lafazi masu tsuma zuciya Ummu tayi ta kwantar mata da hankali..
Sai da taga ta d'an yi sanyi
sannan tace
"Yanzu alfarma d'aya nake nema a wajen ki 'ki tashi mu tafi asibiti dan Allah'."
Shiruu, Mama tayi, chaan! Ta d'auki wayarta ta kira Baba..
Sai tayi mishi 3 misscalls tukunna a kira na hud'un ya amsa.
Bayan sun gaisa ne take ce mishi "tanaso zata je asibiti, Ummu zata rakata."
Ba tare da ya tambayi mai yake damunta ba yace
"A dawo lafiya, kar kiyi dare!."
Daga haka ya katse kiran.
Shiruu, tayi still da wayar a kunnenta bata cire ba..
....Jiya har amai tayi a gabanshi amman bai damu ya tambayi me yake damun ta ba!
Kuma wai a haka ne yake cewa 'yana sonta'...
Dafa ta d'in da Ummu tayi, tana mai cewa "mai ya ce?"
ne, ya dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi
"Ba komai"
Kawai ta iya cewa sannan cewa Ummu "ta mik'o mata hijabinta a wajen kayanta"
daganan suka fito tsakar gidan...

Jikin Huda ba k'aramin sanyi ya sake yi ba dan kasa zama ma tayi a d'akin! Tun lokacin da taji bayanin Mama akan abunda Hajiya Shuwa tace ta juya ta fita, daga d'akin gaba d'aya! Sakina da Sumayya ma suka bi bayanta..
Kamar yadda ta shawo kan Mama da kyar haka nan itama Sakina tayi fama da Huda
dan da farko itanma cewa tayi 'guduwar zata yi!' Wai "tunda Mama ta haifeta bata huta ba har yau!
Maybe idan bata nan Maman ta samu sauk'in wasu abubuwan...
Ta gaji da ganinta cikin tashin hankali kullum."

Sai da Sakina ta bud'e mata wuta daga baya ta dawo lallashinta tukunna ta saduda.

A gida suka bar su Sakina
Ita da ummu suka tafi asibitin
basu dawo ba sai wajajen k'arfe 10:00pm dan sai da aka k'ara mata ruwa
Jikinta yayi weak sannan jininta ya hau..
Da kyar ma asibitin suka barta ta taho gida da ragowar drip ukun da bata gama shanyewa ba bayan Ummu tayi musu bayanin 'akwai wata nurse mai chemist a bayan layin su da zata na chanja mata (drip d'in) sannan zuwa gobe da yamma in shaa Allah za su dawo'.
Kamar kullum yau ma Ummu ce ta biya bill..

Kusan a tare Adaidaita sahunsu suka tsaya a k'ofar gidan da motar Auwal.

Sam Jalila bata lura da su Mama ba, da yake duk a rud'e take kuma tayi dare tsoronta kar taje Baba ya dawo ya nemeta bai ganta ba! Dan
bata san lokaci ya tafi haka ba
Sai ta kalli wayarta yanzun tukunna ta gani..
Shiyasa ta zo ta wuce su tanata sauri nik'i nik'o da ledoji ta shige gidan.

Kallonta Ummu tayi sannan ta kalli motar kafin tace
"Allah ya kyauta!"
Daga nan taci gaba da k'ok'arin taimakawa Mama ta samu da sauk'o daga napep d'in saboda har yanzu jikin nata babu kwari.

SO DA BURI Where stories live. Discover now