chapter four

12 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
04
                    
A nan ya tafi ya barta a tsaye kamar wata statue, kana ganin fuskarta ka san ranta a b'ace yake, ita sam! ta kasa gane kan Auwal kwata kwata,bata son halayyar nan tashi, kalli yanzu k'iri k'iri ya had'a uwa da d'anta fad'a, shikuma Arshaad  ta tabbata kunyar ta ce ta sanya ya k'i cewa komai,gashi
Daddy ya rok'eta akan dan Allah su taru ita da shi su dinga rufama d'ansu asiri...shi kad'ai Allah ya basu su daina yayata wasu halayyarshi da kansu a cikin family, domin kuwa duk ranar da aka yi rashin sa'a granpa ya ji to tabbas kashin Auwal ya bushe....
Tana cikin wannan tunanin ta ji an dafa ta...tana juyowa suka had'a ido da Mijinta Alhaji Yusuf MT
murmushi ta yi kafin tace
"Daddy yaushe ka dawo?"

Sai da ya d'an k'ura mata ido kafin yace "Auwal ne ko?"

Murmushin ta sake yi sannan tace"amsa tambaya da tambaya, are we??"

Sauk'e wata nannauyar ajiyar zuciya ya yi kafin ya fara magana"Ta windown kitchen na hangoku Ina waya da doctorn ABBA, shine na fita ta k'aramar k'ofa na rufe na tsaya a k'aramin compound saboda bana son Auwal ya ji ni.
Kin san yadda suke shi da granpa,ba k'aramin aikin sa bane ya kwashe komai ya fad'a mishi
Tunda ya san in dai da granpa a case babu abinda zan iya yi masa."
Shiru yayi da alamun damuwa a kan fuskarsa kafin ya sauk'e ajiyar zuciya yace
"Adama akwai matsala fa, don sun sake yin wani fad'an da granpa har ya ma fi na last time, sannan shi kuma ya sakawa kanshi damuwa over gashi yanzu har ya kusan shiga next stage."

"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun"shine abinda Mom tace idanunta suna kawo kwallah kafin ta kalle sa sosai tace
"To ai ni da ka bari Auwal d'in ya ji ya fad'a ma granpa d'in watak'ila hakan ya sanya shi ya d'an sauk'o daga fushin.
Na ga kwana biyun nan ma ai kamar yad'an yi sanyi ai ba kamar da ba,ko?"

D'an murmushi Daddy ya yi tukunna yace"babu fa abinda ya chanja daga halin granpa,kawai dai kwana biyun ba a samu wanda ya tab'o sa bane ba shiyasa kika ji shiru...d'azun fa malan iliya ya kirani ya ke ce mini Auwal ya fatattake sa,da na tambayi drivern granpa d'in yace mini shi granpa d'in ne yace a kori mallan iliyan d'azu daga dawowarsu daga meeting,wai dan ya bar bakin main gate ya tafi siyan agwaluma."

"Allah ya kyauta"
Shine abinda Mom tace, sannan ahankali tace "wai menene ma to abunda ya taso da fad'an nasu shi da Abban??
daa fa har muna murnar almost 2 years lafiya k'alau tsakaninsu,shima kuma Abban ciwon nasa ko tari babu."

Sai da Daddy ya d'an furzar da numfashi tukunna yace"Wai mafarkai yakeyi da Maryam! da jariri a hannunta,tana kuka tana cewa ya zo ya taimaketa, abun ya kai 3 months yace kullum in ya kwanta sai yayi shinefa ya d'aga hankalinsa...
Da farko,Dad ya samu ya fad'a mishi. Shikuma Dad yace mishi ya yi ta addua kawai...
shine fa tsabar ganganci kawai ya je ya tunkari granpa da maganar..
akan wai yana so yaje ya ganta,ya tabbatar babu Yaro a tsakaninsu,saboda mafarkan da yake ta  yi."

Ba shiri Mom ta zaro ido waje sosai kafin ta yi k'asa da murya tukunna tace"me granpa d'in ya ce??"

"Cewa za ki yi me ya yi masa,ba me yace ba!
In banda abun Abba kai da ka san mutumin nan yanata fushi da kai for morethan 24 years ko ga miciji ba kwa yi da shi, amma shine zaka kwashi k'afa ka je ka tunkare sa da irin wannan zancen?
Ni wallahi Adama nima na fara tunanin ko dai asiri ne matar nan ta yi masa,saboda ki duba kiga yadda he's willing to risk everything just to talk to her again. Dukda irin bak'ak'en maganganun da ta dinga  rubuto masa har da fa threatening nashi da kotu fa ta yi...
Daga k'arshe fa idan ta aiko da sak'o ba ya nuna mana! daina nuna mana yayi ni da Dad 
Allah kad'ai ya san irin maganganun da suke a ciki
Shikuma a wannan lokacin kullum cikin bata hak'uri yakeyi yana aikawa.
Da kyar granpa ya samu ya rabasu, shine yanzu yake son tada zaune tsaye, shi ko ta jikinsa da lafiyarsa ma bayayi, gashi yanzu granpa ya yi masa horo mai tsanani.....
..Kinga da farko ya sallame shi a duk wani company da kika sani namu a yanzu babu Abba a ciki,sannan ya hanashi share d'inshi. Kuma ya bashi notice akan ya bar masa estate d'inshi kar ya k'ara ganin shi ko y'ay'ansa.
Yace kuma duk wanda ya bashi hak'uri sai ya had'u da tsananin b'acin ranshi,hatta gramma."

SO DA BURI Where stories live. Discover now