Chapter thirty two

13 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
32

Tun azahar! Sai bayan sallar magrib tukunna
Hudan da Sakina suka baro gidan Baaba Talatu suka nufi gida.
     ...Tun azahar d'in suna
tare da su Anty Zainab wadda suka zo ita da y'arta Khadijah (amarya) ana ta shirye shiryen biki...
Yarinyar tana son Hudan sosai
sai faman sakota take yi acikin lamuran bikin
Anty Zainab ita kuma tana ta gwasalewa har sai da Baaba Talatu ta d'an tsawatar mata.....

Ganin Hakan ne ya sanya Hudan ta mik'e ta shige d'akin Baaba Talatu ta barsu nan.
Tana shiga ta hau video call da Arshaad, sai da aka kira  Magrib tukunna suka yi sallama..

Suna shiga d'akin suka k'arasa da sauri wajen Mama sakamokon hangota da suka yi
kwance a duk'unk'une cikin bargo!
Dama sun fita sun bar ta tana  d'an zazzab'i da ciwon kai!.

Sakina tana zuwa tasa hannu ta tab'a goshinta!
Aikuwa a rikice ta hau salati...
kafin ta shiga cewa Hudan "ta zo maza maza, su fita su nemo adaidaita a kai Maman asibiti!
Ko kuma su kira Ummu."
Dan jikinta ba k'aramin zafi ya d'auka ba wanda hakan ya sanya gaba d'aya suka  rikice lokaci guda.!

Da kyar Maman ta lallab'a su suka hak'ura suka bari akan 'sai gobe da safe za a kaita asibitin'
A cewarta "ciwon nata, it not that serious."

Tsumman d'ankwali suka jik'o suka hau d'ad'd'aura mata a jiki...
A hankali ta fara jin zazzab'in yana sauk'a, dan haka ta mik'e ta nufi bayi domin yin alwala..

Bayan ta idar da sallar ne
ta juyo ta kallesu, kafin tace
"Kika ce d'azu Arshaad zai zo kuma naga baku dawo ba."

Sakina ce ta karb'e ta hanyar cewa "Eh! Ya kira waya...
wai Yayan nashi da zasu zo taren ne bashi da lafiya.
So sai gobe za su zo, in sha Allah."

Kamar Maman ba zata ce komai ba, sai kuma tace
"D'azu naji kamar Yaro ya shigo yana cewa 'wai Jalila taje inji Arshaad!'."

 
"Around what time?"
Hudan ta tambaya tana d'an kallon Mama."

"Wajajen biyar dai haka, zuwa, kafin Magrib naji ta shigo."

Murmushi Sakina tayi kafin tace "Iskancin su ne kawai!
Maybe wani abun nasu suke son k'ullawa..
Amman ya Arshaad bai ma tab'a ganin Jalila ba!
I don't even think  ya san ma tana existing.
Ko kin tab'a gaya mishi akwai Jalila a gidan nan?"
Ta k'arashe maganar tana kallon Huda."

"A'a" shine abinda Hudan tace
Sannan ta d'aura da cewa
"Tun wajajen hud'u da rabi ma muke video call da shi, sai da aka kira Magrib tukunna muka kashe."

Jinjina kai Mama tayi alamun cikakkiyar gamsuwa da zancen nasu! Daganan ta mik'e ta gabatar da sallar isha dan har an fara kira...
Da kyar ta d'an tab'a abinci ('ta zarcen' da suka yi tun rana)
shima kuma dan su Hudan sun takura mata ne daga nan tabi gado, su Hudan kuwa basu kwanta da wuri ba!
Dan bayan sun yi sallah sun ci abinci sai da suka d'an tattauna akan bikin Khadija wanda da farko Hudan tace "ba zata je ba!"
Sai da Sakina tayi mata nuni da yadda amaryar take k'aunarta tukunna ta yarda suka bari akan zata je d'in amma ba zata je har Kaduna ba (dayake a chan za ayi bikin)
Ta yarda dai zata je wunin da Baaba Talatu ta had'a anan (Kano) Saboda jama'arta bayan an kawota an dawo Kano, za kuma taje bud'ar Kai gidanta amma gaskiya ba zata je har Kaduna ba!
Ta san Mama ma ba lalle taje chan d'in ba..
Dan haka za suyi zaman su idan an dawo Kano suje events d'in Kano....

Haka nan Sakina ta hak'ura,
dan taga Huda ta riga ta kafe a kan bakarta.

Kamar yadda Umma tayi zato!
Bayan ta koma gida...
Sai da suka kai ruwa rana
tukunna Jalila ta yarda ta bata rabin kud'in shima kuma dan 
taji Umman tace 'akan Auwal d'in yayi ta kawowa sannan ya turo da wuri za ayi aikin!!'
Ba dan hakan ba to da ba zata  bayarba....
Daga nan ba suyi barci ba sai da Umma ta kokkoyawa Jalila d'abi'u da dabarun karb'ar kud'i a hannunshi.

SO DA BURI Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum