Chapter fifteen

7 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
15
                        

Ba tare da b'ata lokaci ba Baba Bashir ya fad'a musu duk abinda ya faru d'azu...
Tun kafin ya k'arasa Baaba Talatu tace "zancen banza ma kenan!!! Ai indai gaskiya za a bi to haramun ne neman aure a cikin aure".

Cikin b'acin rai Baba Bashir yace "waye kenan yake yi miki zancen banzan?? Sannan ban gane maganarki ta 'neman aure cikin aure' ba! Shin a tsakanin ni ko Madu waye kika tab'a ji ya cewa Usman ya bashi Maryam??
Shiyasa fa d'azu na kyaleku ban kiraku ba, dukda yadda na so ace ke da Shuwa kun zo kun yiwa mutumin nan godiyar abinda ya yiwa Usman kwanakin baya, amman kawai sai na fasa domin na san k'aramar kwakwalwa gareku, indai kuka lura shine yayan Abba sai kunsa munji kunya..."

"Ko kuma dai an so shirya munafurci shiyasa aka k'i kiran nasu ba!"
Maman Shuwa ta fad'i hakan
sannan ta mik'e tace "Madu na lura ba zaka iya tsawatarwa Yarinyar nan ba! Ba zaka iya tirsasa mata tayi abinda ya dace ba, a k'a'ida fa babu ita a hurumin zab'arwa kanta mijin aure, ku iyayenta ku ya kamata ku zab'ar mata.
Allah na tuba yaushe ma Maryam d'in ta NuNa ne wai? Da har ta san wani soyayya?.
Daman ni tunda naga sauyi a tattare da ita d'azun na san da wata a k'asa!.
Son da kake yi mata ya sanya baka son ganin b'acin ranta kwata kwata, to inaso ka sani wannan Maryam d'in da kake  shagwab'awa ko bayan raina zaka ce na fad'a maka 'Wallahi sai ta kunyataka!!' Ai shi Yaro ba a yi masa haka kwata kwata.
Taya ma za ayi ka bari ta auri wanda suka gama lalacewa a waje? Allah na tuba Yaro ka auresa da mutuncinka ma ya aka k'are ballantana wanda ya sanka tun a waje??
Ai ni wallahi na ma ga k'ok'arin wannan Yaro Usman da ya amince zai aureta, ga mahaifiyarshi itama y'ar albarka bata k'i jininka ba!!
Ana k'ok'arin a rufa maka asiri, kana son tonawa kanka asiri da hannunka.
Ba Baki zan yiwa Maryam ba amman duk daren dad'ewa indai wanchan Yaron zata aura to kuwa auren ba zai d'aure ba! Sai ta dawo gida kuma sai kun yi dana sani!!!".

Madu kasa jurewa yayi dan haka yace
"Inna na rok'e ki da girman Allah kiyi shiru!! A matsayinki na Babba ba a so ki dinga mugun alkaba'i haka!! Kawai ki bita da fatan alkhairi..."

A hasale Innar tace
"Ank'i a bita da fatan alkhairin!!! Ai sai mutum yaso alkhairi tukunna za a bishi da alkhairi!
Masifa kuke son janyowa kanku kai da ita k'iri k'iri!!!
Yaron nan ko bincike na tabbata ba kuyi ba....Kai nan kaga mai arzik'i ko? Shine zaka fake da wani wai 'Yayansa ya taimaki Usman', ai taimako daban neman aure daban.

Wannan karon Baba Bashir
ne yace "Inna tunda suka zo suka tafi muke bincike akan shi, kuma bamu samu wani mugun abu a kanshi ba kowa alkhairi yake fad'a."

Cikin fad'a sosai Innar ta katseshi ta hanyar cewa
"Amman tabbas yau na tabbatar Yaran nan baku da hankali wallahi!!! Binciken wuni d'aya shine Bincike????"

Madu ne yace "ai ba a son tsananta bincike ko a addini!"

Ga mamakin su kawai sai  sukaga Inna ta fashe da kuka a cewarta wai 'Madu da Bashir sun rainata! taya za a yi tana fad'a suna mayar mata saikace sun samu sa'ar su!?. Nan ta hargitse musu harda cewa "Sister's din Shuwa su shirya a daren nan zasu wuce Maiduguri ba zata sake kwana a gidan Madu ba!! Dan yaga ba itace ta haifeshiba shiyasa zai yi mata rashin kunya a gaban Yara, kuma sai ta kira Babansu, zata gaya mishi duk halin da ake ciki, wallahi indai tanada rai ba zata bari Maryam ta auri wanchan Yaron da suka gama lalacewa ba, shagwab'ar ai tayi yawa!! Taya Yarinya tayi laifi kuma still lallab'ata akeyi sai abunda takeso tukunna shi za ayi mata??.
Madu ne yau har da yi mata rashin kunya duk akan y'arsa???"
Da kyar su Shuwa suka d'an lallab'ata ta sassauta kukan, sannan ta hak'ura da tafiya amman tace 'tabbas maganar auren Maryam da Abba babu ita indai tana raye! Dan sai ta hukunta Maryam akan laifin ta,
da fari taso ta kyaleta amman yanzu ubanta ya janyo mata."

Hayaniyar su ta sanya har su Maryam d'ib da ke a d'aki suka d'an firfito.

Tarin da Ya Usman ya hau yi ne ya karkato da hankalinsu gareshi, gaba d'aya suka nufe shi....kafin su k'arasa har ya zub'e ya fad'i a wajen sumamme....
Nan kuwa Baaba Talatu ta fashe da kuka, tashi d'aya ta rikice!
Hankalin kowa a tashe aka fara k'ok'arin kinkimarshi..ganin baya motsi ko kad'an kamar gawa, ya sanya Baba Talatu ta juyo a zafafe tayi kan Maryam wadda take k'ok'arin k'arasowa wajen, tana matsowa kawai ta d'auketa da mari!! Ta fara magana cikin kuka
"Maryam mai nayi miki a rayuwar nan in banda alkhairi da kike shirin yi mini gib'i a rayuwa?? Tun tasowarki banda soyayya muraran babu abinda nake nuna miki har iyau, mai Usman yayi miki a rayuwa haka? Muguwa kawai!! Wallahi idan wani abun ya samu d'ana ba zan tab'a yafe miki ba!!."

SO DA BURI Where stories live. Discover now