Chapter twelve

8 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
12
                     

Da 'bell' ta yi amfani wajen tashi y'an hostel d'in nata tukunna ta wuce ta yi alwala ta fice mosque.

Sai da gari ya d'an yi haske
tukunna y'an mosque d'in suka fara dawowa. A hanya ne wata roommate d'insu da suka fito daga mosque d'in tare take ce mata "gaskiya Maryam kin b'ata wayonki, ban yi expecting haka daga gareki ba, gashi yanzu kin janyowa kanki! Allah kad'ai ya san hukuncin da za'a yanke miki."
Da mamaki Maryam take kallonta kafin tace "Ban gane ba Hafsa, mai nayi?!".
Tsaki Hafsat d'in tayi kafin tace "Ai ga irinta nan, daman Zainab ta fad'a.. k'aryata mutane zaki yi!
Ni dai shawara ta idan an je wajen principal ki rungumi laifinki, dan wallahi kin san halin principal idan kika yi mata k'arya laifin ki k'aruwa zai yi."

Zuwa yanzu kam gaban Maryam ya fara dukan uku uku gashi sun iso bakin gate d'in shiga hostel, hakan yasa tayi saurin rik'o hannun Hafsat tace "Hafsa dan Allah d'an tsaya, kin saka ni a duhu, kiyi mini bayani, sai magana kike ta yi a baibai."
Har Hafsat ta bud'e bakinta zata yi magana, wasu y'an  mata biyu suka fito da bokiti a hannunsu, suma duk y'an d'akinsu ne, kallonsu sukayi kafin d'ayar tace
"Ah lalle Hafsa, me ake koya miki? lalube ko shafa mai??."
Hararar su Hafsat tayi sannan ta cire hannunta a na Maryam ta yi cikin hostel ba tare data waiwayi kowa ba.

Su kuwa dariya suka saka sannan suka nufi unity tap d'in dake tsakiyar hostels d'in domin d'ibar ruwa.

Ita dai Maryam har ta shirya...taje dining aka nufi assembly ground, duk tayi sukuku, k'ok'ari take yi ta fassara kalmar 'lalube ko shafa mai' amman ta kasa, saboda amsar da kalmar take bata ba abune mai ma'ana a tsarin rayuwar da take yi a makarantar ba.

Ana shirin roundin up assembly d'in Principal ta rambad'a kiran sunan ta a mic tace kar taje class ta sameta a office d'inta.

To fah!!
Dan yanzu kam Maryam ta gama rud'ewa.
Da kyar a daddafe ta k'arasa office din principal d'in, gaba d'aya jikinta in banda  karkarwa ba abunda yake yi, gashi gabanta sai fad'uwa yake.

Knocking tayi,
ta ciki aka bata izinin shiga.
Tana shiga mamaki ya kamata sakamokon ganin Abba, metron da house mistress d'insu duk a zazzaune a cikin office d'in.
Da kyar ta iya k'arasawa ta zauna ta gaishesu, principal d'in ce kawai ta iya amsa ta Abba kuwa kanshi a k'asa yake tunda ta shigo, bai d'ago ba.

Gyaran murya principal d'in tayi sannan ta mik'o mata wata takarda, tace mata "ta karb'a tayi signing."
A hankali ta mik'e taje ta amsa, tun kafin ta dawo wajen zaman ta ta fara dubawa....ai kuwa bata iya k'arasawa wajen zaman nata ba sakamokon rikicewar da ta sake yi tashi d'aya ta shiga matsanancin tashin hankali......
Karantawa take yi tana sake duba takardar 'expell' d'in da aka bata ga sunanta b'aro b'aro a jiki, hankalinta bai gama tashi ba sai da taga dalilin korar!
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" shine abinda ta fara maimaitawa idanunta na zubar da kwalla, a hankali ta k'araso ta durk'usa a gaban teburin principal d'in ta fara magana muryar ta na rawa
"Ma, wallahi this is not the truth, pls don't expel me, i promise I won't talk to Abba ever again!. I don't want my parents to find out about this. I have been framed here I swear...."

Cikin rashin walwala principal d'in tace mata
"Don't worry your parents already know about this since yesterday, they are on their way now as we speak."

Rushewa Maryam tayi da kuka, ta fara magiya, tana cewa "sharri aka yi musu" .....tana alk'awarin rabuwa da Abba har abada, amman principal d'in bata saurareta ba kawai dai tace mata "Ita fa ta riga ta gama magana, so ta jira zuwan iyayenta kawai."

Metron kuwa munafuka in banda zuga principal babu abunda take yi, hadda cewa "ai ranar tun a clinic ya fara rungumeta. Waye waye"
Sai faman zuba dai take yi,
ba ita tayi shiru ba sai da principal ta aiketa ta je ta kira Zainab da wasu class mates d'insu.

SO DA BURI Where stories live. Discover now