Chapter thirty

9 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
30

D'akin da d'an duhu amman ba chan sosai ba sakamokon side lamps d'in da suke a kunne wanda hakan ya bashi daman hango ta kwance a kan gadon.
A hankali ya k'arasa ya zauna a gefen gadon.

A kwance take, rigingine..
pillows wajen uku aka d'aura kanta a kai hannayenta duka biyu tayi folding d'insu a kan cikinta!
Kalar fata ta iri d'ayane da ta Aslam, sai dai shi ya d'an fi ta haske kad'an.
Babu d'ankwali a kanta, wanda hakan ya bawa gashin kanta damar baiyyana wanda yake nan rabinsa bak'i rabi furfura!
Mai santsi da shek'i had'e da tsaho sosai.

Shekarunta ba zasu wuce hamsin ba...kallo d'aya tak! Zakayi mata ka gano kyakkyawa ce ajin farko.
Yanayin hancinta ne Aslam d'in ya d'auko sai dai nata har ya d'an so yafi nashi tsayi da tsaruwa amma saboda yanayin na Yarinta yasa za'a iya cewa ya fita kyau.....

Hannunshi ya saka ya kamo nata sannan ya d'aura d'ayan hannun nasa a kai ya dunk'ule a hankali ya saka guiwowin hannayenshi a kan gadon for sopport kafin ya d'aura fuskarshi a kan hannayen nasu !

Tunani ya fara 'rabonshi da ita yau shekaru bakwai! Kenan....

........Tun lokacin da psychiatric Doctor d'inta yace musu "the last option d'in da suke dashi shine a kulle su a d'aki d'aya, daga ita sai shi sannan a d'aure hannayenta da k'afafuwanta gudun kar ta cutar da shi ko ita kanta.
Hatta abinci ana so ya zamana shi ne zai dinga bata a baki, yayi mata alwala yayi mata komai for 24 hours!
May be daga hakan tayi snapping out, ta dawo cikin hankalinta."

Tun a 12 hours Aslam ya ga ba zai iya ba domin kuwa tak'i chin abinci kuma daga ya matso kusa da ita sai ihu! K'arshe ma suma ta fara yi...
Gaba d'aya duk ta firgice.
Ganin haka yasa ya d'auki waya ya kira Dad wanda shima d'in jin da yayi tanata suma yasa yace "bara ya zo ya gani."
Sannan ya kira Doctor,
shima Doctor d'in yace gashi nan zuwa.

Dad d'in yana zuwa yayi knocking k'ofa Aslam ya bud'e, basu ankara ba kafin ya shigo ta taho da gudu ta hankad'o Aslam d'in waje ashe ta kunce hannayenta ba tare da ta bari ya lura ba!
A take ta saka key...

Ba suyi wata wata ba Aslam ya fara k'ok'arin b'alla k'ofar Dad kuma ya tafi ya d'auko spare key!...Amman ko da ya zo ya saka k'ofar k'in bud'uwa tayi sakamokon barin key d'in da tayi a jiki ta ciki..
Suna cikin kiciniyar bud'ewa suka ji k'arar fad'uwar abu kamar kujera, a rikice Aslam yayi kan 3 seater d'in da take a parlourn ya cewa Dad "ya zo ya kama mishi".
Haka suka kinkimi kujerar da kyar, suka yi kan k'ofar da gudu da k'arfi suka buga!
Allah ya taimake su kuwa ta bud'u....

Aslam kasa motsi yayi sakamokon ganin k'afafuwanta a sama suna lilo kanta kuma tayi hanging a jikin chandelier d'in d'akin, sai dai k'afafuwan nata still suna d'an motsi!!.

Dad ne yayi k'arfin halin shiga da gudu ya d'auki kujerar data taka ta sak'ale kan nata ta yar! Ya saita mata ya d'aura kafafun nata a kai sannan ya hau ya kunto ta, sai dai zuwa wannan lokacin bata motsi!.

Shi dai Aslam duhu kawai ya fara gani daga nan bai sake sanin inda kanshi yake ba.

Sai da ya farfad'o tukunna ya fahimci ashe suma yayi...
Yana farfad'owa Dad da Arshaad suka yo kanshi suna tambayar shi jiki...
Cikin tsananin tashin hankali  , muryarshi tana rawa yace
"Dad ta mutu ko?
Shikenan nayi silar mutuwar  mahaifiyata!!"

Da sauri Dad yace mishi
"Bata mutu ba Aslam, suma kawai tayi."

A tunanin Aslam kwantar mishi da hankali kawai Dad yake k'ok'arin yi, shiyasa yak'i yarda da zancenshi har sai da Dad d'in ya kaishi ya ganta ta window tana zaune Gwaggo Asabe tana bata abinci a baki hannunta kuma ana mata k'arin ruwa!.

Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan yace
"Alhamdulillah"

Ba a dad'e bai aka yi discharging d'inshi..
Auna komawa gida ko gama dedeta parking d'in mota bai bari Dad yayi ba, ya fito cikin hanzari ya nufi cikin gidan..

SO DA BURI Where stories live. Discover now