Chapter Eight

13 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
08. 

Duk juyowa suka yi suna kallonshi da mamaki a kan fuskokinsu.
K'arasowa yayi ya kalli Mama yace "Nace miki Yarinyar nan yawonta ta tafi irin wanda kika yi amma kin k'aryata ni ko??
To mai adaidaita sahun da ya kawota shi na bi na tsare na tambaya ya kuma tabbatar mini da cewa 'Ita da wani saurayi dogo fari tass suka tsaida shi a wajen kwandila, bayan ta shiga har yana ce mata ta gaida su Mama har ya bada dubu d'aya a kawota, da mai napep d'in ya bata chanji tace ta bar masa.' Haka akayi ko ba haka ba?"
Ya k'arashe tambayar yana kallon Huda wadda jikinta a yanzu yake mugun karkarwa ga hawaye sai zuba sukeyi ta gagara controlling d'insu.

Mama ce ta k'arasa ta kamo hannunta ta share mata hawaye sannan a hankali tace
"Huda da gaske ne abinda mai napep ya fad'awa Baban ku? Dan Allah kar kiyi mini k'arya."
Addua Mama take yi a ranta Hudan tace mata 'A'a'
amman sai taga tana d'aga mata kai alamar 'Eh'.

Wata uwar gud'a Umma ta rangad'a sannan tace
"Huda Allah dai ya yi miki albarka, gwara da kika fara  fitowa fili kina fad'in gaskiya, yanzu sai a daina janta d'aki a na b'oyewa..
Don kowa yanzu ya san hali!
har shi Junaidu mai goya mata baya yau kam ya ji kuma ya gani. A bi dai a hankali kar a kwaso k'anjamau."

A fusace Mama tace
"Bana son mugun alkaba'i, dan an ganta da wani sai kuma akace wani abun ke tsakaninsu??
Ki fad'i alkhairi ko ki yi shiru mana! Mai ya kawo maganar k'anjamau a nan?"

Baba ne yace "Wallahi Maryam zan yi mugun sab'a miki!!!
Ya da girman mu kina raina mana hankali? Uban mai ya had'ata da shi to da har ya sako ta a adaidaita sahu?
To bari kiji in gaya miki!!
Malam Iro mai kayan Miya da kika rainawa arzik'i kika hana shi auranta, yanzu zan je ince ya turo!! Dan ba zan zauna Yarinya ta lalata mini gida ba.
Amman kafin nan sai na sauya mata kamanni ta yadda shi kansa d'an iskan saurayin nata ba zai iya ganeta ba, kuma gobe ko ance ta je ba za ta je ba."

Junaidu ne ya sha gaban sa ganin ya yo kan Hudan, kafin
yace "Baba a yi bincike dan Allah, kar a yi saurin yanke hukunci."

Cikin fushi Umma tace "tou shanyayye!!
binciken me kuma bayan wanda akayi?"

Da sauri yace
"Umma mu tambaye ta mana mu ji, kina gani fa bata b'oyewa kowa ba ta fad'i gaskiya bata k'aryata mai adaidaita sahun ba, ko?"

Yanzu wannan munafukar Yarinyar za ka tambaya???
Kuma kana zaton za ta fad'i gaskiya? Tou Bismillah bari mu ji."
Umman tace tana mai gyara tsayuwarta da d'aurin d'ankwalinta.

Ahankali cikin nutsuwa Junaidu ya tambaye ta "hanky d'in na waye? sannan waye wannan mutumin da aka gansu tare,a ina ta sanshi?"

Amsa d'aya ta iya bashi,
"hanky d'in na mutumin ne amman ita wallahi ba ta sanshi ba."
Ta kuma bashi labarin tun daga yadda kare ya biyo ta har lokacin da ya sakota a adaidaita.....

Dariya Umma da Jalila suka saka kafin Jalila tace
"Lalle Huda kin cika tantiriyar mak'aryaciya!"

Junaidu kuwa ganin raina masa hankali ma zata yi yasa ya jefar da hanky d'in kawai ya juya ya fita ranshi a mugun b'ace.....A hanyar fita suka had'u da Ya Jaafar yana shirin shigowa shi kuma, yana tafe yana tangad'i.

Yana shigowa ya hango Mama  a gaban Huda ta na k'ok'arin kare ta daga dukan da Baba yake shirin yi mata tana kuka tana bashi hak'uri..saboda ita har ga Allah ta yarda da labarin da Hudan ta basu.

Da saurinshi ya k'araso yace
"Ke dan ubanki Ina zob'o na???tun jiya na k'i shan ruwa ke nake jira, Jalila tace mini tun jiya da yamma muka aikeki, a gidan ubanwa kika kwana?"

Ita Hudan sai yanzu ma ta tuna da kud'in aiken kuma indai za ta iya tuna a inda ta zubar to a wajen gudun kare ne....
Hak'uri ta shiga bashi tana cewa "Bata ga gidan mai tuwo tuwo ba, ta duba duk wani lungu da sak'o na Gabdun Albasa. Sannan kud'in sun fad'i, ya yi hak'uri dan Allah."

SO DA BURI Où les histoires vivent. Découvrez maintenant