Chapter eleven

15 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
11
                     

Yana fita y'an ajin suka fara tofa albarkacin bakin su, har da masu cewa 'ai tayi sneaking ta shigo da waya dan da gani free call suka kwana suna yi jiya shiyasa daga ita har shi idanuwansu suka nuna alamun rashin barci. Wata Ramlat wadda hostel d'insu d'aya kuma k'awar Zainab ce k'ut da k'ut tace
"Tab! Yanzu girman kai zai k'aru, su o'o ba'a da had'add'en saurayi ma ana kallon mutane a kan hanci, ballantana yanzu anyi.."
D'agowa Zainab tayi ta kalleta a take tayi shiru bata k'ara cewa uffanba. Abinda ya bawa Maryam mamaki shine har suka koma hostel, aka yi lesson na evening, suka sake fitowa night prep kwata kwata Zainab bata ce mata uffan akan maganar ba. Sai dai kawai ta ga tanata yawan kallonta.

Straight jss2 ta nufa tana shiga ta gansa a zaune a gefen sit d'inta kamar ko yaushe.
Yana jin shigowa ya d'ago kai ya kafeta da ido har ta k'araso ta zauna ta gaidashi. A hankali ya amsa sannan yace "Ya hannun??"
Itama a hankali tace " da sauk'i." Sannan ta fara k'ok'arin bud'e jakarta domin da d'auko littafi ta samu ta fara karatu.
Littattafan d'azu ya mik'o mata yace "gashi, gobe sai ki bata nata ko?!"
D'agowa ta yi ta kalleshi sannan ta d'auka littafin ta bud'a da niyyar ta d'an k'ok'arta ta kwafa, saboda Yarinyar har ta fara mata maganar littafinta wai 'tanaso za tai karatu', amma kawai sai ta ga wani had'add'en rubutu ya baiyyana daga dai dai inda suka tsaya, dubawa tayi tai comparing da na k'awar tata taga Note d'in nata ya zama complete, kallonshi tayi taga shima Itan yake kallo da murmushi a kan fuskarshi kafin yace "Ko ban iya rubutu ba?".
Bata san lokacin da murmushi ya sub'uce mata ba saboda yadda yayi maganar yana wani langab'ar da kansa, kuma harga Allah tayi mugun jin dad'in taya ta d'in da yayi dan bata san ya za tayi ba, bata da wanda zata rok'a ya tayata dan kusan kaff y'an class da room d'insu daga safe zuwa yanzu kamar haushin ta duk suke ji wanda ita bata san dalilin su na Jin haushin nata ba.

Ganin tana murmushi kawai ya tsaya yana ta kallon ta dan ji yake kamar kar ta daina.

A hankali ganin ya kafe ta da ido tace "Ni ka daina kallo na."
D'auke idanunsa yayi daga fuskanta yana murmushi....idanunsa suka kai
kan hannun rigarta, dayake da d'an jini jini a jiki tun na jiya, har zai tambayeta dalilin da ya sanya bata wankeba sai ya tuna da hannunta, kuma a yadda take da shiru shiru d'innan ya san ba zata iya saka Junior wanki ba.
Dan haka kawai sai yace mata
"Ki dinga kawo kayan wankin ki zan na kai miki wajen wanki har zuwa lokacin da zaki warke ."
Murmushi kawai tayi tace mishi "to"
Sannna yace duk note d'in da bata yi ba ta kawo, da kyar ta bashi na physics, ragowar kuma tace "za ta k'ok'arta da hannun hagu."
Har aka tashi suna hira yau kam ta sake dashi, hakan kuwa yayi mishi dad'i sosai.

Washegari kam da bata zo da wankin nata ba taga b'acin ransa matuk'a, dan kicin kicin yayi, kuma ko da aka tashi da kyar ya yarda ta tafi bayan ya sanya ta ta rantse akan washegari za ta kawo."

Hakan kuwa akayi, washegari ta saka a leda ta sako a skul bag d'inta ta kawo mishi.
Ko da yaje gida akwai washing machine, ga dry cleaning a arean da wajen wanki dai kala kala, amman haka Abba ya zage ya tik'i wankin nan nata da hannunshi, abinda bai tab'a yiba kenan tun tasowarshi, cook d'insa kam da mai yi masa gyaran gida tsayawa suka yi suna kallon ikon Allah, dan babu yadda basu yi da shi ba akan ya kawo su wanke ba amma sam ya k'i.
A wajen ya zauna ya jira ya bushe, ya kwashe ya tafi d'aki ya goge mata, yana yi yana murmushi......

Hakanan ya mayar da abun aikin sa....note da wanki shi zai yi mata ko jinkiri ta d'an yi wajen kawowa ya dinga mita kenan yana fushi, hannun nata ya warke amman kwata kwata ya hanata wanki k'arfi da yaji.

Zuwa yanzu shak'uwa sosai ta shiga tsakaninsu, bak'in jini kuwa a wajen y'an class da hostel d'inta ta kwasheshi ba 'a magana, dan zuwa yanzu kowa ya sani saboda indai ya shigo aji har ya fita hankalinshi gaba d'aya yana a kanta suna had'a ido kuwa zai sakar mata murmushi ba ruwanshi da inda suke.

SO DA BURI Donde viven las historias. Descúbrelo ahora