chapter three

20 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
03
                      
A hankali Mama ta bud'e idanunta da suka d'an kumbura ta juyo tana kallon fuskar Hudan kafin ta kai hannun a hankali ta shafa kumatunta tausayinta yana sake shigar mata zuciya.

Nasarawa GRA, Kano.

Wani dogon dattijo ne ke tsallako titin da sauri had'e da d'an gudunshi,hannunsa na dama rik'e da agwaluma guda uku a cikin farar leda,na hagun kuma yana amfani da shi wajen mayar da y'an chanjin sa cikin aljihun gabar rigarsa,da alama agwalumar ya tsallaka siyowa.
K'ara saurin gudun nasa yayi sakamokon ganin har motocin da ya hango sun iso bakin mahaukacin gate d'in makeken estate d'in.
Da saurinsa ya zaro wani d'an k'aramin makulli a cikin aljihun gefen wandonsa ya isa gaban wata had'add'iyar k'ofa wadda ke a ta gefen makeken gate d'in wadda colour d'inta da design d'in exactly irin na gate d'in ne, cikin sauri ya zura mukullin a ramin mukulli sannan ya murza k'ofar ta bud'u ya tura da sauri ya shiga har yana tuntub'e, shigarsa ke da wuya waennan motocin da ke jiransa a ta wajen gate d'in suka fara danna masa horn babu k'akk'autawa...tashi d'aya duk ya bi ya rikice hakan yasa ya yi sauri ya fad'a d'akinsa na mai gadi ya d'aga k'asan pillow ya d'auko mukullin babban gate d'in ya fito yanata sauri ya k'araso jikin gate d'in ta baya ya bud'e padlock d'in sannan ya bud'e wani lock kafin ya durk'usa k'asa ya zare wata makekiyar sakata tukunna ya mik'e ya fara k'ok'arin tura gate d'in jikinsa duk yana rawa kana ganinsa ka san a rikice yake gashi an k'ara rikita shi da uban horn d'in da ake ta maka masa babu k'akk'autawa...  ,
Bai kai ga k'arasa tura gate d'in ya bud'u duka ba motar farko k'irar benz G wagon Bak'a wuluk! ta danno kai da mugun gudu ta biyun na binta a baya, ba don ya yi hanzarin barin wajen ba da babu abunda zai hana gilashin motar tafiya da y'ar sharar jikinsa.
Ganin motocin sun shige ne yasanya shi K'arasowa bakin gate d'in ya fara turawa domin rufewa, da kyar yake iya turawa saboda tsabar girma da nauyi.

Wani gate d'in motocin suka nufa a cikin jerin gidajen estate d'in da a kalla sun kai 15 kuma gaba d'aya ginin gidajen   yanayin tsarin 3D ne masu hawa biyu,tsayuwa fad'an haduwar ginin gidajen b'ata lokaci ne.
Wani kakkauran mutumi ne zaune a bakin gate d'in da suka nufa,sanye cikin uniform d'in sojoji,da alama shi ke gadin wannan particular gate d'in, mik'ewa ya yi sakamokon hango motocin sannan ya shiga ta k'aramar k'ofa ya bud'e musu gate d'in wanda hakan ya bawa farfajiyar gidan damar baiyyana..mahaukacin makeken mansion ne yanayin tsarin ginin 3D shima...
Ma sha Allah aljannar duniya kenan domin kuwa ya had'u har ya gaji da had'uwa da tsaruwa ga kyau ga girma duk ya had'a.
Wajen da aka tanada domin ajijiye motoci suka nufa sannan suka yi parking.

Wani mutum ne ya bud'e motar farko,ta wajen mazaunin driver ya fito ya zagayo ta wajen owners corner da d'an saurin shi ya bud'e murfin motar ya koma gefe ya tsaya .

....K'afarshi ta dama wadda ke sanye cikin had'add'en black d'in covershoe mai tsananin tsada ya fara zurowa waje, kafin ya sauk'o da d'ayar sannan ya mik'o ya fito gaba d'ayansa, ba matashi bane ba ko magidanci ko kuma dattijon Alhaji, tsohon mutum ne ,tukuf da shi!!
Sanye yake cikin wasu zazzafan suit,ash colour, kai kana ganin yanayin kayan ka san ya kai kud'in jarin mai k'aramin k'arfi,idanunsa sanye cikin wani farin glasses wanda kana gani ka san na k'arin k'arfin gani ne,walking stick d'in dake rik'e a hannunsa for sopport ma kanta abar kalloce!! Ka na gani ka san an zuba mak'udan kud'ad'e wajen siyar ta,ga wani had'add'en Rolex watch a hannunsa,
Tsohone amman skin d'insa glowing yake yi wanda kana gani ka san tsabar hutune..to cut it short dai,every part of him is screaming 'I'M RICH!!'.

Sandar hannunsa ya d'aga domin yin tafiya har ya d'an tura k'afarsa gaba sai kuma ya yi amfani da ita ya juyo ya tsaya yana kallon motar da suka shigo tare.

Wani kyakkyawan saurayi ne ya fito daga mazaunin driver da alama shi ya tuk'o motar da kansa, yana d'an fizgen kama da tsohon sannan kalar fatar su iri d'aya ce.
Ganin da Auwal ya yi kakan nasa ya kafeshi da idanune ya sanya shi K'arasowa wajensa da d'an sauri, tukunna ya d'an rissinar da kansa yana mai kallon k'asa kafin yace"Garanpa,u need something??."
Ya yi masa tambayar ba tare da ya kallesaba .
Juyawa Grandpa d'in ya yi ba tare da ya sake kallonsa ba,har zuwa lokacin da drivern d'insa ya d'auko suitcase d'inshi ya gama rufe motar yana taka mishi baya....
yana tafiyar ba tare da ya tsayaba cikin muryarsa ta tsofaffi yace"Go and give iliyasu 50k,ask him to leave this house foreva,he is fired!!
Sannan ka cewa Daniel ya nemo sojan da ya san zamu shirya ni da shi,ya fara gadin main gate,within 3 hours."
Yana magana yana tafiya ko sake waigowa bai yi ba balle ya amsa Auwal wanda yake cewa"Ok Granpa consider it done".
Ya shige.

SO DA BURI Where stories live. Discover now