Chapter thirty five

48 5 4
                                    

So da Buri
Free Book
35

Washegari Kamar yadda Mom ta yi niyya...
Haka nan ta d'auki video d'in da ta shiryawa!
Ta saman balcony d'in d'akin Mammy ta d'auki video d'in Aslam da Arshaad lokacin suna shirin fita..
Ko ta kan Mammy wadda take ta faman tambayarta "me za tayi?" Bata bi ba, ta fice abunta tana cewa "In na dawo zan yi miki bayani"...

Sai dai kuma
tana zuwa gidansu Aslam d'in ta tarar su Gwaggo Asabe sun yowa Mommyn rakiya
Flight d'inta nan da awa d'aya (9:00pm) zai tashi!!
Lokacin appointment d'inta da Neurologist d'in da Granpa yayi mata booking yayi...

Kamar Mom ta had'iye zuciya haka taji, ba yadda ta iya haka nan ta hau yi musu fatan alkhairi suka wuce ita da Aaima. Flight d'in Abuja za su bi, idan sun sauk'a a Abujan Aaima zata wuce makaranta ita kuma Mommy su wuce tare da Dad...

BAYAN WATA D'AYA!
(After a month!!).
Da gudu Jalila ta fito daga d'akin Umma..
Bata kai ga k'arasawa band'akin da ta fito na niyyar  zuwa ba! Ta hau kwarara aman da ya taho mata babu shiri
a nan bakin rijiyarsu wajen wanke wanke!.
Da sauri Mama ta fito daga d'aki jin mutum yana amai
Dai dai nan itama Umma ta fito da waya kare a kunnenta tana cewa
"Haba Zainab! tafiyar taku ba sai gobe ba?
Kiyi sauri kizo muje mu kaita asibitin mu dawo a san abunyi.
Kinga yanzun ma fa tana sa ruwa a bakinta kinganta ta fito ta hau amai!
Gara a yita a gama dan ni wallahi jikina ya na bani c....."
Ganin Mama ne ya sanya ta had'iye ragowar maganar tata.

Ita kam Mama ta Jalila ma takeyi, dan haka tayi saurin k'arasawa inda take ta hau shafa mata baya tana yi mata sannu....
Dama fa ita kwana biyu ta d'an ga wasu changes a tattare da Jalilan
Kuma tana lura da yadda Umman ta hanata zaman tsakar gida kwata kwata! Maybe ko dan ta lura da kallon kurillar da take yiwa Jalilan ne? Oho!

Da kyar Jalila ta samu ta amayar da d'an ragowar  ruwan da yake a cikin ta sannnan ta d'ago tana mayar da numfashi
Dai dai nan Umma ta k'araso wajen nasu tana hararar Mama..
Da mamaki Maman take k'arewa Jalilan kallo!..Tayi wani haske na ban mamaki
Bakinta sun yi pink sosai!
Sannan k'irjinta yayi mugun cika!
A hankali Mama da taji k'irjinta ya buga da k'arfi ta lumshe idanuwanta tace
"Innalillahi wa innailaihirrajiun"
Kafin ta bud'e su ta zubasu a kan Jalilan wadda itama ta kafeta da nata idanun...
A hankali Maman tace mata
"Sannu, me yake damunki?"
Jalila ancikin wata d'ayan nan ba k'aramin sanyi tayi ba,
yanayinta ma gaba d'aya ya sauya kamar ba Jalila ba..
Ta bud'e baki za tayi magana kenan Umma tace
"Ina ruwan ki!?
Sannan da kike wani salati
shin aljana kika gani ko me?
Kinga! Maryam!! wallahi ki fita a harkaata ni da y'ay'ana..
Ina jin ku jiya ke da Bilkisu kuna munafurcin Ja'afar
Bayan ke Huda ta fi sati bata a gidannan Allah kad'ai ya san inda ta tafi wannan karon!!
Ki fita a idona tun muna sheda juna wallahi...."
Tana ga fad'in haka ta jaa hannun Jalilan fuuuu suka shige d'aki.

Mama kam kasa motsi tayi a wajen...duk kalar tarin rashin d'aa'ar da Jalila ke zuba mata hakan bai hanata jin tsananin tausayinta ba!
Tabbas idan idanuwanta sun gane mata daidai to d'anyen ciki ta hango a jikin Jalila!
Bayan yadda ilahirin jikinta ya nuna
Aman da ta gama yi yanzu mai mugun k'arni ya sake tabbatar mata....
Salati kawai take yi tana sake nanatawa a cikin zuciyarta...
Ta ma kasa d'aga k'afafuwanta ta bar wajen!
Da kyar ta samu ta d'an motsa ta jawo ruwa a rijiya ta d'auraye wajen
daga nan ta sake luluwa duniyar tunani.....

A haka su Ummu suka shigo suka sameta.
Sai da su Sakina suka yi hugging d'inta tukunna tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data lulu.
Ummun ce ta d'an k'ura mata ido sanann tace
"Tunanin me kike yi haka?"

Wata nannauyar Ajiyar zuciya ta sauk'e kafin tace
"Ba komai"
Daga nan suka d'unguma suka yi d'aki.

Ba kalar tambayar da Ummu bata yi mata ba amman tace mata "ba komai" kawai!
Saboda hasashen alkhairi ake so a yayata, na sharri kuwa ba a fad'i!
Harshe na da kaifi!.

SO DA BURI Where stories live. Discover now