Chapter nineteen

7 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
19

Jiki a mace haka Alhaji Yahaya ya tashi ya fito, Madu har wajen mota ya raka shi yana mai sake yi mishi godiyar taimakon da yayi musu shekarun baya da suka wuce na Usman.

Bayan Yahayan ya koma ne ya d'au waya ya shaidawa Abba halin da ake ciki.
Hankalin Abba ba k'aramin tashi yayi ba a wannan lokacin, idan ya kalli Maryam sai yaji gaba d'aya tausayinta ya rufeshi. Dan, in dai ya fahimta to Mahaifinta disowing d'inta yayi kenan!
Duk sai yaji haushin kansa dan a ganinshi shine ya ja mata...

Baya son gaya mata komai a yanzu, yafi so sai ya lallab'a Granpa ya barshi ya koma Nigeria in yaso sai suje tare da shi da Yayansa har ma da Limamin da ya d'aura musu aure ya tayasu bawa Madun hak'uri.
Amman yanzu idan taji ta waya ko ta tafi Nigerian ita kad'ai ta samu wannan labarin
ya san it'll break her!!.

Da kyar ya samu ya lallab'ata tayi shiru bayan yace mata "idan Yaya zai taho k'arshen watan nan zai zo mata da numbar Madu. 

Karshen wata nayi Yaya yazo, kamar kullum tare da matarsa da d'anshi mai shekara bakwai mai sunan Abba ana kiranshi da 'ASLAM'.
Maryam ita ta zab'a mishi suna Aslam, dan bayan an rad'a mishi sunan YAKUBU, sai
Yayan ya tura musu sak'o yace Abba ya nemi sunan da za ana kiranshi dashi, shi kuma Abba ya cewa Maryam ta zab'a mishi...a wannan lokacin lokacin watanninsu shida da zuwa Madina aka haifi Aslam.
Aslam ya shak'u da Maryam sosai, dan kamar yadda Abba ya fad'a suna yin shekara Yayansa ya fara bibiyar shi duk k'arshen shekara kuwa sai yazo, tun yana zuwa shi kad'ai har ya fara zuwa da Aslam da Mamansa.
Dan Abba d'aga mishi hankali yayi akan 'yazo mishi da takwaranshi ya gansa.
Ai kuwa ranar da aka fara zuwa dashi Yaron yaga gata a wajen Maryam da Abba, shi yasa ya saba dasu sosai, yana son Maryam over itama tana son Yaron gashi yana da hankali. Mamanshi ma tanada kirki, dukda cewa ta girmi Maryam d'in amman hakan bai hanata k'ulla k'awance da Maryam dan tashi d'aya taji Maryam d'in ta kwanta mata a rai. D'ayar matar Yaya kuwa (amaryarsa) so d'aya aka zo da ita, ita ma ta haihu a lokacin d'anta d'aya sunansa 'Muhammad (Arshaad) amma bata zo da shi ba. Tunda matar ta zo Maryam d'in ta lura y'ar rainin wayo ce, dan sai wani cika da batsewa take yi sannan tak'i sakewa da Maryam kwata kwata, idan aka zauna ana magana kuwa bata da labari sai na company's da kadarorin Mahaifinta, bama ta cika yin magana da Hausa ba.! Ita Maryam a tunaninta maybe
ko dan ta san uwar gidan Yaya (Maman Aslam) k'awarta ce shiyasa ta had'a take kishin harda ita.
Sai bayan tafiyar su ne take tambayar Abba "Wai shin
mecece matsalar amaryar Yaya da ita ne? Dan ta fahimci bata sonta."

Abba bai b'oye mata ba yace "ai best friend d'in Zainab ce (cousin d'inshi da ake so ya aura), sannan y'ar Abokin Granpa ce, shine ma ya had'a auren tun da dad'ewa a lokacin Allah bai bawa Maman Aslam haihuwa ba, a tunaninsu bata haihuwa, to ita kuma Maman  Arshaad d'in sai mahaifinta yace "sai ta kammala karatunta wanda saura shekaru uku ta kammala"!
Anyi komai an saka rana, Maman Aslam ita tayi ta k'arfafawa Yaya guiwa a kan auren dan bata son abinda zai jawo matsala tsakaninshi da Granpa kuma ita a nata tunanin ko da gaskene bata haihuwar! Amman cikin ikon Allah ba a yi shekara da yin baikon Yaya da Maman Arshaad ba! Maman Aslam ta haifi Aslam.
Murna a wajen Yaya ba a magana dan yana mugun son matarshi a tunaninshi mahaifin nasu zai janye batun auren.
Sai dai kuma Maman Arshaad tana kammala karatunta aka d'aura aure tare dana d'ayan brother d'insu Yaya Yusuf wanda ya auri cousin d'in Zainab ne shima, ta b'angaren Uwa."

Maryam ba k'aramin tashin hankali ta shiga ba data gama jin bayanin Abba. Dan sai da Abban yayi dana sanin bata labarin..
Daman chan rashin haihuwa shine main problem d'insu gashi kuma yanzu taji wagga zance!! 'Kar fa taje itama Granpa yasa ayi mata kishiya!!!'

Da kyar Abba ya lallab'ata amman shi kansa a chan k'asan zuciyarshi hankalinshi ba a kwance yake ba..
Shi bama ta Granpa yake ba, a rayuwarshi bashi da burin daya wuce yaga jininsu shi da Maryam......

SO DA BURI Where stories live. Discover now