Chapter twenty six

6 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
26

Abun duniya duk ya bi ya taru ya ishi Mammy..
Hakan yasa ta mik'e, hijab d'inta kawai ta d'auka ta nufi gidan Mom.

Tana shiga kuwa kamar had'in baki ta tarar da Ummi itama a falon.
Sai da ta nemi waje ta zauna suka d'an gaisa tukunna tace
"Alhamdulillah! Da na sameki a nan."

Murmushi Ummi tayi kafin tace
"Me kuma ya faru yanzu?"

Ajiyar zuciya Mammy ta sauk'e sannan tace "Aaima da Arshaad ne! Wai ace Yaran nan har sun san su had'e mini kai suna k'usk'us a tsakanin su?"
Sai a lokacin tukunna Mom tayi magana, tace "Haba Mammy, ai abin farin cikine ma ace y'ay'anka sun had'e kai, kinga bakida matsala kenan dan babu mai iya shiga tsakaninsu!"

Murmushin takaici Mammy tayi kafin tace "Na san da wannan Adama, amman abunda nake so ki gane shine 'da ace abun kirki suke k'ullawa to da sai nafi kowa farin ciki !'.

Kin tab'a jin labarin wasu Yara da Aaima take gaya min Arshaad d'in ya kai ya had'ata da su?"

Shiruu, su Mom d'in suka yi kamar masu k'ok'arin tuna wani abun kafin chaan! Mom
tace "'Sakina' kamar naji tace ko? Waenda take cewa d'ayar Yarinyar tana kama da Aslam."

"Allah yayi miki albarka Adama, su dai. To wai d'ayar fa yake so, shine suketa k'us k'us d'insu.
Jiya Arshaad d'in inaga har kuka yayi wai ko tak'i d'aukar wayarshi ko fad'a sukaa yi, Oho musu dai."

Ummi ce tace "amman Yaron nan anyi ja'iri! Yanzu ya za muyi da maganar Khadija?? Kin san ko jiya sai da na had'u da Mahaifiyarta a wajen gyaran farce...
Tanata tambaya ta ya sirikinta
harma take gaya min next week khadijan zata dawo ta kammala masters d'inta."

"Banda Arshaad ma dai da abinshi, da class d'insa da komai amma shine zai je ya d'auko mana wachchar?? Daman wallahi ni jikina sai da ya bani.
A yanayin labarin Aaima kamar fa har provision shi yake yi mata lokacin da suke makaranta."
Cewar mom

Da sauri Mammy tace
"Kinji ko! D'azun nan kuma ya gama cemin 'ai she's very rich waye waye kawai dai iyayenta sunyi choosing ta tafi a scholarship ne waye waye'."

Murmushi Mom tayi tace
"k'arya yake yi!
Aaima ai ta tab'a bawa Auwal Labari, tace Yaran ko ishashshen turanci basu iya ba, ita ta dinga yi musu lesson lokacin tana chan...da zata tafi ma sai da ta had'asu da wasu.
Waenna Yara da suka samu good foundation a makarantar kirki ne za a ce basu iya turanci ba saboda Allah??
Kawai dai k'ok'arin watsa mana k'asa a ido yake yi."

Mammy kamar zata yi kuka tace "Ni ba wannan ne problem d'ina ba, dan bai auri Khadijah ba (ya watsamin k'asa a ido) shi ya sani!! Ni babban bak'in ciki na kar ya d'auko min Yarinyar da bata waye ba! Bana son had'a jini da su kwata kwata, zuciyata zata iya bugawa!
Kuma yadda yake son Yarinyar nan, in dai ya aure ta to shikenan ni da shi sai dai kallo daga nesa! Dan na san janyeshi zata yi gaba d'aya, gata kuma y'ar matsiyata na san ta dinga sakawa yana yiwa iyayenta abubuwa kenan, a gindinsu kud'insa zasu k'are!".

Murmushi Ummi tayi sannan ta dafa kafad'arta kafin tace
"Ki kwantar da hankalinki, Granpa fa ba zai tab'a yarda da wannan had'in ba, kin san yadda yake."

"Um um fa! Granpa d'innan ba a gane mishi alk'ibla, kar mu dogara dashi yaje ya watsa mana k'asa a ido, mu dai nemo wani solution d'in gaskiya, dan wallahi koni naji bana son Yarinyar tun kafin a je ko'ina, kuma daga gani yana sonta over ma kuwa! Kina ji fa wai jiya har da kuka , k'ato dashi."
Cewar Mom.

Ummi ce tace "na san ba a ganewa Granpa alk'ibla amman dai kin san ya fiki k'in son had'a jini da talakawa ko? Ki tuna Aisha fa."

Mom ce ta katseta ta hanyar cewa "Ai bamu gama confirming ya yanayin gidan su Yarinyar yake ba!
In aka yi rashin sa'a kuma ta fito daga middle class kinga ai an gama magana, dan Granpa ba lalle ya hana ba.
Kawai mu bama son Yarinyar ne, in ya aure ta akwai matsala
kar ya manta da mu da uwar shi, and ke kinfi kowa sanin ulterior motive d'inmu akan aurenshi da Khadija, ko?"

SO DA BURI Where stories live. Discover now