Chapter twenty seven

6 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
27

A hargitse ta k'arasa kanta ta d'ago ta, sannan ta hau dudduba ta tana cewa
"Ke!! Wai lafiya kike kuwa??
Meye haka? Dukan ki suka yi?
Mai ya faru???"

Rungume ta Jalila tayi ta fashe da wani sabon kukan...
Duk da kwakwazon tambayoyin da Umma take jero mata hakan bai sanyata ta sarara ta amsa mata ba, sai da tayi mai isarta tukunna ta share hawayenta tace
"Umma anya Kaka shi ya haifi Baba kuwa?
Ki duba fa kiga yadda yayi talla ta a masallaci shekaru uku baya wanda ba don na gudu na b'uya Gidan kawu Usman 
ba to da fa tuni yanzu ina gidan malam mati mai wanki!
Kuma kina gani fa har yau ya dage akan shi zan aura, ba dan munata addu'o'i ba na san da tuni yanzu an kawo kud'in an saka rana....
Ya dage ya hura min wuta ya hanani auren saurayi amman ita Huda kiga yadda yake k'ok'arin aura mata mai kud'i saurayi kuma kyakkyawa!!
Kamar ba ni ce jikar sa ba?"

"Ban gane me kike nufi ba!
'Yana k'ok'arin aura mata'! Kamar yaya?
Shin kin ji wani zancen ne bayan na fita?"
Umma tayi mata tambayar da alamun tsoro wanda ya bayyana k'arara a kan fuskarta.

Murmushin takaici Jalila tayi sannan tace "Umma, a gaban idona Huda ta tafi d'aya daga cikin makarantun da ake ji da su a kaff fad'in Nigeria!! Kullum ce mini kike yi zaki saka ta dawo gida gashi har sai da tayi candy ta gama bakiyi komai ba! Kuma na tabbata wannan saurayin nata yadda yake d'innan na san nan da nan zai nema mata jami'a ta tafi ni kuma ina nan ina wasan y'ar b'uya da Kaka!
Wannan wacce irin rayuwa ce saboda Allah??
Wallahi Umma sai dai in kashe kaina dan ba zan tsaya ina ji ina gani ta auri wanchan mutumin kuma tayi karatun da ni ban yi ba!."

Da sauri Umma ta buge mata baki, sannan cikin fad'a tace
"maganar kashe kanki ma bata taso ba!.
Sannan kin san Allah idan baki gaya mini abunda ya faru yau d'innan kin bar ja mini rai ba to sai na bubbuge ki yanzun nan."

Share hawaye Jalila tayi
sannan ta kwashe komai abunda ya faru yau d'in ta fad'awa Umma
Dan ko lokacin da Sakina ta ganta tana lek'e da ta komo d'akin nasu ci gaba da lek'a su tayi, tsaf sai da taga komai......
Sannan ta k'ara da cewa "kuma na san har wajen su Kaka ma yaje dan da wuya in ba a  saka rana ba ma, tunda gashi har kud'in k'unshi ya bayar...
Umma gashi wallahi tallahi ina son shi, sosai Umma!!.."
Ta k'arashe maganar tana mai fashewa da kuka....

Takaici! Da ya ishi Umma bata san lokacin da ta daddage ta d'akawa Jalila duka ba!
Sannan cikin fad'a tace
"Wallahi Yarinyar nan tun da nake ban tab'a ganin dak'ik'iya kamar ki ba!
Tun zuwan Yaron nan na farko nace miki 'idan ya zo ki fita! Idan yazo ki fita!!' Amman da yake y'ar iska ce ke!! Kina kuma so kisa inga abunda zuciyata zata buga shine kika yi zaman ki a d'aki kamar kumama!!"

Cikin kuka Jalila tace "Umma wai taya zan fita? Ko na fita na san ba lalle ya kulani ba!
Ki kallafa yadda Hudan ta koma sannan ki kalle ni.."

Katseta Umman tayi ta hanyar cewa "Dan uban ki ban san abunda nake yi bane ba?
Tunda nace miki ki fita d'in ai na san me nake yi ko?
Naki aikin kawai shine ki fita ki tabbata kun had'a ido da shi daganan ki bar min sauran aikin...Amman sam kin kasa! Abu guda d'aya za kiyi tak Jalila amma kin kasa yi wajen shekara uku yanzu!!
Kalle ki, sai dai ki zauna kina ta kuka, tou wallahi idan baki yi wayo ba a haka zaki k'are!! Tunda ni dai ba nice zan yi aikin da kece ya kamata ki yishi ba! Shegiyar Yarinya kawai....

Idam kika ga wanda Bilkisun kawun ku Nasiru ma zata aura sai kin yi mamaki!! D'azun muka je ganin gidanta a sabuwar gandu, tamfatsetse mai gate da bene! Da ke da ita da Hudan duk kusan tare kuka taso, ga y'ar gidan Zainab itama mai kud'i sosai ya fito mata nan da wata biyu za a sha biki in sha Allah...
Ke kuwa kina nan a d'aki, ke ko irin samarin nan masu motoci ma basa biyoki in kin fita, kina nan dai da malamin maths dan buhun uba mai shegiyar rowa, ni Allah yasa ma ba shine yayi miki asiri ba!"

SO DA BURI Where stories live. Discover now