Chapter twenty one

9 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
21

Murmushi Mama tayi kafin ta mik'e ta shiga yi musu 'sannu da zuwa'.

Baba Bashir ta jawa kujera ya zauna, Baaba Talatu da d'an gidan Ya Jamilu mai sunan Madu su kuma ta shimfid'a musu darduma.

Bayan sun gaggaisa ne Kaka (Baba Bashir) ya ke tambayar Mama "mai ya faru?,d'azu Bilkisu ta kira take ce musu Hudan na asibiti."
Shiru Maama tayi dan ita harga Allah bata san ta ina zata fara ba, gashi tanajin kunyar su.

Junaidu ne yayi gyaran murya, ya hau zayyano musu duk abunda ya faru.

Ai kuwa nan Kaka ya hau fad'a! Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba
A take ya sa aka kira mishi Baba yace masa "yazo yanzun nan yana son ganinshi a asibitin da aka kwantar da Huda."
Bayan kamar minti biyu Baba ya kira Junaidu ya tambayeshi "ko ya san sunan asibitin?" nan ya fad'a mishi harda number d'akin.

Suna zaune Baaba Talatu itama tanata bawa Mama baki
Baba ya turo k'ofa da sallama a bakinsa ya shigo.
Tun kafin ya zauna Kaka yace
"Wato Usman ban isa da kai ba ko?
Wato na hana su Sadiya zaluntar Yarinyar nan shine ka b'ullo ta hannun Ja'afar ko!?
Tayaya ma zaka bari shi da ba ishashshiyar nutsuwa garesa ba ya bugi Yarinya haka?!
Haba Usman, katako fa mai k'usoshi a jiki ya maka mata, a ciki!!!.

Yaro gaba daya duk ya bi ya haukace? Yo hauka mana, idan ba hauka ba wa zai yi wannan ta'asar saboda Allah?
Sannan ku kuma kai da uwar sa sam baku son kuji laifinshi.

Lokacin da yake hannun Maryam ai tun farkon fara lalacewar shi sai da ta nutsar da shi amma tun dawowar Sadiya gaba d'aya ya sake tab'arb'arewa!
Daga ya saci akuya sai ya saci kaza!
Shekaran jiya sai da aka kawo mana k'arar sa akan ya saci zakara!. Kuma abun haushi naira ashirin ko talatin yake saidawa k'arshen tsadar d'ari ko d'ari da hamsin.
Mai unguwa da kanshi yace mini 'dan kawai ya ga jikanmu ne shiyasa yake d'aga mishi k'afa.
Usman kai ka san a irin unguwar da muke Abu kad'an suke jira a fara gustiri tsoma!
Dan haka tunda kun kasa tsawatar masa ni zan dauk'i mataki! Tun kafin yaje ya janyo mana maganar da tafi wannan in dai baku tashi tsaye a kanshi ya shiryu ba to wallahi kaji na rantse 'Ni da kaina nan zan kaishi gidan mahaukata!!'."

Da sauri Baba ya d'ago ya kalleshi..

"Kwarai kuwa!"
Shine abinda Kaka ya fad'a kafin Baaba Talatu itama ta d'aura da cewa
"Yo ai Usman dole a kai sa gidan mahaukata, domin kuwa kwata kwata Jaafar baya yin abun masu hankali, kuma
gashi kun barshi a gida yana shirin yin kisan kai!!
Idan k'ungiyar masu kare lafiyar d'an Adam taji maganar nan Ina mai tabbatar maka da 'su zasu fara kaishi kafin mu mu kaishi'!
Shekaran jiya fa da Jamilu da iyalinshi suka zo...
ga Abba k'arami anan ka tambayeshi kaji
'a bakin kwata suka sami Jaafar ya tsugunna yana ta shak'a!' Babbar kwatar layi mai uban d'oyi.

Yau Huda ya yiwa zamu iya rufa asiri, gobe ka san wa zai yiwa??

Gaskiya ce muke gaya maka tun wuri kusan abunyi kai da uwarsa da bakwasan jin laifin shi...."

Shiru d'akin ya d'auka, a hankali Kaka ya mik'e ya isa inda Hudan take.....shafa kanta yayi yai mata sannu sannan ya cewa Abba k'arami "su taso su tafi."
Baba talatu ce itama ta mik'e tana mai cewa "Yanzu inda ace Jaafar mai hankali ne ai da tuni shima ya tara iyali
Kalli Abba shekara d'aya aka haifesu amma shi y'ay'ansa biyu....
Idan kuka bari so ya rufe muku ido zaku yi dana sani a gaba, dan gaba d'aya rayuwarshi kuke neman lalatawa ba tare da kun sani ba."
Tana gama fad'in haka itama ta yiwa Mama sai da safe sannan tayi hanyar fita tana cewa "ita kuma Hudan idan ta warke ki turo min ita inji waye wannan Yaron da suka ce ya sakota a napep d'in."
"To in sha Allah"
Shine abinda Maama tace
tana mai sake yi mata "sai da safe"
Har zata fita sai kuma ta juyo tace mata "Sadiyar sun zo??"
Shiruuu Mama tayi nanma ta kasa magana.
Girgiza kai kawai Baaba Talatun tayi tace "Hmmm"
Daga haka ta sa kai ta fita.

SO DA BURI Where stories live. Discover now