Chapter thirty four

17 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
34 

A meeting point d'in da suka yi zasu had'u...
  A nan suka tarar da Khadijahn tana jiransu.

Ba tare da b'ata lokaci ba
Aslam ya zaro blank check ya mik'a mata yace
"Ta rubuta ko nawa take so
muddin ta san zata fad'i gaskiyar abunda ta sani game da case d'in Arshaad."

"Mai yasa kake so ka sani"
Ta yi musu tambayar tana mai kallonsu.

Fahimtar da Aslam yayi za ta yi taurin kai ne ya sanya
kawai yace mata
"Ko ta fad'a ko kuma ya d'auke check d'in ya hanata kud'in kuma dole in za a shigo court sai anje da ita dan sunanta ya  fito! Dan Auwal ya ambato  sunanta a cikin case d'in."

Cikin tsanannin tashin hankali da b'acin rai tace
"Auwal d'inne ya ambato  sunana?
Sannan abun naku har da court daman?".

Arshaad ne,
yayi mata bayanin komai
sannan ya d'aura da cewa "ina da recording d'in wayar da muka yi da Auwal lokacin da ya ambato sunanki a ciiki"

Saboda haka ki taimaki kanki ki taimaki Auwal ta hanyar fad'in gaskiyar iyaka abunda kika sani.

If not zata rufta da ke da Auwal d'in, duk ranar da aka zauna a kotu....
Domin kuwa shi Auwal yana tunanin yayi mini sharri!
Sai dai kuma bai san iyaka wannan evidence d'in na voice call ya isa ya d'auresa tamau!! 
Kuma dole abun ya shafe ki.

Jikinta har rawa yake yi
tace "Dan Allah....zan gaya muku komai amman kar ku gayawa Auwal ni ce na fad'a!"
....Nan ta hau zayyano duk abunda suke da buk'atar ji da zai taimaka wajen wanke Arshaad!
Daga k'arshe tace "gobe da sassafe su had'u a nan, zata kawo wasu takardun duk akan bayanan da zasu taimaka wajen wanke Arshaad d'in ne.."
Sannan ta sake rok'ar su akan dan Allah dan Annabi kar su bari Auwal ya san itace ta fad'a musu, dan in dai ya sani to sai ya koreta a aiki bayan wulak'ancin da Allah kad'ai ya san kalar wanda zai yi mata...
Sanann su yi k'ok'ari kar a shiga court kar sunanta ya fito
dan ta san nan ma zata samu matsala da CEO!
Bayan an yanke mata hukunci kuma kora ta biyo baya..
Da wannan aikin ta dogara
su uku ne a family d'inta
Ita , mamanta, sai k'anwarta
Babanta ya dad'e da rasuwa
ita take providing a family d'in
su taimaketa! Dan Allah.
Ta k'arashe maganar cikin had'e hannunwanta alamun rok'o!.

"Thankyou Khadijah!." shine kawai abunda Aslam yace mata daga nan ya mik'e tsaye yana cewa "Nayi miki alk'awarin 'sunanki ba zai fito ba'." Kafin yace
"Rubuta kud'in da kike buk'ata
za mu wuce.

Da farko cewa tayi su barshi kawai. Sai da Arshaad yace "Ai alk'awari suka yi mata tun farko kuma ta fad'i abunda sukeson ji don haka dole su cika mata alk'awarin da suka d'auka."
Tukunna ta d'auki blank check d'in ta rubuta 300k!
Sukayi signing mata suka wuce...

Suna yin gaba Aslam ya zaro wayarshi a gaban aljihun rigarshi ya katse video d'in da ya saita tun kafin su fito daga mota.

Basu samu sun je wajen Auwal a ranar ba!
Saboda busy d'in da Aslam da Abba suka shiga har ma da Arshaad dan so suke su yi su gama shirye shirye su samu su bud'e company d'in nasu soon.

Around 9:00 pm washegarin ranar bayan kowa ya dawo a office an yi dinner da isha  suka nufi gidansu Auwal..

Da Mom suka fara cin karo a k'asa tana waya.
Faram faram ta karb'esu
bayan y'an gaishe gaishe Arshaad yace "Auwal yana nan?".
"Eh, yana sama har ya
kwanta ma.
Wai ya gaji yau sosai."Ta basu amsa, a tunaninta za su bari ne amman sai taga Aslam ya mik'e yana cewa "yana nan a side d'inshi na daa har yanzu ko?"

"Eh" ta sake basu amsa.

"Muje"
Aslam ya cewa Arshaad, daga haka suka nufi saman.

Mom ji take yi kamar ta bisu ta lab'e taji meyene ya kawo su dan
tabbas ta san ba lafiya ba!
Tunda dai Auwal ba shiri yake yi da either of them ba.
Tana shirin mik'ewa Daddy ya shigo! Kamar ta kurma ihu haka taji, haka nan tana ji tana gani ba yadda ta iya...ba dan ta so ba ta hak'ura da lab'en data shirya yi.

SO DA BURI Where stories live. Discover now