Chapter six

12 1 0
                                    

So da Buri
Free Book
06

Shiru Abba ya yi yana so ya gano inda kalmar 'ka maida ita!' Ta nufa,dan bai gane ba.
Fusata granpa ya yi jin yadda yayi masa shiru
Dan haka ya daka mishi tsawa ta hanyar cewa
"Ko baka ji na ne Abba!!!"
Tuni Abba ya hau cewa "to granpa in shaa Allah..yanzu yanzu...."
Duk ya bi ya rikice.
Ganin hakan ya sanya Ummi share fuskarta da ta jik'e da hawaye ta faki idon granpa ganin ba su yake kallo ba ya sanya ta d'an tab'a Abba tace
"Ka taso mu tafi,yake nufi."

Kallon ta Abba ya yi sannan ya mik'e ya ce "taso mu tafi."
Dan ba ya so ya fara zazzage mata ta cikinsa a gaban granpa. Har ya juya sai kuma ya dawo ya zo ta gaban granpa ya tsugunna yace
"Dan Allah ka yi hak'uri na san na yi maka laifi, ka yafe mini, in shaa Allah duk abinda kace inyi zan yi daga yau ba zan sake k'etare umarnin ka ba."

Kusan 1 minute tukunna granpa ya juyo ya kalleshi sannan yace "Yafe maka da na yi ba wai yana nufin na manta da abunda ka yi bane,na yafe maka ne saboda ni kaina in samu peace of mind na zama a same environment da kai tunda ka zame mini dole,
it's all for Ummi's sake, so idan kanada hankali do your best to keep her happy hakan ne zai sa ka gujewa b'acin rai na, ka samu mu rabu lfy.

Yana gama fad'in haka ya juya ya fara dogara sandarshi
har ya kai k'ofar d'akin shi ya juyo yace mata idan bai yi abunda nace ba, ko kuma ya yi trying anything stupid ki zo ki sameni."
Daga nan ya shige ya barsu a palon.

Kallon ta kawai Abba yake yi, ji yake kamar ya shak'e ta ya huta, gashi ya yiwa granpa alk'awari...idan ya fahimci kalmar granpa ta 'ka maida ita'
Tabbas Yaji Ummi ta yo
Ta karkad'e zani ta kawo k'arar sa kenan. Sannan
for her sake ne ma aka hak'ura zai ci gaba da zama a estate d'in....

Muryarta ce ta katse masa tunani
"Doctor is waiting"
Kawai tace ta kama hanyar fita
tana d'an tafiya da kyar tana tari irin na marasa lafiya.

Ta zo daff da fita kenan ta ji muryar gramma tana kiran Abba.
Da k'arfi Ummi ta runtse idanunta domin ta san yanzu kam k'arya ta ta k'are.

Kamar kuwa yadda ta yi zato gramma tana k'arasowa ta rufe Abba da fad'a akan sakin da ya yi, sannan ta hau bada umarnin ya maida ita nan take kuma karya k'ara.

A rikice yake kallon gramma sannan ya juya a fusace yana kallon Ummi wadda kana ganinta ka ga mara gaskiya...gashi babu Mom a wajen bare ta ceceta, fahimtar rashin gaskiya k'arara a kan fuskarta ne ya sanya kawai ya juya ga gramma ya fara k'ok'arin fahimtar da ita.

Hakan ne ya bata damar zaro wayar ta ta hau kiran Mom a rikice.

Abba kuwa hak'uri ya hau bata yana ta rantsuwa a kan "shi bai san da wata maganar saki ba ma, wato shiyasa granpa ya zuciya sosai!! Haba
no wonder
Ai kuwa yanzu sai an koma wajen granpa an wanke shi wallahi"
Ya k'arashe maganar a fusace yana kallon Ummi.

A fusace itama gramma ta cillo masa takardar hannu nata tana cewa
"Wallahi zan yi matuk'ar b'ata maka,bana son rainin hankali, ko a mafarki In aka tasheni na san rubutunka kai da y'an uwan ka."

Durk'usawa ya yi ya fara k'ok'arin d'aukar takardar yana kallon gramma a ransa
yana cewa 'yanzu kam ya samu mafita k'arya Ummi ta k'are!! Dama ace cewa ta yi a baki ya fad'a mata tou da da sauk'i, a rubuce kuwa ai ko hauka ake dole a gano inda rubutu ya bambam ta.'
Hannu ya kai kan takardar ya d'auka,bai kalla ba sai da ya mik'e...

A take gabansa ya yi mugun fad'uwa ya k'urawa takardar idanu yana k'ok'arin tuno yaushe ya rubuta....
Tilastawa kwakwalwarshin da ya yi ne ya haddasa masa jiri ya tafi yuuuu zai fad'i.
Da sauri Likita da suka shigo tare da Mom yanzu ya yi saurin taroshi yana
"Be careful,wat happen again??"
Ya yi maganar yana kallon su gramma.

SO DA BURI Where stories live. Discover now