1.

1.7K 149 11
                                    

MARYAMA MARYAM 1.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

TUSHEN GININ..

Yanayine na shigowar sanyi, ya kasance kowa na cikin gida dan sanyi dake ratsa mutane baya barin kowa fita, ya zama mutum baya sanin wucewan lokaci da tafiyarshi har sai ya duba agogo.

Ƙarfe sha ɗaya na safiyar ranar asabar ta shigo cikin gidan, tafiya take cikin harabar gidan tamkar wacce bata son taka ƙasa yanayin tafiyarta kaɗai zai nuna maka cewa ita ɗin yarinya ce mai diri da zubin halitta da Allah ya zuba mata.

Kanta sunkuye ƙasa, duk da ita ɗin ba baƙuwar gidan bace hakan bai sata jin shakkun shiga ciki ba.

Wangale get na gidan aka yi cikin sauri dan jin yadda ake zuba horn, da gudu matuƙin motar yayi harabar cikin gidan dan neman gurin parking, ganin ta tare hanyar ga tafiyarta take cikin nutsuwa ya sata danna horn iya ƙarfina tana fisgar motar tayi kanta gadan gadan.

Dai dai fitowar Ya Nurain ya hango hakan da saurinsa ya ƙarasa wajen yana fizge Maryama a kan hanyar ya mayarta gefe.
"Baki da hankali Maryama."

Juyawa tayi ta kalli mai motar yayin da take fitowa taja ƙaramin tsaki tace.
"Ya Nurain ta cika gadarane tamkar da kuɗin Babanta aka gina gidan, ina Nafisah."

"Ke ɗin ma Maryama, ki daina faɗin irin haka."
Da to ta bishi tana barin wajen ganin ta dumfaro wajensu.

"Da kin tsaya na koya miki hankali marar kunya."
Shine furucin da Maryam ta faɗa tana isa wajen Ya Nurain.

Tsayawa Maryama tayi jin kamar tayi magana sai taga suna gaisawa da Ya Nurain amma idonta a kanta, tsaki taja ciki ciki tana yin part ɗin Ammin Nafisah.

Bayan sun gama gaisuwar ya kawo mata maganar irin gudun da take yi in tana tuƙin yanzu idan ta bugeta fa.

"Rabu da ita Ya Nurain."
Maryam tace tana girgiza kanta dan kwata kwata ta tsani yarinyar tun farkon ganinta da ita, jin abunda ta faɗa yasa Nurain yin gaba ya rabu da ita itama ta nufi part ɗinsu.

Tana shiga cikin falon da Ammin Nafisah na zaune tana duba kaya da aka kawo mata dan sayawa Nafisah taji sallamar Maryama, da murmushi ta amsa tana cewa.
"Lallai yau za ayi ruwa da kankara Maryama."

Kyataccen murmushi tayi tana durƙusawa har ƙasa tace.
"Ina kwana Ammi?"

"Lafiya lau ya su Maminki? jiya na leƙa sun fita da Zaid kuna wajen Kaku lokacin."

"Eh sunje kasuwa nima na dawo basu dawo ba."

"Eyyerh Sadeeya bata iya bada aiken ga masu aiki sai da kanta, ke da take dake kina bakya zama, ganin ma ƙaramar yarinya take miki."

Murmushi tayi tace.
"Eh gani take ba zamu saya mata dai-dai ba, Nafisah fa."

"Tana ɗaki kinga wasu kaya nake zaɓa mata wai tazo ta tayani zaɓa taƙi wai kunya take ji."

Dariya tayi tana tashi tace.
"Bari in duba ta."

Ɗakinsu Nafisah tayi, kwance ta sameta tana waya da saurayinta wanda shine zata aura, gefen fadon ta samu ta zauna tana sauraton yadda ake musayar kalaman soyayya tsakaninsu har suka gama ta kashe wayar ta tashi tana cewa.
"Kinga sister ko wanka banyi ba."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now