18.

370 58 0
                                    

MARYAMA MARYAM 18.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Washegarin ranar Maryam ta tashi da kudurin da ta kwana dashi a ranta, bata jin zata iya biyewa Faruq ta cuci kanta dan taya shi fita haƙƙin wata can daban.

Tana zaune tun da ta farka tayi kwalliyar ta tana duba agogon dake jikin bangon ginin ɗakinta dan duba lokacin da zai iya fita ko wani dakika ɗaya dai dai yake da dagowar idanunta ta kai kallonta ga agogon dan gudun kar lokaci ya kure mata.

Tana gani manuniyar cikin gidan agogo ya nuna mata dai-dai a irin wannan lokacin yake fita ta tashi da hanzarinta tana karawa kanta turare tare da fice a cikin ɗakin.

Dai dai suka fito cikin ɗakunan su suka haɗa idanu ko wanne ya aika wa ɗan uwansa saƙon gaisuwar safiya ta hanyar murmushi kafin su ƙarasa ga junansu suka rumgume.

"Good morning Babyna."
Shine furucin da Maryam tayi bayan ƙara ƙarfin rumgumar da tama Ya Faruq.

"Morning My Dear ya daren?"
Abin da Faruq ya faɗa bayan ya kai bakinsa saman goshinta ya sumbata dan shi kansa shaidane ga kewar matarsa da yayi ga irin tsawon da daren jiya ya masa.

Shigewa tayi jikinsa sosai yana shaƙar ƙamshin jikinta tace.
"Daren jiya akwai tsayi tamkar dare biyu aka haɗa."

Gareshi ma hakane dan haka ya sassauta riƙon da ya mata tare da fara takawa daga inda suke yana jan hannunta yace.
"Nima hakan ya zame mini sai dai ba yanda na iya, zan wuce aiki kar na makara."

Tana biye dashi hannunshi tsarke cikin nata bata iya furta ko kalma ɗaya ba har suka sauƙa tare da ficewa cikin falon suka isa gaban motarsa bayan ya buɗe ya shiga ya kallonta.

Ƙoƙari fa take ta ƙara samun gurbi cikin zuciyarsa so take sonta ya zame masa komai nata duk da yana ƙoƙarin nuna mata hakan tana son ƙari.

Cikin jikinsa ta shige ta ɗaura hannayenta saman wuyansa ta saƙale tana dubanshi.
"Babyna yau ko kiss ɗin bye bye bazan samu ba."

Hannuwansa saman kugunta ya ƙara matso da ita daf dashi yace.
"Zaki samu Dearest zo kiga."

Bai iya ƙarasa maganar ba ta rufe bakinsa ta hanyar haɗa wa da nata suka fara ƙoƙarin mantawa da komai da kowa kafin ya fargar da su da tuni cewa fita zai yi.

Sakin juna su kayi ta koma ciki ya kunna motar ya fita ya buɗe get ɗin ya koma ya fitar da motar ya sauƙa ya rufe get ɗin a ranshi yana mitar dole ya nemi mai buɗewa.

Da farin ciki tattare da annuri shine kwance saman fuskarta in da tana gani nan da lokaci kaɗan zata mallakeshi.

Tana ƙoƙarin hawa stairs Maryama ta sauƙo suka bi juna da sakon harara.

Maryama ta ja tsaki tare da faɗin.
"Iska yana wahalar da mai kayan kara."

Baya Maryam ta dawo dan maganganun Maryama tamkar a gabanta tayi ta tsaya tace.
"Daɗinta shi mai kayan karan ya damu da abinsa ba kamar wanda bai san da zamanta gidan ba, da ita da babu duk ɗayane gurinsa."

Juyawa Maryama tayi ta kalli Maryam daga sama har ƙasa ta kwashe da dariya tace.
"Wallahi kina bani tausayi, Ya Faruq da ina da niyar samun gurbi cikin zuciyarsa da ko kaɗan ba zaki samu gurbi cikinsa ba, kawai dai da ke dashi duk bakwa gabana."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now