10.

390 46 1
                                    

MARYAMA MARYAM 10.


Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Da safe karfe bakwai suka ɗau hanya tare da Ya Faruq da Abba ya ƙira yama tas yace ya biyosu duk da ya nuna zai bi jirgi zuwa gobe ba zai iya tuƙi daga Abuja har Maiduguri ba amma Abba ya sashi dole biyosu.

Ɗan abinda zai buƙata ya ɗauka ya kulle gidan kafin su ɗauki hanya.
Karfe takwas na dare suka isa dan sun tsatstsaya sallah a duk garin daya kamasu a gaji suka isa bayan sun sallami mazan suka yi gida.

Da suka isa sallah suka yi suka ci abinci dan ma koshe suke Ya Faruq duk inda suka tsaya sallah sai ya saya musu abinci.
Daya shiga part ɗin samarin ɗakin Zaid ya sauƙa dan har lokacin maganar fatar baki bata haɗasa da Ya Nurain.

Sai safiya aka gansa dan tun daren kin fita yayi.

Ranar ta kasance safiyar Alhamis har karfe goma Maryama tana kwance shame shame tana bacci bata san inda kanta yake ba har karfe sha biyu shima hayaniya mutane shi ya farkar da ita.
Brush kawai tayi ta fito tana fita dan neman abinci a cikinta dan yunwar da take ji.

Cikin kitchen ɗin ta tarar mutane ya sata tsayawa waje ta hango Aunty Hawwah autarsu Maminta.
Da hannu ta mata alamar yunwa take ji ta ɗaga mata itama hannu alamar tana zuwa hakan yasa ta koma ɗakinta dan jiranta.

Da kallo Nafisa dake zaune ta bita dashi.
"Wai ke haka zaki zauna ba wanka ɗaya fa ta kusa."

"To ina ruwanki ni yau wankar ne ma bana jin yi ki barni da yunwar cikina."

"An koyi ƙazamar amarya dalla ki tashi kiyi wanka ko in ƙira Mami."

Baki Maryama ta murguɗa ta juya mata baya.

"Bazan yi ba ina da niyar yi ma na fasa."

Aunty Hawwah dake shigowa tace.
"Aiko sai kinyi, ina aka taɓa amaryar da bata wanka."

Baki ta turo tana ɓata rai idanunta kamar su zubo tana hararan Nafisa.
"Aunty Hawwah zan yi amma yunwa nake ji ki taimaka in fara cin abinci sai in yi."

"Ba zan baki abinci sai kinyi wanka." Aunty Hawwah tace tana ajiye plate din data haɗa mata abinci ta kawo.

Ganin dagaske take yasa ta tashi da sauri ta faɗa bathroom ɗinta, Aunty Hawwah ta tashi ta tsaya baƙin kofar tace.
"Ki tabbatar kinyi wanka da sabulun dana baki inko ba haka ba zaki sake wani."

Daga cikin bathroom ɗin ta dinga turo baki tana ɓata rai haka tayi wanka da sabulu mai kamshi da ta haɗa na hannu ta bata tun aurenta saura wata ɗaya tace tana wanka dashi taƙi sai zuwansu ta sata dole ta fara yi.

Mintuna kaɗan taci ta fito tana shirin neman kayan sawa Aunty Hawwah tace.
"Ga shaddar nan ita zaki saka."

Ɗauka tayi ta saka ta shafa mai da turare ta dawo ta zauna Aunty Hawwah ta mika mata abincinta ta hau ci.
Tas ta cinye dan ba karamin yunwa take ji ba tasha ruwa Aunty Hawwah ta fita da plate din tace ta zauna saboda baki suna shigowa.

Bayan fitarta Nafisa ta dubi Maryama tace.

"Wai Maryama haka za ayi aure ba ƙawaye ba komai salam ba ɗan gishiri ko ɗan walima ku haɗa mana man."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now