7.

404 60 0
                                    

MARYAMA MARYAM 7

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

CIGABAN GININ.

Sallamar Maminta shi ya sata buɗe idanunta tana kallonta ta shigo tana zama bakin gado tare da ƙiran sunata.
"Maryama."

"Na'am Mami."
Tace tana maida kanta ƙasa.

"Magana za muyi Maryama ina so ki faɗa min gaskiya tsakanin ki da Allah shin zaki iya auren Yayanki har kuyi zaman aure duk abubuwan da suka faru duk da shi ya fara nuna son aurenki, ina ganin Umar tamkar ɗana amma hakan bazai sa in ya wulaƙanta mini ke bazan ji zafi ba."

Kan Maryama ƙasa kamar ba zata ce wani abun ba ta buɗe baki tace.
"Mami ni kaina bansan mai yake faruwa ba ki tayani da addu'a kawai, Mami Abbi yana so naga farin ciki a tattare da shi, ko da Ya Faruq bai fara nuna haka ba in har Abbi ne ya haɗamu zan karɓa hannu bibbiyu."

Murmushi kawai Mami tayi tace.
"Shikenan Allah sanya alheri ya nuna mana."

Ba tace komai ba ta rufe fuskarta da hannunta tana murmushi itama Mamin murmushi tayi tana tashi ta fita.

...

Da dare ya turo mata text yana mata ya jiki ta tura masa tayi taji sauƙi ai sosai.

Yana zaune saƙon ya samesa murmushi kawai yayi bayan ya karanta.
Baya jin zai iya kai nan da karshen week kafin ya tafi dan sakata cikin idanunsa ba, yana son ganinta sosai.

Cikin satin aiki yake sosai dan samun sauƙin aikin da zai zo masa next ko daman ƙiranta bai yi ba sosai sau ɗaya yake ƙiranta a waya suke gaisawa.

Bayan samun sauƙin aikin yasa ya nemi hutun one week, sai ranar da jirginsu zai tashi zuwa Maiduguri ya sanar dasu yana hanya.

Itama ƙiranta yayi ya sanar da ita yana hanya zai zo ganinta musamman dan ita yazo.

Tunda suka gama wayar ta kasa saita kanta da zuciyarta gani take tamkar mafarki take wai yau Ya Faruq ne zai zo mata a matsayin saurayinta ba Yayanta mai cin zalinta ba.

Bata iya masa komai na taransa ba bayan tayi wanka ta wuce part ɗin Kaku tayi kwanciyarta.

Jirginsu na sauka ya sanar Nurain yazo ɗaukarsa, sun kusa isa gida Ya Faruq ya kalli Nurain da hankalinsa ke titi yace.
"How was Maryam."

"She's fine." Ya Nurain yace hankalinshi akan titi har suka isa gida.

Bayan sun shiga cikin gidan ya sauƙa part ɗinsu huta gajiya yayi ya tafi part ɗin Mami Nurain ya fita, bayan sun gaisa ta kawo masa abincin data girka masa sanin yana hanya.

Yaci yaji daɗin sa yace.
"Kamar kinsan nayi kewar abincinki."

"Shi yasa na dafa maka da kaina." Mami tace tana bashi guri.

Daya gama ya leƙa yace mata zai shiga gurin Kaku tace to a ranta kuma tana mamakin wai Umar Faruq ne yake son ƴarta Maryama yarinyar da ba jituwa tsakanin su.

Yana zaune saman kujera dake falon Kaku ba kowa ƙira na uku kenan yana mata bata ɗauka ya tura mata saƙo dan jiran amsarta.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now