15.

377 55 0
                                    

MARYAMA MARYAM 15.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Washegari ranar asabar suka halllara gidan Baba Musa dashi da Abba da Abbi da Yayan Aunty Saleema, acan suka tarar ƴan uwan Baba Musa ma sun zo aka tattaunawa.

Bangaren Maryama kam da ƙaramin ciwon mara da ciki ta farka amma haka ta daure.

Bayan gaisuwa da addu'o'i suka gabatar da abinda ya kaisu aka bawa Ya Faruq auren Maryama Abbi ya bada sadaki dubu ɗari da kudin komai da komai dubu ɗari biyar aka yanke ranar ɗaurin aure nan da watanni uku dan shiryawa bikin.

Godiya su kayi kafin su baro gidan Abba ya saka Ya Faruq gaba yana masa faɗa har ya zo nasiha kafin su ƙarasa gida.

Da suka isa Abba ya tara dukkan ahlin a bangaren Kaku tun daga Mami, Ammi, Abba da Ya Nurain hatta Zaid da twins suna gurin da Aunty Saleema ya buɗe taron da addu'a.

"Assalamu alaikum sannunku dukkanku kun san musabbabin taron nan dai akan Umar Faruq ne wasu cikinku sun san yadda aka gudanar da aurensa da Maryama wasun ku basu sani ba to wanda suka sani yau munje mun samu iyayen Maryam anyi magana an bashi aurenta zuwa nanda watanni uku."

Bayan gama sauraron bayanin Abba Kaku tace.
"Yanzu shi Umarun sai da ya taso da maganar nan bai hakura ba."

"Mu musu fatan zaman lafiya kawai Allah haɗa kansu."
Abba ya tari numfashinta da sauri.

Addu'ar samun nasara da zaman lafiya suka musu kowa ya watse a gurin suka bar kaku na mita.

Tun da Mami ta shiga ɗaki hankalinta ya kasa kwanciya ta shiga tashin hankali da jin maganar mijinta akan ƴartan, bata taɓa tsammani haka ya faru a auren ba da ba zata taɓa yarda Maryama ta auri Umar Faruq ba har azo maganar yi mata kishiya.

Nawa Maryama take? Duka duka shekararta goma sha tara ina ita ina kishiya, Maryama bata da wayo, Maryam ta fita wayo da wayewa, Maryama banda rashin ji ba abinda ta iya yaushe ma tasan soyayya balle kula da miji da har za'a fara mata maganar zama da kishiya.

Ina laifin ma auren so da kauna su kayi ashe Umar Faruq ba son ƴarta Maryama yake ba, Maryama har ta iya ɓoye mata haka.

"Sadeeya lafiya."
Taji muryar Abbi juya tayi ta bar bakin window ta ƙarasa wajensa.

"Abbin Nurain akwai matsala fa akan maganar nan ina tausayin Maryama bana jin zata iya zama da kishiya duk rashin jinta."

Hannun matarsa ya kama ya zauna yana zaunarta yace.
"Ki mata fatan alheri Sadeeya inshaAllah nata jarabawar kenan inshaAllah zata samu nasara kin manta Maryamanki bata ɗaukar raini."
Abbi ya ƙarasa yana dariya.

Murmushin dole tayi tace.
"Duk da haka kenan ma ka goyi bayanta akan rashin jinta."

"Bance ba nasan dai kishiya ba zata raina min Maryama ba."

"Shikenan Allah basu zaman lafiya mai yasa baka sanar dani cewa Umar Faruq ba Maryama yake so ba ka haɗa aurensu."

"Bana jin zaki yarda lokacin shi yasa na ɓoye miki."

...

Yana komawa hotel ɗin ya fara haɗa abubuwansa tana kallonsa tana zaune har ya gama yace.
"Mu tafi."

MARYAMA MARYAMNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ