41.

455 70 6
                                    

MARYAMA MARYAM 41.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Da safe Ya Faruq ya shigo part ɗin Kaku ya samu Maryama tana cin faten wake da Kaku ta dafa mata, Kaku na zaune gefenta sai hira take mata.

Guri ya samu ya zauna kusa da Maryama ya gaishe da Kaku ya juya yana kallon Maryama tace.
"Ina kwana?"

"Lafiya lau ya Babynmu?"

Bata mishi magana ba taci gaba da cin abincinta ya karɓi spoon ɗin ya fara ci. Tare suka cinye Kaku tace ta ƙara musu suka ce ya ishesu.

Bayan sun gama yace tayi wanka suje gaishe da Mami da Abbi da Abba kar su Abbi su fita, girgiza kai tayi alamar a'a yayi ƙasa da murya yace.
"Ba fa wanda ya sani, ki shirya muje kawai."

"Kaje ni anjima zanje."

"To in ji ɗaya ne sai na faɗa musu."

Ai bai gama maganar ba ta miƙe tsaye tace.
"Bari in yi wanka."

Daga haka ta wuce ciki Kaku ta dubeshi tace.
"Haka Kubrah ma tayi laulayin haihuwarka mugun ci ga yau lafiya gobe sauƙi."

Murmushi kawai yake kaku tana bashi labarin da ya wuce har Maryama tayi wanka ta saka kaya ta fito da babban hijab da ta ɗauki saran sawa ya rasa na menene.

Sallama suka ma Kaku za suje cikin gida su dawo tace.
"Mai zan dafa miki kafin ki dawo."

"Koma mai nasan dai in kika dafa zanci."
Maryama tace suka fita.

Bangaren Ammi suka fara shiga suka gaisheta sai bin Maryama take da kallo.

Bayan sun gaisa suka wuce falon Abba suka gaishesa da fara'a ya amsa yana musu nasiha kafin su wuce part ɗin Mami, Mami kam da dama tana zargin ƴartan ta ga yadda ta ƙara haske sai ta tabbatar cikine da ita.
Gaisheta su kayi Maryama sai nuƙu nuƙu take sai ta bawa Mami dariya tana mamaki a ranta ashe akwai ranar da Maryama za tayi hankali har taji kunya.

Abbi suka gaishe inda shima duk yawanci nasiha ya musu musamman Ya Faruq duk yawanci akansa ne.

Daga nan suka fito yace suje gidan Nafisa da Nurain da murnarta tace to suka tafi.

Gidan Nurain suka fara zuwa wanda ganinsu yasa komai ya wuce a zuciyarshi ya sake fuskarshi suka shiga hira da Ya Faruq.

Maryama da Surayya ma guri suka samu cikin ɗakin Surayya sukai ta hira bayan ruwa da abin ci da Surayya ta kawo mata.

Awansu biyu suka musu sallama zasu tafi suka musu rakiya har mota kafin koma.

Haka gidan Nafisa ma tayi murnar ganinsu sosai ta saka Maryama gaba tana kallonta, da kallon ya ishi Maryama tace.
"Dalla ni ki daina kallona kar kisa na kware."

"To ba dole ba irin wannan rabo haka da wuri ashe da rabon zanga ƴaƴanku da Ya Faruq."

"Ke kika sani magulmaciya."
Maryama tace tana tashi Nafisa tayi dariya tabi bayanta suka fita ta musu rakiya har mota kafin ta karɓi ƴarta Mimi data maƙale da Maryama.

"Allah kiyaye hanya Yaya sai munzo suna."

Kallon Maryama Ya Faruq yayi ta ɗauke kanta ya kalli Nafisa yace.
"To Sister sai kunzo."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now