17.

370 57 3
                                    

MARYAMA MARYAM 17.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Washegari aka fara shirin kai amarya gidanta, cikin ƴan uwanta Aunty Sameera da mata biyune zasu kaita dan gari ba kusa ba ga kuɗin jirgin zai yi yawa yasa aka zaɓi mutum uku.

Karfe sha biyun safe jirginsu ya sauƙa a airport ɗin Abuja basu tsaya ko ina ba bayan saukarsu sai kofar gidanshi.

Har cikin ɗakinta suka zaunarta suna mata nasiha maganar Aunty Sameera kawai cewa take.
"Kar ki raga mata Maryam yarinyar nan bata da kunya sai kin koya mata hankali ni dai kawai ki kwaci ƴan cinki da kan ki ba sai an kwata miki ba."

Duk huɗubar da Aunty Sameera na mata yana shiga kunnenta ban da wanda Momynta take mata kullum.

Tun da suka kawota suka samu Aunty Hawwah da Nafisa da Maryama zaune falon ƙasa.
Aunty Hawwah ta saka Maryama yin wanka ta saka lace cikin kayan akwatinta da Abba ya haɗa mata, lace ne mai kyau da yabi dirin jikinta ya zauna ya fito da farin fatarta, ba tayi wani hayaniyar kwalliya ba Nafisah ta mata dauri tana zaune ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya tana kaɗawa.

Da suka shigo da Maryam fuskarta lulluɓe suka zaunarta saman kujera suma suka zauna suna gaishe da Aunty Hawwah ta amsa tana musu ya hanya.

Aunty Sameera ne ta watsa Maryama kallo ɗaya ta ɗauke kai ta buɗe baki tace.
"To ga amarya mun kawota fatan ko wacce zata sauƙe kai su zauna lafiya."

Murmushi Aunty Hawwah tayi tace.
"Maryam ba yarinya bace fatan ba zata biyewa Maryama ba su zauna lafiya."

"Haka itama Maryama ba yarinya bace fatan zata girma mata ta bata girmanta."
Aunty Sameera ta faɗa bayan gama maganar Aunty Hawwah.

"Hakane shi yasa nace itace babba sai ta kama girmanta."

Kasa magana Aunty Sameera tayi ta tashi ta daga Maryam da niyarta magana yaci gaba da nisa zata buɗe fuskarta ta saka baki.

Da suka ajiyeta ɗakinta suka zauna nan.

Dariya Nafisa ta saka bayan wucewarsu tace.
"Aunty kin min maganinsu."

"Rabu dasu Maryama ce sai ta koya mata hankali."
Tace tana kwafa ta kalli Maryama da hankalinta na ga kallon tv da take ana Avengers a mbc2.

Daren angon bai samu ganin amaryarshi ba.
Ko wacce ranar da dare danginta su suka shiga kitchen suka dafa musu abinci duk da Faruq ya kawo amma sun girka.

Da safe karfe sha biyu su kayi haraman tafiya su Aunty Sameera su suka fara wucewa kafin su Nafisah hasr bakin motarshi ta rakosu ya fita kafin ta koma ciki.

Tsaye tsakanin stairs ta hango Maryam tana bin gidan da kallo, ɗauke kai tayi ta wuce kitchen ta ɗan haɗawa kanta abincin rana.

Sauka Maryam tayi ta nufi kitchen ɗinta itama ta buɗe ta gani komai yayi yanda take so ta rufe tana komawa cikin falon ta zauna.

Maryama bata bar kitchen din ba sai da ta gama girkinta tsaf lokacin ƙarfe ɗaya da mintuna, bata ga Maryam ba a falon alama ta jima da bari.
Dakinta ta wuce ta saka lock ta ajiye abincin ta ɗauro alwala tayi sallar azahar taci abincinta ta jawo wayarta ta ƙira Nafisa tana mata ya hanya.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now