8.

360 52 0
                                    

MARYAMA MARYAM 8.

Pharty Bb
Wattpad phartybb.

"Kai lafiyarku kuwa Umar mai haka?"

Muryar Abbi suka tsinca a bakin ƙofa yana shigowa tare dasu Zaid da twinsa da su kayi gurinsu da sauri dan rabasu ganin Abbi ya sasu sakin juna suna ja baya ko wanne na hararan ɗan uwansa.

"Mai ya faru haka da girmanku zaku tsaya dambe abinda ko su Hassan baza suyi ba."
Abba daya ƙarasa wajen yana faɗar haka.

Ba wanda ya iya magana a cikinsu sai huci suke musamman Ya Faruq da yake jin zuciyarsa na zafi tamkar ya fita.

"Ku sameni falona muyi magana."
Daga faɗar haka ya wuce ciki ya barsu tsaya a gurin.

Nurain ne ya fara shiga shima Ya Faruq yabi bayansa.
Maryama na ganin Ya Nurain ya shigo ta tashi zata mishi magana taga shigowar Ya Faruq a bayansa da sauri ta koma ta zauna tana yin ƙasa da kanta.
B

ai bi ko ta kanta ba ya wuce sama falon Abbi.


Abbi, Ya Nurain da Ya Faruq suna zaune Abbi sai binsu yake da idanu yace.
"Mai ya faru Umar mai ya haɗaku da har zai jawo muku aikata irin haka."

Shuru su kayi dukkansu hakan yasa ya ƙara cewa.
"Nurain sanar dani mai ya faru."

"Abbi shi ya fini sanin komai."

"Ƙarya yake Abbi shi ya haddasa komai."
Ya Faruq ya faɗawa Abbi.

"Ya isa to kai faɗa min menene Nurain."
Abba ya dakatar dasu dukkansu yana faɗar haka.

"Abbi akan maganar Maryama ne, munyi saɓanin fahimta tsakaninmu, Maryam yake so ba...."
Sai kuma ya kasa ƙarasa maganar yayi shuru ganin Abbi ya tsura masa ido.

Ganin yayi shuru yasa Abbi cewa.
"Idan na fahimce ka Nurain Maryam yake so ba Maryama ba hakane Umar?"

Ya Faruq kansa ƙasa bai iya bashi amsa ba ya ɗaga.

"Shikenan ku tashi kuje zan samu Haruna muyi magana dashi Allah yasa haka shi yafi alheri."

Ya Nurain ne ya fara tashi sai kuma Ya Faruq da yaji jikinsa yayi sanyi sai yaji nauyin Abbi da ya iya nuna masa ba komai amma hakan hanashi jin wani sanyi a ransa ba, ko ba komai zai samu burin ransa.

Suna fita ya jingina da kujeran da yake zaune bai taɓa tsammani Umar zai zo masa da wannan maganar ba.
Wayarsa ya ciro ya ƙira ƙaninsa ya sanar dashi da dare za suyi magana in yazo kafin ya kashe.

Ya Nurain a falo ya zauna shi kuma Ya Faruq ya fita, tunda ya zauna ya kasa faɗa ma Mami yafi so taji ta bakin Abbi kuma ko ba komai tunda Abbi yaji maganar fatansa kar suce sun fasa haka kawai yake ganin Ya Faruq ɗin da Maryama sunfi dacewa akan Maryam.

Ya Faruq na fita part ɗin Aunty Saleema yayi bayan sun gaisa sai kuma yayi shuru can dai da ta tasan mai ya kawosa ta tashi tana cewa.
"Bari in ƙira maka ƙanwarka ku gaisa nasan ma baku taɓa haɗuwa ba."

"Mun haɗu jiya da ita bata sanar dake ba." Yace da ita.

"May be ta manta ina zuwa." Tace tana wucewa sama.

MARYAMA MARYAMTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon