20.

419 63 0
                                    

MARYAMA MARYAM 20.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Daren ranar masoya dukka biyun sun kwana ba farin ciki ko wanne zuciyarshi da abinda yake saƙa masa.

Haka suka wayi gari ya zama weekend ba aiki har karfe goma bata shiga cikin ɗakinsa ba ya sashi bayan yayi wanka ya shiga ɗakinsa.

Saman kujera ya ganta kwance tana danna wayarta, ciki ya ƙarasa ya zauna ya dubeta.
"My Dear!"

Ya ƙira ganin ta nuna tamkar bai shigo ba ya ƙara cewa.
"Are you still angry with me."

Bata bashi amsa ba ya sashi isa gurinta ya ɗagata gaba ɗayanta ya zaunarta suna fuskantar juna.
"I'm sorry but you know it's my responsibility to take care of her, za muje Maiduguri da zaran tayi exam kinji."

"Shikenan Allah kaimu lokacin na hakura."
Tunawa da kalaman mahaifiyarta da irin abubuwan da suka shirya ya sata nuna masa ta hakura da komai.

Yaji daɗi sosai data fahimce shi ta hakura nan ya lallaɓata ta musu breakfast suka ci.

...

Konduga, Borno State .

Tafiya take da motarta tana bin layin duk da an samu canji dayawa daga gine gine hakan bai sa ta mance layin da tsawon shekara takwas bata bi ba.

A kofar gidan dake cike da ɗalibai tayi parkinga tana sauƙa tabi gidan da kallo.
Nan ne dai da mahaifiyarta ta kawota akan kawarta da yayi sanadiyar rabuwarsu har abada.

Cikin gidan ta nufa tana sallama manyan garadan gidan suka amsa mata bayan sun gaisa ta tambayesu shi suka mata jagoranci zuwa wajensa.

Da sallama ta shiga ta samu guri ta zauna ya amsa yana binta da kallo dan tunawa da inda yasan mai fuskar.

"Ina wuni ya aiki?"
Shine furucin da Aunty Saleema tayi tana ƙasa da kanta dan irin kallon da yake mata ya sata shan jinin jikinta kar fa ya ƙi bata taimako dan irin abinda da suka masa a baya.

Dubanta yayi sosai duk da shekaru sunja hakan bai sa ya kasa tuna mallakiyar fuskar ba yace.
"Salamatu."

"Na'am Malam ya hakuri damu."

"Ashe in tayi tsami ana jin warin abu dagaske ne, shekara nawa rabona dake tun da buƙatar ku ta biya kuka watsar ni, kuka mance da ni yanzu mai kike bukata in taimaka miki kenan Salamatu."

"Haƙuri za kayi malam wannan karan ba irin na da bane wannan dabanne akan ƴa tace in baka taimaka min ba wa zaka taimaka."

Kai ya girgiza.
"Salamatu kun bani mamaki da mahaifiyarki albarkaci ɗaya ki ka ci cewa ba kanki bane kan ƴar kine sannan kin nuna ni ɗin ina da amfani menene matsalar ƴarki?"

Nutsuwa taji ya sauka a ruhinta ta gabatar masa da buƙatarsu yayi tunani da dube dubenshi yace.
"Mijin ƴarki na da addu'o'i sosai na tsare jikinsa sai tazo da kanta, amma yanzu zan baki wasu abubuwa ki kai mata ta fara amfani dasu zuwa kafin ta zo."

"Godiya nake Malam Allah biyaka."

Magungunan ya haɗa ya bata guda biyu gari ya mata bayani ta amsa ta jefa a jaka ta cikashi da kuɗi ta tafi.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now