19.

396 57 2
                                    

MARYAMA MARYAM 19.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Maryam bata sauƙe hannunta ba taji sauƙar mari saman fuskarta ta gwalo idanunta ta kalli Maryama da karfin halin ramawa kafin ta yi wani motsin Maryama ta hankaɗata saman miyar dake zube ƙasa tayi kanta ta fincikota ta fara kai mata bugu.

Bugu kawai suke kaiwa juna cikin zubebbiyar miyar dama Maryama na cikin jin haushin Maryam hakan yasa ta rufe idanunta kawai duka take yi ta ko ina ta samu.

Sauƙowar Ya Faruq kenan da ya fara jin hayaniyar ya fito duk yaji maganganunsu har da marin da Maryam ta ma Maryama itama ta rama.

Ganin abinsu ya fara wuce gona da iri kowacce ƙoƙarinta ta ma ƴar uwarta rauni ya sashi ƙarasa ya shiga takaninsu ya rabusu Maryama na ƙoƙarin kaiwa Maryam wani dukan ya bata mari a fuskarta da ya sata dubanshi cike da masifa tace.
"Ka mare ni to wallahi a kanta zan rama akan mai ita ta dake ni kai ka dakeni ni jakarku ce ka sake ni nace."

"Get in Maryam."
Ya Faruq ya faɗa da tsawanshi ta bar gurin ta wuce sama dan yadda Maryama ta birkice ta san yana sakinta zata yi kanti.

"Wallahi kaji na rantse sai na rama ita uwata ce ka dake ni na barta."
Maryama ta faɗa tana ƙoƙarin kwatar kanta daga riƙon da ya mata yana ƙara matseta jikinsa yana son mata magana ta hanashi.

Ganin bata da niyar barin faɗan ya sashi ɗaukarta gaba ɗayanta ya wuce sama da ita, saman kujeran falonta ya ajiyeta tana kokarin tashi ya fizgota ya sata jikinsa tare da rumgumeta ya matse.
"Ke wai bakya hakura ko da yake haka kike ashe, ina ji fa laifinki ne Maryama ke kika fara buɗe mata abu."

Har lokacin tana ƙoƙarin kwatar kanta daga riƙon da ya mata tace.
"To akan mai zata mare ni ta bari nima duk ranar dana dafa maka abinci ta buɗe mana."

"Zuwa yaushe kenan?"

Taji tambayar da ya sata ɗaga ido ta dubeshi yana kallon cikin kwayar idanunta.
Ɗauke kai tayi tace.
"Ni dai sai na rama ko ba yau ba."

"Kin hakura yau ɗin."

"Eh ni ka sakeni."

Sai lokacin ya farga da irin riƙon da ya mata ya sassauta ta tashi tana nufan kofa yayi saurin riƙota.

"Ina kuma za kije ba mun gama magana."

"To ba lunch zan ɗaura ba."

Zaunarta yayi saman kujera yace.
"Bari in sayo miki kiyi zamanki kar ki fita dan Allah."

Kai ta ɗaga masa tana juyarwa gefe ya tashi ya fita yana sauƙe ajiyar zuciya da ganin Maryama ta haƙura rana ta farko da ya gani an mata abu ta hakura duk da ta rama.

Ba wai ta haƙura bane haka kawai cikin zuciyarta tunanin abun da zata mata ta rama kawai take yi.

..

Ɗakin Maryam ya shiga ya sameta zaune ta fito ɗaure da towel bayan shigarta tayi wanka, ƙarasa gurinta yai ya zauna yana dubanta ta haɗa rai.

Rumgumeta yayi cikin kwantar da murya yace.
"Haba Dear ki dai na biyewa ƙaramar yarinya kuna tace nace zata rai naki dubi yanzu abinda tasa ku yi gaba ɗayanku."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now