4.

456 58 0
                                    

MARYAMA MARYAM 4.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Ahmadi da Haruna ƴaƴa ga Kaku tsohuwa mai suna Hamsatu mazauniyar garin Damaturu jihar Yobe a unguwar Sabon Fegi.

Abbi Ahmad shine ɗan farinta bayansa Abba Harun daga baya tayi ta haihuwar basa zama har rasuwar mahaifinsu.

Haka suka taso yaranta biyu kwal Ahmad a iya sakandare ya tsaya da taimakonsa dana Mahaifyarsu Harun ya samu karatu mai karfi.

Tare su kayi aure bayan samuwar aikin Harun a garin Maiduguri jihar Borno, a nan ya ajiye matarsa su kuma sukaci gaba da zama a Damaturu.

Abba Harun shi Allah ya fara bawa haihuwar namiji Umar Faruq sai Zaid sai Nafisa, sai Abbi Ahmad, Nurain ya haifa bayan haihuwar Umar Faruq sai Twins da Zaid ya fisu.

Tun da su kayi wayo Abba ya ɗaukesu zuwa Maiduguri dan karatu acan gurinsa suke zama da ƴaƴansa.
Bayan tafiyarsu Allah ya bawa Abbi Maryama dan har sun cire rabo da sake samun haihuwar daga nan kuma ya tsaya.

Bayan haihuwar Maryama Abba ya takurawa Abbi suka dwo gidan daya gina musu a Maiduguri harda Kaku da dakyar tazo lokacin Maryama nada Shekarau takwas a duniya.

Tun da suka dawo yara mazan ke nunawa ƴar autansu Maryama so banda Umar Faruq da ko suna zaune sai dai yayi shuru ko hankalinshi akan Tv, kwata kwata ta tsani halinsa na shariya da rashin kulawa da yake mata.

Ita da Nafisa sun kulle sosai duk da Nafisa ta girmeta hakan bai sa jin kansu ɗaya ba, haka Ammi da Mami.
A cikin haka Abba ya ƙara aure ya auri Aunty Saleema da har yanzu tsawon shekara bakwai aurensu bata taɓa haihuwa ba.

Tana zaune bakin balcony na ɗakinsu Nurain tana karatun litattafinta da gobe za su fara test na zangon farko da suna gamawa sai jarabawar da za suyi na karshe na sakandare, taji ƙarar horn da ƙarfi.

Yi ake ana sake yi tana ta mamaki mai yin bata iya motsawa ba, tasan dai Abba baya dawowa da wuri haka, Abbi kuma yayi tafiya.
Mai yin dai bai fasa ba ita kuma bata tashi ta buɗe get ɗin ba.

Ganin yana sauri ya sakashi sauƙa a motar ya shiga cikin gidan da saurinsa yayi mugun mamakin ganinta zaune tana ganin mai shigowar ta ɗauke kanta taci gaba da karatunta tana cewa da tasan shine ma da bata wahalar da kanta ta tsaya tunanin wanene ba.

Tsayuwar mutum taji saman kanta, sanin wanene yasa taci gaba da karatunta kamar Allah bai ajiye ruwan halittarsa a wajen ba.

"Ke ɗago kanki ki kalleni."
Taji ya faɗa mata da tunda take da wayo maganan kirki bai taɓa haɗasu ba.

Kanta ta ɗaga tana juyawa gefen hagu da dama ta mayar kanta ƙasa tace.
"Babu ke anan ai."

Fizgota taji anyi ya tayarta tsaye tana ƙoƙarin kwace jikinta ya watsa mata mari a saman fuskarta yace.
"Wato kina ji ina horn kika ƙi tashi ki buɗe min get sannan in zo ina miki magana ki tsaya raina mini hankali."

"Ai ni ba mai gadinka bace ko ka ajiyeni ne."
Maryama tace tana ƙoƙarin mai da hawayen idanunta dan karta karaya sosai marin ya shigeta.

Wani marin ya kai mata yana sakinta bai iya cewa komai ba ya wuce ɗakin.

"Allah ya isana."
Cak ya tsaya jin maganarta yana juyawa ya kalleta da gudu tayi cikin part ɗinsu, tsaki yayi yana kwafa zai kamatane ya faɗa a zuciyarshi.
Abinda zai ɗauka ya shiga ya ɗauka ya fito ya fita.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now