23.

425 55 4
                                    

MARYAMA MARYAM 23.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Tun ranar Ya Faruq ya fita harkar Maryama ko abincinta baya ci baya shiga ɗakinta ko taɓa ta sai ya zama dole.
A haka zamansu ya ɗore har ta fara exam ya nema mata tsohon driver da ya taɓa kaita ya cigaba da yi.

In ya zama ita take da girki tana da paper ranar cewa yake ta bari hakan kuma ya mata daɗi dan yana nisanta ta dashi tama daina girkin gaba ɗaya in ba nata ba.

Maryam hakan ya mata daɗi sosai ganin rashin jituwa tsakainsu ya fara wanzuwa.

Sati biyar suka ci suka gama, ana saura paper ɗaya da za suyi a karshe Nafisa ta haihu wanda zai kama in sunyi da kwana biyu za ayi suna.
Da ta ƙira Maryama ta sanarta kamar tayi kuka take ji anma haka ta daure ta samu ta zana exam ɗinta.

A ranar data gama sha biyu, ƙarfe ɗaya a gida ya sameta ta dawo sai fatan samun nasara.

Data dawo Ya Faruq baya gida haushi ya kamata dan taso su tafi ranar.

Ɗakinta tama gyara sosai lungu lungu tayi goge goge ta kimtsa komai ta cire kayan wanki ta wanke ta zaga ta shanya tazo wucewa Maryam ta tsaya hanyar stairs tare da kawarta da tazo mata.

"Zan wuce."
Tace musu tana bin gefe suka juya suka kallon banza su kayi kamar basu jita ba sun ƙi matsawa.

In ran Maryama yayi dubu ya ɓaci basu ankara ba ko waccensu taji sauƙar bucket a kanta da ya sa suka dubeta kowacce riƙe da kanta.

Maryam ta kalleta tace.
"Ni kika daka dan kinga Ya Faruq yana goyon bayanki to yau ko zan miki abinda in ya dawo ba zai ganeki ba."

Harara Maryama ta watsa mata tace.
"Taɓani kiga yadda ake fasa kai a gidan nan wannan kan naki sai na fitar masa da jini."

Kawar Maryam ta dubeta tace.

"Yanzu ke dama Maryam abunda take miki kishiya ta ɗauki hannu ta dakeki ki kyaleta."

"Dalla rufemin bakinki mai wari a gurin."
Maryama tace tana hararanta ta buga tsaki zata wuce Maryam ta fincikota Maryama ta ɗaga bucket ɗin hannunta ta maka mata a hannuwanta da ya sata jin zafi ta saketa.

Ganin hakan yasa kawarta ja baya tace.
"Wallahi Maryam yarinyar nan bata da hankali kinga sai anjima kafin ta mini rauni."

Maryam da bakin ciki ya hanata motsi tana kallo kawarta ta sauƙa ta fita hakan ya harzuƙa zuciyarta ta nufi ƙofar Maryama ta buga taji a kulle tace.
"In ba tsoro ba ki buɗe."

Maryama na zaune ta ɗaga murya tace.
"Bani da lokacin ki mahaukaciya."

Iya ƙarfinta ta buga kofar tace.
"Kece mahaukaciya."

Haka Maryam tayi ta zage zagenta Maryama taƙi ko tari wanda shi ya ƙona ran Maryam tayi ta gama ta bar gurin tana huci.

Maryama na ɗakinta ta cire kayanta na tafiya da duk abunda zata buƙata a akwati ta ajiye a gefe kafin ta sauƙa zagaya ta ciro shanyarta ta goge na gogewa ta saka a wardrobe.

Karfe hudu Ya Faruq ya dawo gidan dan aiki da kuma hutu daya ɗauka ga kuma ticket daya nema musu na tafiyan gobe.

Haka Maryam ta sashi gaba da mita crwa Maryam ta mata rashin kunya har da bugin kawarta da ita.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now