5.

419 61 0
                                    

MARYAMA MARYAM 5.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Da safe tana tashi ko damar break ba tayi ba tasha tea kaɗan tana fita bata jira mai kai ta yazo ba ta tari abin hawa tana tafiya.

Tun da taje Allah Allah take a tashi har taga 1:30pm yayi kafin hankalinta ya kwanta, har aka watse tana zaune tana jiran Uncle yazo, can ta hangosa ya yafi to ta da hannu ta ƙaraso wajensa.

"Aina na ɗauka kin hakura kin tafi, zagaya ki shiga muje."

Ba musu ta buɗe gaban motarsa ta shiga ya shiga yana ja suna barin gurin yana janta da hira duk dan ta saki ranta.

Har layin unguwarsu ya shiga bai ƙarasa ba ya samu gurin da ba mutane yayi parking ya juyo yana kallonta.

"Kin ga mun tsaya anan ko? To maganar tsakanina da ke ne bada iyayenki ba, zaki samu result mai kyau amma har sai nima kin bani abinda nake so."

Bata kawo komai cikin ranta ba tace.

"Zan baka Uncle in har ina dashi dan ina son samun result mai kyau."

Fuskantarta yayi sosai kafin ta ankara ya damko hannuwanta cikin nasa yace.
"One night, just one night and get A+ in your all papers."

Hannunta ta kwace zuciyarta na bugawa da sauri bata taɓa tsammani abinda zai buƙata ba kenan, yanayin tausayi ta koma masa tace.
"Am sorry uncle amma bazan iya ba gwara nayi amfani da abinda yake kaina kayi hakuri."

Murmushi yayi bai ji ko ɗar ba yace.
"Shikenan zaki ko ta resitting in har ina aiki a school ɗin nan ba zaki taɓa samun result mai kyau ba har sai kin bani abinda nake so."

"Ni ba ƴar iska bace bazan aikata abinda kake so ba dama sharri kake nemana dashi to Allah ya fika azzalumi."
Ta karasa maganarta tana buɗe ƙofar motar ta fita.

"Shawara nake baki if kina son samun result mai kyau gobe ki sameni a office nawa in baki address."

Wani mugun harara ta wulla mishi da dararan idanunta ta juya taci gaba da tafiyarta, a kafa ta ƙarasa gida.

Tana isa ko sallama ba tayi ba ta shiga falon, Ya Faruq da Nurain ta samu suna cin abinci.

"Ke wawiya koma kiyi sallama haka aka koya miki."
Ya Faruq ya faɗa yana binta da mugun kallo.

Wani mugun kallo ta watsa masa tana komawa baya tayi sallamar Ya Nurain ne ya amsa shi kuwa tsaki yaja ta wuce ciki fuu kamar zata tashi sama.

"Ka kul la auta fa."

"Bata jine." Yace kawai yana cigaba da cin abincin sa.

Tun da ta shiga ɗaki abinda ya faru take tunawa.
Yanzu fa in dagaske yake fa, kar fa ya hanata samun kyakkyawar result, kar ya sata yin resitting, gashi an fara rufe registration balle tace za tayi a wani makaranta.

Da wannan tunanin har dare yayi ta lallaɓa ta tafi ɓangaren Ammi anan ta tarar Maminta da Aunty Saleema bayan sun gaisa Aunty Saleema tace.
"Ke kam ba'a ganinki Maryama ba irin tawa Maryam ɗin ba."

"Aunty school ne wallahi yake ɓoye ni."

"Allah taimaka an kusa fara paper da zaran kun gama tawa Maryam ɗin za ta dawo gurina sai ku zama ƙawaye."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now