12.

377 49 6
                                    

MARYAMA MARYAM 12.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Da safe Ya Faruq ko takan Maryama bai bi ba ya wuce aikinsa, haka ranar ma Maryama ta wuni ɗakinta bata fita ko nan da falo a ciki take girkinta taci tasha.

Kwana huɗu suka cinye haka duk abin duniya yabi ya ishi Maryama tagaji da cin indomie da shan cornflakes ga kuɗin account nata duk ta cinye a kati da take sawa tana sayan data tana kallo a waya dan kallon tv duk ya fita a ranta.

Karfe sha biyu ta sauƙa tare da kwalin indomie data zuba tarkacen abunda take amfani dashi mai datti da sauran da ya rage, masu kyan ta kai kitchen sauran ta nufi hanyar fita dan zubarwa a dustbing.

Murɗa kofar falon tayi a kulle wato ma kulleta yake ya fita bata sani ba, kwafa tayi tana ajiye masa dattin baƙin ƙofa ta koma kitchen ta fara binciken kayan abincinta ta samu macaroni ta dafa sama sama dan sauri take ta koma ɗakinta, taji alamar buɗe kofa ta leƙa ganin za'a shigo ya sata komawa cikin kitchen din da sauri ta saka lock tare da kashe gas ɗin ta tsaya tana leƙan mai shigowa.

Yana buɗe kofar falon kafarsa na farko da zai saka yaji ya taka abu da hanzari ya kai dubanshi gurin yana jan tsaki da mugun karfi dan ganin abunda ya taka datti, datti ta kawo masa kofa ta ajiye.

Anan ya cire takalminsa yana yin sama, ƙofar ɗakinta ya tsaya yana bugawa da karfi yana cewa.
"Maryama! Maryama ki buɗe kofar nan ki fito ki kwashe waccan dattin da kika ajiye ƙazama kawai wawiya."

Tana cikin kitchen tana kallonsa har hawa saman da yayi yana magana ta kwashe da dariya har da riƙe ciki ganin yadda duk ya hargitse jin ya daina buga kofar ya sata tsayar da dariyarta ta koma gurin abincinta ta deba ta jawo kujera ta zauna ta fara ci ta gwammace ta zauna a kitchen ɗin har ya fita da ta fita ya ganta tasan zata daku.

Bugun da yayi tayi yasa bata fita ba ya ƙara ɓata ransa ya buga kofar da ƙarfi tare da buɗewa ga mamakinsa buɗewa kofar tayi ya shiga da saurinsa yana nemanta bata falon ya duba cikin ɗakinta da yaune shigarsa na farko nan ma bata nan har bathroom ya duba bai ganta ba sai kuma ya fara tambayar kansa ko dai ta fita ne to yaushe? Ta yaya? Kofar dai falon a kulle yake bari kullum.

Fita yayi yana shirin sauƙowa ya hangota tana buɗe kofar kitchen ɗin cikin sanɗa tana hangosa ta koma da sauri ta saka lock tana jingina da murfin ƙofar ta ɗaura hannunta saman kirjinta da ya tsinke ganin ya ganta.

Gurin ya ƙarasa ya tsaya yace.
"Ki fito tun muna cikin ruwan sanyi kar in buɗe kofar nan in sameki."

Daga ciki ta ɗaga murya yanda zaiji tace.
"Wai ni mai na maka? In fito ka dakeni a banza ga jaka."

"Kar ki buɗe kiga in sameki sai na ballaki."
Yace yana ƙoƙarin barin gurin.

Ganin haka ya sata leƙawa ta buɗe a hankali da tazara tsakaninsu tace.
"Gani na buɗe."

Daga inda yake tsaye ya juya ya kalleta yana mai da idonsa gurin data zubar da sharan yace.
"Ki kwashe wancan kazantar ki a gurin can gidana ba bola bane babu kuma gurin ƙazamai irinki."

"To ba zan buɗe in zubar ba naji a kulle shine na bari a gurin ba."

Kanta yayi yace.
"Zaki rufe mini baki kije ki kwashe ko sai na bugeshi yayi jini marar kunya kawai."

MARYAMA MARYAMHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin