29.

424 74 4
                                    

MARYAMA MARYAM 29.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

A hankali Maryama taja kafarta ta nufa cikin gidansu zuciyarta na bugawa da sauri ko wani daƙika tsorone da bata san daga ina yake zuwar mata ba ya dinga ratsa zuciyarta.
Bata san ya zasu karɓeta ba ta tashi ta taho cikin daren nan.

Cikin sanɗa ta tura kofar dake gefen jikin get din gidansu ta leƙa kanta, kamar yadda take tsammanin hakane ba kowa filin gidan hakan shi ya bata damar shiga gaba daya ta tura ƙofar taja ƙafarta ta fara nufan hanyar da zai sadata da part ɗinsu.

Ta kai rabi taji ƙarar horn da ya haddasa mata tsoro ta juya a harzuƙe hasken wutar motar daya dalle mata idanu bai bata damar ganin motar da kyau ba ta tsaya jikinta na rawa.

Yayi mugun mamakin ganinta da saurin isowarta cikin garin hakan yasa ko kashe motar bai yi ba ya buɗe da sauri ya fito ya nufeta.

Tana ganinshi taji gabanta ya fadi tayi baya da saurin ganin ya nufota ya sata sakin akwatinta tayi part ɗin Kaku da yafi kusa da ita da gudunta ya bi bayanta cikin sauri yana jan akwatinta.

Falon ta faɗa tana shirin rufewa ya shigo ya turata baya ya rufe ƙofar tare da fizgota ya watsa mata mari cikin fushi yace.
"Are you mad? Zaki iya tahowa ke ɗaya daga Abuja har Maiduguri? Mai aka miki."

Kuka ta fashe dashi dan marin ya shigeta tana ƙoƙarin kwace jikinta tace.
"To dolene sai na zauna dakai na gaji da ƙaddararren aurenka a kaina, ka sake ni."

Da mugun mamaki yake dubanta yace.
"Saki! maimaita mai kika ce."

"Cewa nayi ka sake ni ko dole sai na zauna da kai ba sona kake ba nima kuma bana so biyayya nayi kuma Allah yaga nayi ƙoƙarin na bi umarnin iyayena."

Turata yayi tayi baya yace.
"Baki da hankali banga ranar yin hankalinki ba."

Daga haka ya buɗe ƙofar yaga tahowar Kaku ya koma zai ɗagota tayi baya ta shige ɗakin Kaku ya rabu da ita ya fita suka haɗu da ita da kallon mamaki ta bishi tace.
"Umaru sauƙar yaushe?"

"Ban jima ba ina zuwa."
Yace ya bar gurin yaje ya kashe motarshi ya wuce part ɗin samarin gidan, ɗakin Zaid ya shiga ya fara gabatar da sallar da ta sameshi a hanya dan tun fitowarsa a Abuja bai tsaya ko ina ba.

Maryama na shiga ɗakin kaku saman gadonta ta faɗa ta buɗe sabon shafin kuka a haka Kaku ta shigo ta falon ta ga akwatinta taja zuwa ciki tana cewa.
"Waye anan, Maryama."

Ganin Maryama kwance ya sata ajiye akwatinta a gefe ta zauna kusa da ita Maryama ta juya mata baya tace.
"Ashe tare kuke, sannu kun sha hanya."

Ƙin mata magana Maryama tayi da ta gajima da surutunta tace.
"Dan Allah ki matsa a kaina ciwo yake min."

"Ni da ɗaki na za kice in fita to tashi ki tafi gurin Sadeeya."

Tashi Maryama tayi a fusace taja akwatinta ta bar mata ɗakin Kaku ta bita da harara.

Tana fita cikin sauri ta wuce part dinsu da sallama ta tura kofar falon ta shiga ta tsaya tsakiyar falon ta ƙara sallama.

Mami dake kitchen taji ta fito da mamaki take cewa.
"Walaikis salam kamar muryar Autana."

Karasa wajen Maminta tayi ta faɗa jikinta tace.
"Mamina."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now