39.

467 67 6
                                    

MARYAMA MARYAM 39.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

"Ina da magana da kai Dr Faruq amma ban san ya zaka ɗauka ba sai dai in har ka sawa zuciyarka yardan hakan."

Kallon Dr Umar kawai Ya Faruq yake yi dan jin maganganunsa har gama yace.
"Wani abun ya faru Dr?"

"Zan fi so mu zamto mu biyu dan fahimtar da kai da samun gamsuwa ga bayanina sannan in nuna maka wani abun da zai baka tabbacin haka bayan tambayoyi da zan maka."

Shi dai Ya Faruq duk ya kasa gane inda maganar Dr Umar ya nufa hakan yasa yace.
"To shikenan a ina zamu haɗu."

"Ga katina ka bani naka in har baka zo in zan zo in sameka."
Faɗin Dr Umar ya ciro katinshi ya miƙa ya Faruq ya karɓa yace.
"Nawa yana mota in an tashi sai muje in baka."

Daga nan aka ce gaba da hidinar da ya kaisu bayan godiya da aka musu na matsayinsu na likitoci aka basu kambun girma inda Ya Faruq ya fita da guda biyu na ƙaramin Dr mai tarin ilimi da basiri sai kuna mai ƙoƙarin kula da kowa ko ba ranar aikinshi bane.

Da ya tashi karɓa Maryam da taji daga waje ta shigo da sauri ta bishi aka dinga ɗaukarsu hoto sai sham ƙamshi take tana hura hanci da wasu ta burgesu wasu kuma ko kallo.

Daya karɓa yayi godiya ya nemi izinin tafiya dan ya bar patient aka bashi dama.

Har sun shiga motar bayan barinsu hall Dr Umar da ya biyo bayanshi ya ƙwanƙwasa gilashin motar ya sauƙe Ya Faruq yace.
"Sorry Dr na manta."

Murmushi yayi yace ba komai ya karɓa ya ɗaga Maryam hannu yace.
"Sai kuma haɗuwa ta biyu Madam."

Kai Maryam ta iya ɗaga mishi tace.
"Tace Babyna muje."

Sallama suka sake yi da Dr Umar bayan karɓar numbern junansu dasu kayi Ya Faruq yaja motar suna barin gurin sai da ya hau titi ya kalli Maryam yace.
"Kun san juna da Dr Umar ne?"

"A'a ko sau ɗaya."
Tace tayi gum da bakinta hakan yasa ya bar naganar yaci gaba da tuƙi.

Da suka isa ya ɗauki Maryama ya wuce ɗakinta da ita ya kwantarta saman kujera ta buɗe ido ta dubeshi ya zauna kusa da ita ya riƙo hannunta da ya sata kallonshi yayi murmushi yace.
"Are you feeling hungry?"

Kai ta ɗaga mishi tayi shuru yace.
"Mai za kici?"

"Kunu zansha?"

Shuru yayi rasa amsar da zai bata hakan yasa ta rufe idonta dan tazan ba samu za tayi ba.

Hannunshi ya zare cikin nata ya fita ɗakin Maryam ya shiga ya samu bata nan ya sauka ƙasa ya samu Maryam cikin kitchen ɗinta tana ganinshi ta haɗa rai tace.
"Kana buƙatar wani abu."

T

sare gira yayi yace.

"Kunu nake so na gyaɗa."

"Kana so ko tana so?"
Ta faɗa tana ɓata rai.

"Maryama ke so ta kasa cin komai, ki taimaka min dan ni ba dan ita ba."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now