30.

473 65 7
                                    

MARYAMA MARYAM 30.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Hannunshi ya saka ya riƙo hannayenta yana kallo tana kallonshi ta kasa kwacewa ya kai bakinshi ya sumbata ƙasa ƙasa yace.
"Yayi kyau sosai ina so."

Bata iya bashi amsa ba dan ganin Nafisa da Zaid ya sata yin shuru a haka suka ƙarasa gida hannunshi cikin nata yana murzawa kaɗan kaɗan wanda ya sata jin gashin jikinta ya tashi.

Zaid yana gama parking a harabar gidan Nafisa ta fita Maryama tana ƙoƙarin fita Ya Faruq ya hanata har suka gama fita Ya Faruq ya fita yana riƙe da ita ya rufe motar taga ya nufi part ɗin samarin da ita taja ta tsaya ya dubeta tace.
"Zan shiryane za muje wajen kamu."

"Nima can zanje muje ki jirani in shirya."
Yace yana riƙe da hannunta ta fara kwacewa ya saka hannuwansa ya ɗauketa gaba ɗaya tana wutil wutsil kwacewa yaƙi ya sauketa har cikin ɗakin Nurain da ya zama ba komai dan ya jide kayansa.

Ajiyeta saman gadon yayi zata gudu ya cafkota ya mayar ya zaunarta ta ɓata rai tace.
"Ni ka sake ni in fita za'a nemeni."

"Just two minutes Pretty Lady in shirya."

Ya Faruq yace yana kallon cikin idanuwanta da ya sata kawar da nata idon ta ɗaga mishi kai.

Tashi yayi ya rufe ƙofar da key ta bishi da kallo ya wuce bathroom ya watsa ruwa yana shirin fitowa ta kawar kanta gefe ta runtse idanunta taji sauƙar ruwa saman fuskarta.
Idanuwanta ta buɗe ta dubeshi daga shi sai towel tayi saurin rufewa tana turo baki taki mishi magana.

Lips natan ya shafa yana murmushi ya bar gurin ya hau shirinsa har ya gama ya dawo wajenta ƙamshin turarenshi shi ya bata tabbacin ya gama ya sata miƙewa tana kallon gefe tace.
"Muje ko."

Tayi gaba ya buɗe ƙofar suka fita ya riƙo hannunta da tana son kwacewa ya hanata haka suka shiga part ɗinsu ba mutane duk sun wuce wajen kamu.

A falon ƙasa ya zauna yace.
"Je ki shirya ina jiranki."

Da saurinta ta hau sama ta wuce ɗakin Maminta ta hau shiri wanka ta fara ta saka doguwar riga fitted da ya fito da dirin jikinta ta ɗaura dankwali da gyalenta ta yafa ta feshe jikinta da turare ba tayi wani kwalliya sosai ba ta fito ta sameshi yana waya.

Da kallo ya bita har ta iso wajenshi ya kashe wayar ya miƙe suka fita motar da Zaid ya bari suka shiga ya ja suna barin gurin har bakin harabar hall din ya buɗe ya zagaya tana ƙoƙarin fita ya taimaka mata ta fito yana riƙe da hannunta suka shiga cikin hall ɗin.

Hanata wucewa yayi gurin su Nafisa ya sata zama kusa dashi saman table bata so ba haka ta zauna ganin ya haɗa fuska.

Hidima ake sosai ana shagali kowa yana harkar gabanshi in ka cire Maryam data hango Ya Faruq da Maryama zaune ta tashi dan isa gurinshi.

Kamar ance Maryama ta ɗago ta hango tahowanta hakan yasa takai dubanta gurin Ya Faruq ta shagwaɓe murya tace.
"Yaya wallahi kafata zafi yake mini takalmin ya kamani."

"Mu gani."
Yace yana sunkuyawa ya cire takalmin kafartan ya bi kafar da kallo da yasha jan lalle, ɗago kafar yayi ya ɗaura saman cinyarshi ya fara matsa mata yace.
"Bari in matsa miki zai dai na."

Kai ta ɗaga mishi tana ƙirƙiro murmushi ta ɗaura saman fuskarta dai-dai isowar Maryam gurin taga abinda ke faruwa tasha mamaki duk irin kulawar da Ya Faruq yake mata bai kai ko haka ba.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now