16

377 58 4
                                    

MARYAMA MARYAM 16.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Tsaye Maryama take cikin kitchen dan dafa breakfast dankali take soyawa taji tsayuwar motoci bata bar abinda take yi ba har sai da taji hayaniyar mutane na shigowa falon.

Hayaniyar matane yafi yawa kashe gas ɗin tayi ta kwashe dankalin a plate ta ɗauka tare da ruwa ta fita waje anan taga matan har sun fara hawa sama da hanzarinta ta isa wajen ta tare hanyar wucewa da idanu suke binta.

Ɗaya daga cikinsu ce tace.
"Matsa mu wuce mana zaki zo ki tare mana hanya."

"Sai naji dalilin shigomin gidan miji har da karfin halin hawa sama."
Maryama tace tana binsu da kallo ƴan mata biyu a ciki sauran manya sai babbar mace ɗaya banda maza.

Ɗaya cikin ƴan matanne ta matsa kusa da ita tana bin Maryama da kallo tace.
"Ko dai kece ƙarfen ƙafa da aka ɗaura masa."

Sauƙar plate ɗin hannun Maryama taji saman goshinta ta dafe gurin tana saka ihu dan ba ƙaramin bugu ta mata ba, Maryama tace.
"Ko uban waye ya aiko ki ni da Ya Faruq mun fi kusa tunda jini ya tsaga."

Kan Maryama budurwar tayi zata rama ga kuma dukkan alamu sauranma zasu iya taruwa mata ya sata yin ɗakinta da sauri ta shiga ta saka lock.

Bugun kofan suke suna ta buɗe wallahi ko su balla su shigo.
Wayarta ta jawo dake jikin charge ta lalibi number Ya Faruq ta ƙira.

Tun da suka biya office ɗinsa suka karɓi mukullin get dana falo da kuma ɗakin da za'a saka kayan Maryam hankalinshi ya ƙasa kwanciya tsoronsa kar su haɗu da Maryama su mata magana ta musu rashin kunya.

Ƙarar wayarsa ne ya sashi ɗauka saman table ɗin gabanshi.
'Pretty Lady' ya gani a rubuce take mamallakiyar sunan ta fado mishi rai tun ranar da ya tabbatar Maryama ce ya kasa goge numbern kuma ya kasa canza mata suna.

Ɗauka yayi ya saka a kunne bai yi magana ba.

"Ya Faruq kana ina? Komai kake ka bari kazo wallahi ga wasu mata nan sunzo sai buga mini kofa suke, in har na buɗe na samesu mai rabani dasu sai Allah garin Abuja ya mana kaɗan."

"To ki buɗe ki samesu mana."
Ya faɗa mata bayan gama sauraronta.

Cikin jin haushi tace.
"Haka kace to shikenan."

Kashe wayar tayi ya zare a kunnenshi abin ma dariya ya bashi yayi murmushi yana tashi ya kwashi mukullin motarsa ya fita.

Bugun kofar suke ta tashi tazo bakin ƙofar ta tsaya.
"In kun gama ihunku ku matsa mini a baƙin ƙofa ina da abin yi."

"In ba tsoro ba ki buɗe mana."
Taji muryar mata ɗaya da tafi kowa zaƙalewa.

"Bazan buɗe ba dangin jarababbu."

"Ki buɗe in ga ƙarshen rashin kunyarki."
Matar ta faɗa.

Ƙin kulasu tayi ta koma ta zauna tana ji har suka hakura suka bar gurin.

Bai ɗauki lokaci ba ya iso gidan ya shigo suna ganinshi suka tashi ya bisu da kallo.

Aunty Sameera ce ta tashi ta nufeshi tace.
"Kaga abinda wannan yarinyar ta ma Salma wallahi kuma sai ta rama akan mai zata kumbura mata goshi."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now