40.

507 72 8
                                    

MARYAMA MARYAM 40.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Bayan Abbi gama sauraron bayanin Momy ya sauƙe numfashi yace.
"Yanzu shi Umar ɗin ne ya saki Maryam? Ikon Allah lallai Umar yayi ganganci ko ma mai ta mishi bai kamata ya yanke wannan hukunci ba, bari zan ƙirashi yazo muyi magana kuyi hakuri Saleema."

Godiya ta mishi ta mike ta fita.
Bayan fitarta ya ɗauki wayarsa yayi ƙiran Ya Faruq.

Lokacin da ƙiran ya sameshi yana zaune sai roƙar Maryama yake ta saka wani abu a cikinta ko ta faɗa masa mai za taci, tace ita ba zata iya cin komai ba abinda take so babu shi anan ya barta ta girka yaƙi wai bata jin daɗi.

Kallon wayar yayi ya ɗauka ganin Abbi ne ya amsa tare da sallama yana kallon Maryama data tsareshi da ido ƙasa ƙasa yace mata.
"Abbi ne."

"Zamu gaisa in kun gama."
Tace ya ɗaga mata kai suka gaisa da Abbi, Abbi yace.
"Umar ina nemanka kazo gida cikin kwana biyun nan in har baka da aiki a asibiti?"

"Lafiya Abbi?"
Ya Faruq ya tambaya.

"Ina lafiya Umar akan maganar Maryam ne ko ma mai ta maka bai kamata ka yanke wannan hukunci ba cikin sauri, maganar waya ba zai yu ba kawai sai kazo."

"To shikenan Abbi inshaAllah zanyi ƙoƙarin zuwa nan da jibi Friday."

"To Allah kaimu sai kazo."

"Abbi ga Maryama zaku gaisa."

"To bata tana lafiya?"

Amsar wayar Maryama tayi ta gaisa da Abbi ta miƙa masa wayarshi ya amsa ya kashe yaga ta zuba masa ido, ya hura mata iska a idanuwanta yace.
"Wannan kallon fa?"

"Mai yasa kayi haka Ya Faruq baka tsoron duniya ta zageni ace daga dawowata ka rabu da matarka."

Rumgumeta yayi yana ɓata rai yace.
"Ki daina ƙiramin sunan wata mace bayan ke, ke kaɗai ce matata bani da wata matar kuma, ba wanda ya isa ya zageki in har duniyar taji mai ta aikata ita za'a zaga bake ba."

Zata sake magana ya rufe mata baki da nashi, daren ranar lallaɓa ta yayi yabi da ita a nutse ta bashi haɗin kai saboda cikin jikinta.

Washegari haka ya sata ta shirya suka tafi office ɗinsa duk da tace ta fara jin ƙarfin jikinta yace ba zai barta ita ɗaya ba a gida.

Da yamma da ya bar office ɗin ya nema musu tickets kafin su wuce gida ya haɗa musu kayansu da taimakon Maryama da ya hanata motsi amma kuma tace sai ta taimaka masa.

Sai da suka gama shirya kayansu kala bibbiyu dan ran Sunday yake so su dawo saboda aikinsa kuma basu jima da dawowa daga gidan ba, banda case ko ƙiran da Abbi ya mishi ma ba abinda zai kaishi Maiduguri kwana kusa, ga kuma Maryama ba zai ita barinta ita ɗaya a gida ba.
Kwanciya su kayi bayan sun gama komai.

Washegari Jumma'ah fir Maryama taƙi binshi office tace yaje ya dawo bai so ba ya fita ya barta.

Yana tafiya ta lallaɓa ta wuce kitchen ɗinta abinci ta ɗaura white rice and beans da taji sha'awar ci ta gama ta soya manja ta kwashe sauran a Warmers ta zuba wanda za taci a plate ta fito falon, a nutse taci abinta taji daɗin shi kafin ta wuce sama tayi wanka tana cikin shiri taji shigowar motarsa.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now