37.

457 66 44
                                    

MARYAMA MARYAM 37.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

"Abinda yake jikin ƴata nazo ka karya sannan ka nema mana wani hanyar duk abubuwan da mu kayi ya ɓaci yaƙi aiki."

Dariya yayi da taga haƙoransa duk goro yace.
"Abin jikin ƴarki ba ranar karyewanshi in kuma kina son ta rasa hankalinta sai in baki wani aikin."

A harzuƙe Momy tace.
"Bana son wani aikin akan mai? Mai ƴata ta maka zaka mata haka, taimako fa muka zo nema ba mugunta ba."

Wani dariyar yayi na mugunta yace.
"In ke baki lura ba ni na gani ranar da kuka zo ƴarki ta nuna bazan iya mata komai shi yasa na mata wannan abun dan haka kinga ba'a rainamu sai kuje kuci gaba da zama haka."

"Ban yafe ba Allah ya isa tsakanina da kai wannan ai muguntace aniyarka ta bika ta Allah ba taka ba."

A tsawace yace.
"Fita ki barmin guri ko kema yanzu in tarwatsa abin da na miki ki ka auri naki mijin kika kwacewa kawarki manemi."

A fusace Momy tace.
"In ka fasa Allah ya fiki."

Daga haka Momy ta fita a fusace ta bar gidan tana jan motarta sai zage zage take amma ƙasan ranta tsorone kar kuma fa ya mata wani abun ita da ƴarta.

A haka ta isa gida bayan ta nutsu ta ƙira Maryam bata jira tambayarta komai ba tace.
"Dalla rufemin baki, bari kiji in faɗa miki Maryam komai ya lalace wannan malamin ya cuceni ya cuceki ashe mugunta ya haɗa miki da gangan ya miki haka abinda za kiyi kawai ki riƙe aurenki da kyau kiyi ƙoƙarin rike mijinki da kwalliya da gayunki dan nima yanzu aurena zan gyara kina jina."

Tashin hankalin da Maryam ta shiga baya misaltawa wani ashar ta buga kafin tace.
"Allah ya isa tsakani na dashi ya cuceni kuma duk ke kika jawo min Momy ina cikin zamana mijina yana sona kika nunamin wannan hanyar."

"Ubanki Maryam ni na jawo miki ni mahaifiyarki ba zaman lafiya nake nema miki ba banza wawiya."

Daga haka Momy ta kashe wayarta Maryam ta zube saman gadonta ranta kamar ya fita tsabar baƙin ciki duk laifin ta ɗaurawa Momynta.

Har dare tana kulle ɗakinta ta kasa fita data gaji da zaman ɗaki ta fita falonta abin duniya duk ya bi ya isheta ƙoƙar kawai za tayi ta dawo da soyayyarta zuciyar mijinta shine kawai abinda za tayi.

Buɗe kofarta da aka yi ya sata kai dubanta bakin ƙofa Ya Faruq ne ya shigo yana ɗauke da ledoji ya ajiye mata yace.
"Ga dinner."

Yana shirin fita ta tashi ta zauna tace.
"Babyna."

Daga inda yake ya tsaya ya kalleta yace.
"Kina buƙatar wani abu?"

Tashi tayi ta isa gurinshi cikin kwantar da murya tace.
"Har yanzu fushi kake dani?"

Kallonta kawai yake bai bata amsa ba taci gaba da cewa.
"I'm sorry"

"It's ok ya wuce but next time ki kiyaye."

Kai ta ɗaga mishi tana murmushi ta kamo hannunshi tace.
"Muje muyi dinner tare nayi missing ɗinka sosai."

Martanin murmushin ya mata suka koma saman kujera ta buɗe abincin yace.
"Kici naki ne."

"Ni dai a'a yamin yawa muci kawai tare in kuma ba haka ba na bari "

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now