42.

453 72 9
                                    

MARYAMA MARYAM 42.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

"Dr Faruq magana nazo maka dashi amma ban san yaya zaka ɗauka ba, kar ka zargi wani abun."
Dr Umar ya faɗa bayan samun Ya Faruq da yayi har gida Washegarin ranar da su kayi magana da matarshi.

"Ina jinka Dr."
Yace yana sauraran shi.

"Ina son auren your ex wife Maryam, ina buƙatar taimakon ka, ni ne nan na taimaka mata rayuwarta ta ɓaci badan da saka hannuna ciki ba da yanzu nasan tana gidanta ina tsoron Allah ya kamani da laifi."

"A'a Dr Umar son raine ya saka Maryam aikata haka ko kai ka ƙi amincewa to wani fa zai mata hakan ka godewa Allah daya saka ka fahimci laifinka, ka nemi tuba gurin Allah amma bazan hanaka aurenta ba sai dai mai iya zaman kishi da Maryam sai ya shirya mace ma da take da baki bata ɗaukar raini sun yi rigima da Maryam balle mace shuru shuru kam sai yanda Allah yayi in har kana da mace kuna zaman lafiya da matarka kar ka jawo muku fitina in kuma baka da aure to, amma shawara na baka in har hakan ya maka."

Ajiyar zuciya Dr Umar ya sauƙe bayan sauraron bayanin Ya Faruq yace.
"Shikenan Dr Faruq nagode Allah ya yafe mana ni da ita gaba ɗaya."

"Ameen."
Ya Faruq yace suka canza salon hiran har zuwa la'asar kafin su tafi masallaci daga nan Dr Umar ya wuce gidan shi.

Da ya isa gidan matarshi Khairiyya ta tareshi kamar kullum ta kawo mishi ruwa da kayan abinci tana ƙoƙarin tashi ya jata jikinshi.

"Irin kune matan aljannah fatan kece matata har cikin Aljannahtul Firdausi."

"Ameen Nagode mijina."
Tace tana murmushi.

"Na janye maganar auren da nace zanyi bazan iya haɗa ki da ko wacce mace a duniyar nan ba ke ɗin ta dabance a rayuwata ko Allah bai bamu haihuwa ba zanci gaba da zama dake a haka har ƙarshen rayuwarmu."

"Balle ma Allah ya dubemu ya bamu."
Tace tana rumgumarsa iya ƙarfinta sai kuma ta saka mishi kuka.

Ɗagota yayi da mamaki yace.
"Dagaske kike Khairiyya kin san bana son irin wannan wasan."

Hawaye a fuskarta ta ɗaga mishi kai ya rumgumeta shima nashi idon cike da hawaye.

Tsawon shekara biyar da aurensu sai yanzu Allah ya basu lokacin da suka cire tsammanin da samun rabo.

Ribar hakuri kenan tayi hakurin rashin haihuwa sai gashi Allah ya bata haihuwar ga kuma hakurin aure da mijinta yace zai ƙara gashi ya janye shi da kanshi.

...

Ya Faruq yana zuwa gidan ya samu Maryama zaune cikin falonta daga ita sai towel duk ta wani kumbure fuska ya ƙarasa wajenta yana zama yace.
"Ya ya akayi maman Baby."

"Ba duk kayana bane suka min kaɗan."
Tace tana turo baki.

"Oh to ya za muyi?"
Yace yana kwaikwayon muryarta.

"Ni ban sani ba ai."

"Tashi muje mu duba wani sai mu nemo wasu a shago."

Lallaɓa ta Ya Faruq yayi dan kwanan nan ya kula wani rigimar take ji dashi abu kaɗan fushi.

Riga suka samu wanda ya shigeta ta saka hijab suka fita yana mata sannu data gaji tace.
"Wai nikam kaga ciwo jikina ne kana mini sannu."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now