13

372 56 4
                                    

MARYAMA MARYAM 13.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Sauƙa tayi tabi bayansa ganin yayi gaba entrance na hotel ɗin ya shiga ta bishi taga ya tsaya reception itama ta tsaye gefe kaɗan bayan yayi abinda zai yi aka bashi mukullin ɗakin daya nema yayi gaba tabi bayansa.

A baƙin ƙofar ɗakin ta tsaya ya buɗe ya shiga ta bishi ciki yana tsaye, Maryama zama tayi dan ta gaji tana warware mayafin kanta.

"Ki zauna anan zanje in dawo ga abincin dana siya miki ba kici ba nasan ya isheki har dare."
Ya Faruq dake tsaye ya faɗi haka yana fita yaja kofar ya kulle ta baya yana jefa mukullin aljihunsa.

Da kallo ta bisa har ya fice baƙin ciki tare da haushi ya ziyarci zuciyarta na ganin ya kawota ya ajiyeta bai kaita gida ba to ai gwara ya barta a Abuja da wannan kayan taƙaicin.

Bata bi ko takan ledan daya ajiye ba ta tashi ta shiga bathroom wanka tayi ta ɗaura alwala ta fito ta ɗauki doguwar riga marar nauyi cikin kayanta ta saka ta gabatar da sallar magriba da isha'a ta koma ta kwanta saman gado.

Ya Faruq na fita Masallacin dake hotel ɗin ya nufa ya gabatar da sallah ya ɗauki motarsa ya tafi gida.

Bayan ta isa ya shiga da motarshi ya nufi part ɗinsu Maryam wayarta ya ƙira ta ɗauka.
"My Dear na iso ina compound."

To tace ta kashe wayar ta fito ya bita da kallo ji yake kamar ya ɗauketa.

Da tafiyarta dake ɗaukar hankalinshi ta ƙarasa wajensa tace.
"Welcome My Baby kasha hanya kuma shine ka tsaya a waje kamar bako."

"Kunyar Momy nake ji."
Ya Faruq yace yana murmushi.

Itama martanin murmushi ta mayar masa tayi gaba yabi bayanta har falon suka zauna ta kawo masa abinci da abubuwan sha.
"Bismillah Babyna nasan kasha hanya."

Abinci kaɗan yaci yasha fruit salad data haɗa da ɗan yawa ta kwashe duka komai takai kitchen ta ƙira Aunty Saleema tazo suka gaisa tana masa ya hanya kafin yace zai leƙa part ɗinsu.

Suna tsaye hanyar da zai kaishi part ɗinsu tace nan zata juya yace.
"Zuwa safe zan samu Abba da maganarmu ki mana addu'a Allah ya sa su yarda ayi bikinmu kwana kusa I can't wait to see you as my wife."

Murmushi tayi kanta ƙasa tace.
"Sai da safe inshaAllah zan mana."
Daga haka ta juya ya tafi har zai wuce part ɗin Kaku wani abu ya sashi shiga.

Bata falon daga ciki taji motsin mutum.

"Waye haka da daren nan kamar ɓarawo zai shigo mini da sallama ciki ciki baya buɗe murya."
Ta fada haka Ya Faruq na zaune saman kujeranta da yayi sallama ya shiga dan jiran fitowarta bai amsa mata ba har ta gama abinda za tayi ta fito ta ganshi zaune.

"Kai wani irin bawa ne Umaru sai kasa ya'yan hanjina fita ta baki ai tsabar tsoro yaushe ka taho ina Maryama tare kuka zo."

Ganin surutunta bana karewa bane ya sashi tashi ya nufi hanyar fita.
"Dama nazo gaisheki ne tunda ba zaki tsaya mu gaisa ba sai da safe."

Daga haka ya fita ta bishi tana cewa.
"Kai ka sani ubanka ma Haruna duk safiya da yammaci sai yazo gaisheni balle kai karan kaɗa miya na ƴayana ma ya isheni "

MARYAMA MARYAMKde žijí příběhy. Začni objevovat