24.

400 64 2
                                    

MARYAMA MARYAM 24.

Pharty Bb
Wattpad phartybb.

Cikin gidan suka shiga tare da sallama cikin babban hijab da suke ciki aka musu jagora har ɗakin wanda suka zo nema, bayan sun shiga sun samu guri suka gaisa Momy tace.

"Gata nan Malam itace ƴar tawa da nake faɗa maka."

Duban Maryam yake da tun shigowarsu sai kumbure fuska take yace.
"Mai take so a mata."

"A ɗauke hankalin mijinta daga kan kishiyarta."

Shuru yayi can ya dubesu yace.
"Zan bata zaɓi, na farko za tayi amfani dashi idan amma ba zata ma kishiyar wani abu ba na dangane ga sihiri har tayi gigin ma kishiyar ta abu to zata rasa hankalinta, na biyu kuma ita za tayi amfani dashi dan mallakar mijinta amma in har kishiyarta tayi ƙoƙarin mata sihiri ita ɗin wannan ƴarta kin zata rasa hankalinta."

Maryam Momynta ta kalla ta girgiza kai alamar ba zata yi ko ɗaya ba Momy tayi saurin cewa.
"Mun zaɓi na farko Allah yayi amfani."

Miƙa musu wani kulli yayi yace.
"Ta sha da madara ko nono fari."

Karɓa Momy tayi ta buɗe jakar Maryam ta saka ta ciro kuɗi masu yawa ta ajiye mishi bayan godiya da suka masa suka baro gidan Maryam ta cika tayi fam.

Karfe ukun yamma suka dawo gida bayan sun huta gajiya Momy ta samu Maryam har ɗakinta da cup da madara a ciki ta zuba garin maganin ta miƙa mata.

"Bazan sha ba Momy kinji fa mai yace idan nayi gigin mata abu fa zan rasa hankalina, yanzu in naje wannan bai yi aiki ba fa shikenan nan fa bazan mata wani abun ba sai dai in zuba mata ido kinsan kuma ba zan iya ba."

Tsareta Momy tayi da idanuwanta tace.
"Yanzu asara zaki sani ko me kike nufi, karɓi kisha dalla ana nema miki samun zaman lafiya kin tsaya min wani zance banza."

"Nifa bazan sha ba Momy."
Maryam tace tana ƙoƙarin tashi Momy ta jawota ta kwaɗa mata mari ta miƙa mata cup ɗin.
"Karɓi ki shanye ba zaki sakani asara ba, kina ganin nima taya na zauna gidan nan da irin abubuwan nan ne sanin kanki na auri uban Faruq ɗin."

Haka duk fushin Maryam akan marin da tasha Momy ta sata ta shanye abun cikin cup ɗin tas ta bata cup ɗin ta fita.

...

Satin su Maryama ɗaya, Ya Faruq yace su shirya zasu koma saboda aikinsa da farko Maryama ƙin tafiya tayi tace bata gama hutunta.
Ga auren Ya Nurain da aka saka za'a yi cikin wata biyu masu zuwa.

Mami ta haɗa mata kayanta sai kuka take ta sata gaba.

"Wai Maryama lafiyarki kukan me kuma? da ba kiyi kukan ba sai yanzu."

Hawayenta ta share tace.
"Ni dai Mami kawai bana son barinki ke ɗaya."

Murmushi Mami tayi ta tashi ta zauna kusa da ita tace.
"Haba Mamana wani abun suka miki ki faɗa min, shi Umar ɗin ko Maryam sun miki wani abu."

Shuru Maryama tayi tana ƙasa da kanta fahimtar hakan yasa Mami cewa.
"Kiyi hakuri kinji yanzu ki tafi gidanki Allah yana tare dake kiyi ta addu'o'i Allah zai yaye miki komai in har Umar ya miki wani abun da har naji bai kyauta ba zan mishi magana."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now