27.

430 67 6
                                    

MARYAMA MARYAM 27.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Lokacin da Ya Faruq ya shigo gidan Maryama na kitchen tana dafa indomie da taji sha'awar ci tun safiya bata samu ba.
Kitchen ɗin ya leƙa ta ɗago idanuwanta ta kalleshi tana ɗaukewa ya ƙarasa ciki ya tsaya gefenta.
"A dafa dani."

Ƙasa ƙasa tace to kafin ya fita ya wuce ɗakin shi ya watsa ruwa ya sauƙo ya sameta a saman table, gurin ya ƙarasa yaja kujera ya zauna ya buɗe plate ɗin da ta rufe ya fara ci ba wanda yama kowa magana shi kam da idanu yake binta.

Ta rigashi gamawa ta kai Plate ɗin kitchen ta wuce ɗakinta sallar isha'a ta gabatar tayi shirin bacci ta kashe komai na wuta ta kwanta abinta.

Har karfe goma Ya Faruq yana falon tun tafiyar Maryama waya suke da Maryam tana cewa wallahi kar ya kula Maryama murmushi yayi kawai yace mata to duk yadda tace haka za'a yi.

Sha ɗaya saura ya tashi ya kashe Tv da wutan falon ya hau sama ɗakin Maryama ya nufa ya buɗe duhu ya gani sai hasken farin wata da ya haska har ɗakin ya shiga ya hangota tana bacci ya ƙarasa bakin gadon ya zauna yana gyara zamansa addu'a yayi ya shafa ya gyara kwanciyar shi bacci ya ɗaukesu.

Da asuba ya farka ya tasheta tayi mamakin ganinshi ɗakin ta shige bathroom kafin ya tafi sallah.

Tana idar ta sallar ta haye gado ko azkhar ba tayi ba dan gudun kar ya dawo ya hau ta kasa kwanciya.

Bacci ya fara fizgarta ta ji hannu saman fuskarta ta buɗe idanunta fes cikin nashi ta ɓata rai tana matsawa baya ya riƙota.

"Ina za kije?"

"Bacci fa zanyi."
Tace tana ƙoƙarin kwace jikinta ya saketa ta matsa gefe yace.
"Yi baccinki to, amma ki farka da wuri ki haɗa mana breakfast zan wuce aiki kin sani."

Juya masa baya tayi taja blanket ta rufu ya tsura bayanta ido yana tunani da wahalar aikin da zai sha akan Maryama dan shi shaidane sanin yadda su kayi zama tun mafarin rayuwarsu har yanzu.

Karfe takwas ya shirya ya fice aiki bai tasheta ta.
Maryama bata farka ba sai kusan goma saura wanka tai ta sauƙa kitchen bata ganshi ba a falon anan ta tabbatar ya bar gidan bai tasheta ba.
Abin da za taci ta haɗa ta zauna nan falon sai taji gidan ya mata daɗi da Maryam bata nan.

Tana tsaye cikin kitchen baya gama ayyukan ta tana ɗauraye kwanukan da tayi amfani dashi ta dafa tuwor semonvita da miyar allaiyahu data aika da kifi taji alamar buɗe kofar falon barim abinda take ta leƙa taga matasan budurwaye tsaye su biyu cikin falon suna ƙare masa kallo.

Suna ganinta suka kalli juna sai suka ƙarasa wajenta tana binsu da idanu tace.
"Lafiya wa kuke nema zaku shigowa mutum gida ba sallama ko babu ilimin addini."

Ɗayar da tafi kauri tace.
"Wa zamu ma sallamar? Ke? Gurin Maryam muka zo ko bata nan ne."

"Ta tafi gidan uwarku koyo sallama marasa tarbiyya."

Kallon kallo su kama juna kafin su kara wani magana suka ji sauƙar ruwan omo a jikinsu wanda basu san lokacin da Maryama ta koma cikin kitchen ɗin ta debo ruwan wanke wakenta daga sink ta juye musu a jiki.

Ihu siririyar cikin ta saka dan ya shiga idonta tayi kan Maryama, Maryama taja baya tsantsi ya kwasheta ta zube nan tana ƙara sakin wani ihun da yasa mai kaurin yin kan Maryama a hankali kar tsantsi ya kwasheta.

MARYAMA MARYAMМесто, где живут истории. Откройте их для себя