2.

573 74 0
                                    

MARYAMA MARYAM 2.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

MUSAYAR FAHIMTA.

"She's beautiful and classy."
Faruq yace idonsa akanta data koma wajen zamanta ana mata tafi fuskar nan sai zuba murmushi yake.

Idon Ya Nurain akan Maryama yace.
"Yes she's beautiful and naughty."

"Her digits."
Nurain yaji sauƙar wayar Faruq saman tafin hannunsa.
Da mamaki yake kallon ɗan uwansa yana saka masa number nata ya miƙa masa.

Bayan ya amsa wayar yayi saving contact ɗinta yana tashi a gurin bai ko kalli inda Nurain yake da sauran ba ya fita waje yana dialing contact ɗin.

Tana zaune baƙin ciki duk ya cika zuciyarta ba dan ba'a tashi ba da ta bar gurin kuma in tayi duba da yadda take da Nafisa sai ta ƙara ba zuciyarta haƙuri.
Ruri da ƙara da wayarta ya ɗauka a cikin jakarta shi ya sata buɗewa ta ciro tana bin numbern da kallo.
Yana shirin yankewa ta ɗauka tana kafawa a kunne tare da tashi tana fita dan samun sararin jin maganar mai ƙiran da kyau.

"I'm talking to Maryam?"
Taji mai ƙiran ya tambaya.

Kamar ta kashe dan jin wani rainin hankali da aka mata tace.
"Yes! Who's this please."

Jingina kansa yayi jikin kujeran motar daya zauna bayan fitowarsa yace.
"I will introduce myself soon."

Kafin ta masa tambayar da yazo mata kit aka kashe wayar, da kallo take bin screen ɗin wayartan kafin ta buga tsaki iya ƙarfinta ta goge contact ɗin a received call.

Ciki ta koma anan ta tarar amarya da ƙawayenta a filin rawa kamar ba zata je ba har ta juya taji mc na ƙiranta da ta ƙaraso wajen a matsayinta na babbar ƙawar amarya.
Juyawa tayi ta kalli inda Nafisa take tayi fuskar tausayi da alamar roƙo.

Ƙarasawa wajen tayi da duk idanun jama'a ya koma gurinta, tafiyarta dake rinjayar hankalin mutane shita ƙarawa salo inda mazan gurin gaba ɗaya ta tafi da imaninsu.

Data isa wajen canjin ɗari ɗari da Mami ta bata ta fara zuba amarya dake rawa ganin aminiyarta ta ƙaraso inda bayan Maryama ta gama ƙarin ta fara nata rawar cikin nutsuwa.

Ranta in yayi dubu ya ɓaci ta tsaneta tun ranar data fara tsaka idanunta cikin nata, kyau ne ba zata nuna mata ba sai dai ma ita ta nuna mata aji da wayewa, amma tsanarta kullum yawaita yake a zuciyarta.

Tashi itama tayi daga inda take ta fita a hall ɗin, motar Aunty Saleema ta shiga dan jiran fitowarta.

A haka aka gama dinner aka fara watsewa, Maryama motar amarya ta bi suka koma gida, ko part ɗinsu ba tayi ba ta sauƙa a part ɗinsu Nafisah, wanka kawai ta iya yi kasancewar tana hutu tabi lafiyar gado.

Karfe shida ta farka da hayaniyar jama'a ya farkarta kayanta ta ɗauka suka koma part ɗinsu ita da Nafisa da sauran cousins da suka zo.

Ta fito wanka misalin karfe sha ɗaya dan zirga-zirgan da suje bai bari tayi da wuri ba, tana shafa mai Surayya ta miƙa mata wayarta.

Amsa tayi tana kafawa a kunne ganin Surayya ta ɗauka tace.
"Hello!"

"Hey Pretty Lady good morning."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now