11.

370 51 0
                                    

MARYAMA MARYAM 11.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Washegari da safe aka gama shiri tsaf za'a kai amarya Maryama gidanta idon nan kur ba alaman kuka ko ka kalli fuskarta kaga damuwa ko ɗaya babu sai ma taimakawa Nafisa take gurin shirya kayanta da bata gama haɗawa ba.

Bayan sun gama sun fita Aunty Hawwah da Aunty Saudah sune suka sakata tsakiyarsu a motar Abba da ya bayar a kaisu airport dashi Nafisa a gaba Ya Nurain ne yake ja.

Sai fa da taga dagaske Maminta zata bari ta fara rayuwa da maƙiyinta da kuma mutum da tafi tsana a rayuwarta ta ji jikinta yayi sanyi tana son yin hawaye.
Har bakin mota Ammi da Mami da kuma aunty Saleema suka rakosu bayan sun bar harabar gidan suka koma.

Ya Faruq shine motarsa gaba yana tare da Zaid da kuma twins, Ya Nurain yana binsa a baya har suka isa airport suka sassauƙa sai kawai ta nufi Ya Nurain ta fashe mishi da kuka.
"Ni wallahi ka maidani gurin Mamina."

"Haba Maryama ai kuka ya ƙare hakuri za kiyi."

"Zaka bimu ai amma." Tace tana share hawayenta.

Kai ya ɗaga mata yace.
"Ki bi Aunty Hawwah ina zuwa."

Aunty Hawwah da ta zagoya gurinsa taja hannunta suka tafi ciki tana yi tana waiwayon Ya Nurain har suka shige ciki ya matsa kusa da Ya Faruq da yake shirin shiga ciki yace.

"Ya Faruq ga nan ƙanwata Maryama na baka amanarta nine silar haɗa komai in ka cutarta bazan yafewa kaina ba saboda ni na jawo mata komai Allah baku zaman lafiya."
Daga haka ya koma motar yana barin gurin ya bar Ya Faruq da yake jin maganganunsa na ratsashi tun jiya da Abba ya masa ire irensa yaji jikinsa yayi sanyi amma har lokacin yana jin zafin haɗin da aka musu.

Yana tuki amma hankalinsa yana gurin Maryama gani yake tamkar ya rushe mata farin ciki yarinya ƙarama da ita da auren da mutumin da baka so baya sonka kuma tun kafin ka shiga gidan kasan za'a maka kishiya.
Da haka ya isa gida da wannan tunanin amma ya ɗaukarwa kanshi alƙawari ɗaya dashi kaɗai ya bari a ransa.

Ganin har jirgin yana ƙoƙarin tashi bata ga alamar zuwan Ya Nurain ba ta dabi Aunty Saudah.
"Aunty Saudah Ya Nurain fa bai shigo ba."

"Ce miki yayi tare za muje."

"Eh yace yana zuwa."

"May be ya biyo mu daga baya amma ba yau ba."

Kuka tasa tace wallahi ita ba zata tafi ba in ba dashi ba haka Aunty Saudah tayi ta lallashinta har jirginsu ya ɗaga, mintunansu talatin suka isa abokinsa Ya Faruq ya ƙira yace yazo airport yana tare da baƙi ba mota a hannunsa.

Bai daɗe ba yazo suka shiga suna tafiya gidansa, da suka isa sauƙa ya Faruq yayi ya buɗe get din ya shiga da motar kafin su Aunty Hawwah su sauƙa da Maryama ya buɗe kofar falon suka shiga shi kuma ya koma wajen abokinsa suka fita tare.

Suna shiga cikin falon basu tsaya ko ina ba sai sama inda ɗakin Maryama yake yanda yake haka suka dawo suka samu suka sake sharewa suka goge ƙura har kitchen suka gyara komai yayi tsaf.

Da azahar Ya Faruq ya dawo tare da takeaway daya musu a kofar falon ya tsaya bayan yayi sallama Aunty Saudah ta leƙa ta karɓa ya koma.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now