38.

484 76 19
                                    

MARYAMA MARYAM 38.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Karfe biyar ya shiga gidan dan tattaunawa da suka tsaya yi a office din bai barshi ya dawo gida da wuri ba.

Yana shiga Maryama ta fito kitchen ɗinta kenan da sauri dan miyartan ya ƙone ya sata jin zuciyarta tashi data sauƙe ta kasa zama ciki balle maganar zubawa taci.

Maryam data ganshi ta sauƙo kasa tayi saurin nufan wajenshi gudun kar ya tafi gurin Maryama ta rumgumeshi jikinta.

"Welcome back."

Bai iya bata amsa ba ya rabata da jikinshi ya nufa wajen Maryama da take riƙe bakinta yace.
"Lafiya aman ne?"

Bata iya bashi amsa ba ta fara zuba mishi a jikinsa yana rike da ita sai sannu yake mata har ta ƙarasa gamawa ya ɗauketa suka wuce ɗakinta suka bar Maryam tsaye ta shiga ruɗani da bata taɓa shiga ba.

Kar dai cikine da yarinyar nan? Ta yaya? Yaushe? Tana ina hakan ya faru?

Ai ƙwaƙwalwarta bai gama tantance mata ba ta bi bayansu da sauri.

Ya Faruq yana shiga da Maryama bathroom nata ya wuce da ita ya gyara mata jiki dan gaba ɗaya tayi laushi ya fito da ita ya kwantar saman gado ya rufeta dan zafin zazzaɓi daya kamata kafin ya nufa ƙofar fita suka haɗu da Maryam.

Da mugun kallo take binshi dashi tace.
"Kar kace min cikine da ita Faruq."

Ta faɗa hakan tana jiran amsar da ta gwammace bata tambayeshi dan ɗaga mata kai yayi yana murmushi ta kurma ihu taci kwalan rigarshi.

"Ka gama dani ka cuceni ka cuci rayuwata, son kenan Faruq da kake cewa kana min ashe zaka iya zuwa wajen fitsararriyar yarinyar nan ku haɗa shimfiɗa har ta samu ciki.."

Ya Faruq bayan ya samu ya cire hannun Maryam wuyanshi ya watsa mata mari biyu lafiyayye.

"Rashin hankali har ya kai ki damƙi wuyar rigana baki da tarbiyya dama, da kike ƙiranta fitsararriya gashi yanzu kin fita fitsara da kika iya ɗaukar hannu kika damkƙi wuyar rigana wanda gaba bansan mai za kiyi ba, ciki kuma naga matatace tamkar ke wanda yanzu har ta fiki samun matsayi cikin zuciyata."

Daga haka Ya Faruq yaja hannunta tana turjewa sai zagi take wallahi sai cikin nan ya zube ko itama ta samu.

Waje ya jefarta ya kulle kofar falon Maryama ya jefa mukullin aljihunsa ya sauƙa kasa ya gyara inda Maryama ta ɓata ya wuce ɗakinsa dan gyara jikinsa.

Kuka kawai Maryam take tana ƙiran numbern Momy ta ɗauka jin Maryam na kuka yasa Momy cewa.
"Ki rufe min baki ki faɗa min mai kuma aka miki ko in kashe wayata."

"Momy cikine da ita zata haihu da Faruq ban haihu dashi ba Momy nayi dana sanin zubar da cikin da nayi gashi yanzu tun bayan miscarriage nawa ban samu wani ba."

"Waye mai cikin ke wawiya?"
Momy tace da tashin hankali.

"Wannan yarinyar Momy, Faruq ya cuceni ya cuci rayuwata Momy zan iya kasheta wallahi na tsaneta."

"Ki kasheta ko ki bi ko wani hanya ki zubar da cikin."
Abinda Momy ta faɗa ta kashe wayarta Maryam ta ƙara fashewa da kuka taji wayarta ya ɗauki ƙara taga Momy ce ta ɗauka da sauri.

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now