36.

520 72 13
                                    

MARYAMA MARYAM 36.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

Maryama tana jin Ya Faruq ta nuna tamkar bata ji mai yake faɗa ba taci gaba da abinda take yi amma zuciyarta bugawa yake tamkar yanzu ne komai zai faru sabo a gurinsu.

Har ta gama shafe shafenta ta haye saman gado yana kallonta murmushi yayi ya tashi ya zauna kusa da ita tana jinshi ta runtse idanunta ya kamo yatsun hannuwanta yace.
"Tashi mana Pretty Lady wani irin kwanciya za kiyi bayan ga kazar amarci yana jiranki."

"Ni na ƙoshi."
Tace a hankali.

"Oya get up."
Yace yana ɓata rai da muryarshi ya fallasa hakan yasa Maryama buɗe idanunta ta dubeshi dasu ya haɗa rai.

Tashi tayi yana rike da hannunta ya zaunarta ƙasa ya fita bai jima ba ya dawo da plate da cup tana ganinshi ya juye kazar ciki ya zuba fresh milk a cup ya tura mata gabanta ya matsa yace.
"Bismillah Amaryata."

A hankali ta saka hannu ta fara ci shima ya fara kaɗan taci tace ta ƙoshi ya bata fresh milk ɗin, shi tasha sosai dan sanyinshi ta ajiye ta shiga bathroom tai brushing na bakinta ta fito ta kwanta saman gado ta rufe har saman kanta.

Bayan Ya Faruq ya gama ya tattare komai ya kai kitchen ya dawo yai brushing na bakinshi ya kashe komai na wuta ya hau saman gadon tana jinshi tayi kamar bacci take ya saka hannunshi ya yaye blanket ɗin ta riƙe yace.
"Ki bari mana mu raya darenmu da Allah ya nuna mana."

"Ni dai ka barni bacci zanyi."
Maryama tace murya ƙasa.

Bai kulata ba ya yaye blanket ɗin ya shiga ciki hannunshi ya ɗaura saman kugunta ya matso da ita jikinshi tare da ɗaura fuskarshi saman wuyanta yana shaƙan ƙamshin turarenta a hankali ya fara kissing ɗin ta har ya zarce bata hanashi ba.

Daren ranar Ya Faruq ya nunawa Maryama ƙanwarsa kuma matarsa soyayyar da bai san ya iya ba sai a kanta, soyayyar junansu ne daren ranar ya ƙara shiga cikin zuciyarsu, sosai ta rikitashi ta bashi haɗin kai.

Wani irin son Maryama mai tsaftane ya shiga zuciyarshi ya linku saman wanda yake ajiye dama.
Godiya kuma da yayi ta jera mata sai da ya sata kunya ta kasa mishi magana balle kallon idonshi.

Basu farka bacci ba sai karfe goma kasancewar weekend ne ita ta fara tashi ta zare jikinta cikin nashi ta shiga bathroom ta gyara jikinta ta fito ta samu ya farka yana zaune.

Yana ganinta yayi murmushi ya ƙarasa kusa da ita taƙi kallonshi ya saka hannu ya ɗago fuskarta idonta na kallon gefe yace.
"Yau kuma kunyata ake ji?"

Bata mishi magana ta kwace fuskarta ta juya tayi murmushi da ya gani ta cikin mirror shima murmushin yayi ya wuce bathroom.

Kayanta ta saka riga da skirt, ta fara gyara ɗakin tana cikin yi ya fito tayi saurin kawar kanta ya zauna saman stool yace.
"Ɗauko mi kaya a ɗakina."

Sum ta fita ta nufi ɗakinsa komai ba laifi ta buɗe wardrobe ƙananan kaya ta cire mishi kamar yadda taga yana sawa da lotion dinshi da turare ta koma ɗakinta ta ajiye masa saman gado ta fita da saurin ganin zai kamata.

Dariya yayi ya gama shirinsa ya sameta a falon ta gyarashi ya ƙarasa gurinta tana shirin fita ya riƙota.
"Ina zaki?"

"Zan ɗaura breakfast ne."

MARYAMA MARYAMWhere stories live. Discover now